Sashe 118
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rumaisa ta durƙusa ta ce "Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa"
Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya miƙar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi.
Ƴan sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya karɓe ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa ƴan sanda.
Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin É—an uwansa turaki ya kama shi.
Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya ƙaryata abun da suka faɗa, ya sanya a saki Jamil.
Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu.
Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a faÉ—i komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir.
Mummy ta ce "Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata ƴa ya ci bulus ba" jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su ƙarata a wurin ƴan sanda.
Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya daÉ—e matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya É—aukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu.
Wambai ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina neman afuwarka ɗan uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama. Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa'adatu, sai dai wannan abu ba kai kaɗai ya shafa ba, zan yi iya ƙoƙarin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba"
"Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya jiƙan fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta.
Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa.
Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da ɗa, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi haƙuri.
"Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi haƙuri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai"
"Ban gaya maka ba? Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a ƙasar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne"
Mahmud ya ce "Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi".
"Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba"
"Na sani mana, saboda sauƙaƙa maka raɗaɗin da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sauƙaƙa maka aiki. Ina mai baku haƙurin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi haƙuri dan Allah"
Cikin kuka ya sake cewa "Jamil fa mahmud, a ɗakin Ammi muka yi wasa tare muka faɗi muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar? Me nayi masa? An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da ƙoƙarin ɗora mini sharri? Me nayi masa ne?"
"Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwaɗayin abun duniya ya sanya shi haɗa kai da maƙiyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon maƙiyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar ɗan uwa naka ne papa".
"Na gode mimi na gode sosai"
"Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi "
Mahmud ya miƙe ya ce "Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma"
Ruma ta ce "Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?"
"Rabu da ni na warware "
"Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?"
Ya ce "Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu. Na karɓi duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana"
Ruma ta ce "When are you exposing her?"
"Soon in sha Allah"
"Idan ba zaka yi ba, allow me to do it"
"I will in sha Allah" ya juya ya fita.
Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba.
Kuma dolensa ya haƙura da cigaba da duk wani yinƙuri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa.
***
Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga ɗimbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata ɓarakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba.
Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan.
Ba tare da wani cikakken shiri ba, Mahmud ya ce lallai sai Yasir ya tafi canada, Yasir ya so ayi bikin yaya Abubakar yana nan, amma ba dama, aikuwa sai da yayi kuka saboda rabuwa da mama da ƴan uwansa. Mahmud kuma ya ƙarfafa yin hakan ne, kar wani abu ya samu Yasir, saboda aikin da yayi musu, dan a wata fuskar laifi ne abun da ya aikata ɗin, kutse da satar bayanan mutane ba tare da izinin su ba.
Haka ya tsallaka ya tafi ya bar Nigeria.
Abdallah kuwa Bashir ya ce sai sun tafi da shi Abuja, mama ta tashi hankalinta ganin kamar ana yi wa yaranta É—auki É—aya-É—aya, amma ya bata tabbacin babu wata damuwa, a kan Jamil ne ita ma rumaisa Adam ne zai wakilce ta, saboda tsohon cikinta.
Ranar da zasu tafi Abuja, takawa yayi ta rarrashin ruma, tare da bata tabbacin, Abdallah zai dawo lafiya, tun da har da shi zasu tafi.
Rumaisa suna ta shirin fara Waec, sai dai fa nauyin ciki ya hanata sukuni sosai, tun da ta dawo daga makaranta, mararta take yi mata ciwo da ƙafafuwanta, kuma takawa ya riga ya tafi, dama ya ce mata idan ba zata iya zaman gidan ba, ta tafi gida wurin mama ko ammi.
Jin ciwo yaƙi ƙarewa, ta kira Usman a waya, ta ce ya zo zata mutu.
Ya je ya tarar da ita duk a firgice, ta bashi mukullin É—aya daga motocin takawa, ta ce ya kaita asibiti.
Suna tafe a hanya ya ce "Ko dai haihuwa zaki yi?"
"Edd É—in bai cika ba fa"
Ya ce "Ikon Allah, muna zaune yarinyar da muka goya, muka yi wa wanka za ta haihu, haryanzu muna gararamba, bakomai akwai lokaci"
Bakin rumaisa bai mutu ba, sai da aka ce mata haihuwa ce a asibiti, ita dai ta san lokacin haihuwa da saura, aka ce usman ya je ya kwaso kayanta.
Maimakon ya kira mama a waya, ko ammi, kawai sai ya kira Aliyu da Huzaifa, sannan ya ƙarasa gidanta, ya ɗaukko akwatin da ta kwatanta masa, dan tuni takawa ya gama sayen komai na jariri.
Mamaki ya kama nurses É—in, suka ce babu wata mace wadda za ta zauna da ita duk sai maza.
Huzaifa ya ce "Hajiya gidanmu ita kaÉ—ai ce mace, babarmu kuma tsohuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, duk abun da mata zasu yi, mu ma zamu yi"
Nurse É—in ta ce "A dai duba dangi a samo wata"
Usman ya ce "Hajjaju, wallahi zamu iya komai, ki ƙyalemu kawai".
"To ina mijinta?"
Aliyu ya ce "Tafiya ce ta kama shi É—azu"
Ta jinjina kai ta ce "Lallai ƘANWAR MAZA"
Rumaisa ta sare da al'amarin, saboda tun da mama ta haifeta ba ta taɓa jin masifaffen ciwo kamar wannan ba.
Mai sunan baba kuwa, ganin hankalin Adam yayi wani wurin, mahmud kuma ya warware, ya sanya ya yi wa mahmud zancen, mahmud ya din ga murna, ya ce dole su je Lagos tare, dan tabattar da wannan lamari, dan haka ya ce zai yi musu booking Flight su je, su yi abun da za su yi, saboda su koma bakin aiki.
Mai sunan baba ya kira Huzaifa a waya, yana masa faÉ—an duk suna ina, gida ba kowa sai mama itakaÉ—ai a gidan.
Mama ta ce "To yarinya ce ni, da lallai sai sun zauna a gida?".
Huzaifa ya gaya masa in suka tafi, ba tare da ya gaya wa mama abun da ake ciki ba, ya tafi asibitin.
Ƙarshe sai da suka cika asibitin, Abdallah da Yasir ne kawai babu.
Gaba ɗaya suka zama abun kallo a asibitin, wai sun kawo ƙanwarsu haihuwa a asibiti.
Ruma ba ta haihu ba sai bayan magariba, babyn pre term ne, watanni bakwai da sati biyu.
Nurse ta fito ta ce "Kun ga ga mahaifa, ga kayan jini, dan girman Allah ku nemo mace"
"Sai kuma ki yi, karɓar haihuwar ma da kin matsa sai mu karɓa, ko abun da ya fi kayan jini ne zamu gyara, babarmu tsohuwa ce, bamu da ƴar uwa mace, dangi ba kowa ke son ka katse masa hidimomin sa ba, dan haka ba jini ba, ko menene zamu iya"
Mai sunan baba ya ce "Ina jaririn?".
"Nursery zamu kai shi, sa an saka shi a kwalba"
Sai da suka jira aka basu damar shiga su ga ruma, tana kwance kai da ganin idonta ka san an sha gwagwarmaya.
Nurses suka ce a kawo mata abinci, sai a lokacin mai sunan baba ya tafi gida, ya gaya wa Iman, ruma ce ta haihu.
Mamaki ne ya kamata, dan washegarin taron nan sun haÉ—u a gidan ammi, ta ce mata haihuwarta da saura.
Nan da nan ta yi girki, jiki na rawa tare da mamakin haihuwar ruma, ta kira ammi ta sanar mata.