← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 124

Sashe 94

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nothing romantic mai sunan baba ya sani, kawai ayi abun da ya dace, dan soyayya in dai irin yadda Aliyu da Abubakar suke me
Jabir kuwa tamkar zai yi hauka, haka ya ji da aka ce, wai an kai kuɗin auren iman, bai taɓa tunanin da gaske yana son ta ba sai yanzu.
A baya matsananciyar sha'awarta ce take addabarsa, tun ranar da ciwonta ya tashi, yana nan shi ya É—auketa ya kaita mota.
A baya bai taɓa tunanin jin son ta ba, saboda tana girmama shi a matsayin yayanta, shi kuma ƙanwarsa, tun daga ranar da ya ga jikinta, ya sanyawa ransa lallai sai ya mallaki iman, ko ba komai, idan ka samu irinta a yaranka, ka samu kadara, saboda kyakywar bafulatanar yarinya ce.

Washegari, ammi ta bayar order yin girke² snacks, ta ce a kai gidansu rumaisa, ruma ta ce gida za ta je, ayi sabgar nan da ita, saboda wauta ta cewa Iman ta shirya, su tafi tare, laila ta ce ya za ayi ta je kai tukuicin kuɗin aurenta, ban da wauta irin ta ruma.

Ammi ta ce laila da sidi sai su kai, sai su tafi da rumaisa, ruma ta ce ga Mahmud, ba sai sidi ya je ba.
Ammi har mamakin yadda Mahmud yake yi wa rumaisa biyayya take yi, duk abun da ta ce masa yayi, ko musu baya yi yake aikatawa.

Hakan kuwa aka yi, da shi da laila, da rumaisa, suka kai kayan nan, mama ta din ga mitar wannan kayan sun yi yawa, dan sun kusa kai É—aya da kuÉ—in auren, banda uban lemuka da naman kaji.

Laila sun gaisa da mai sunan baba, sai dai sama-sama, yaya Abubakar ne mai sakin fuska, sai usman sarkin tsokana.

Laila ta daÉ—e a gidan, suna hira, take bawa mama labarin yanayin zamanta a canada, da iyalinta, take gaya mata a cikin watan, mijinta da yaranta suma zasu zo hutu.

Laila ta yi wa mama sallama, ta cewa rumaisa, za ta je ziyarar ƙawayenta da ke Kano, idan Mahmud ne ya zo ɗaukarta, ko sidi sa biya su ɗauke ta.

Rumaisa kuwa baki yaƙi rufuwa dan murna.
Yasir ya samu ruma ya ce "Ke, zo mu yi shawara, nifa zan saiwa mai sunan baba akwatunan biki".

Ruma ta ce "Da wani kuÉ—in?".

"Ke baki san na kusa fara shigo da wayoyi, da computer daga china ba, ni da abokina muke tara kuÉ—in, yayansa ne zai tsaya mana, mama ma ta san zancen, amma a kuÉ—in dole ni zan saiwa mai sunan baba akwatunan lefe"

Rumaisa ta din ga bayar da shawarwari, na arziki da na shirme.

Bayan la'asar, Mahmud ya dawo ya ɗauki rumaisa, suka biya suka ɗauki laila, albarkacin rumaisa, duk da ko a baya, laila da Mahmud ba a ga maciji, amma suka din ga hira yau sosai, hirar da ba su taɓa yi a baya ba.

Jabir kuwa, Kasa jurewa yayi, ya É—auki mota, ya tafi gidansu takawa, wani irin kishi, da zafin zuciya yana ta azalzalarsa, ya shiga part É—in su, sai dai kai tsaye da ya shiga babu kowa a falon, ya tafi É—akin iman.

Tana zaune a kan gadonta tana danna waya, kawai sai ganin mutum tayi a tsaye a kanta, yana huci.

Sai da ta tsorata, ta ce "Uncle J, lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, tsohuwar munafuka, ni zaki yaudara? Wato dama wancan banzan talakan matsiyacin ki ke so? Ya rasa abun da zai kawo kuɗin aurenki sai dubu ɗari da hamsin, ko da yake babu mamaki, tun da kema tsatson tsiyar ce, ƴar masu kiwo ƙafa babu takalmi duk da babu wanda yake da tabbacin hakan ma, munafuka mayaudariya".

"Uncle j ya zaka din ga zagina ne?, Nifa ban taɓa cewa ina sonka ba, na sha gaya maka a baya".

"Dalla rufe mini baki, har ke wani zaɓi ne da ke, kina wulaƙantacciya"

Iman tayi murmushi ta ce "Tun da ni wulaƙantacciya ce, sai ka bari mai sona saboda Allah, ba dan jikina ba, ya aureni".

"Ni kike gayawa haka ko? To ayi auren mun gani, zaki gane kurenki ne".

Ya juya ya fita fuuu, ta zuba bishi da ido, a falo yayi kaciɓis da ammi, ammi cikin tuhuma ta dube shi ta ce "Ahh jabir daga ina kuma?".

"Wallahi baki yi wa kanki adalci ba, a da ne ake aibata ki, nake karewa, ashe haka kike, waccan ƴar matsiyatan ta zigaki kin hanani ƴa, ƴar ma da ba wanda ya san tushenta, balle a san daga gidan uban wa take, nayi jihadi na ce zan aureta amma aka wulaƙanta ni".

Ammi ta ce "Jabir, ni ka ke gayawa haka?".

"Na faɗa, ai kema kin san baki yi mini adalci ba, mun gama magana da ke, ki je ki canza magana, har da yi wa mahaifiyata sharri, saboda tsabar mugunta da son zuciya, ban sani ba ko dan ba ƴar ki ba ce ba, ya sanya kika zaɓa mata talaka matsiyaci".

Ji yayi an ja shi baya da ƙarfin gaske, an sauke masa zazzafan marin da ya kasa gane daga ina marin ya fito.

Mahmud ya fuskance shi sosai ya ce "Idan kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri, babarka ce babbar annamimiyar da ta haɗa komai, ita ta zo ta ce ba ta son auren, ta koma kuma ta ce ba haka ta ce ba, idan ka kuma yin mummunar magana a kan ta, sai na yi maka dukan tsiya wallahi".

Duk kallon mamaki suke yi wa Mahmud, banda rumaisa da ta dubi Mahmud ta ce "Ai wallahi duk É—a nagari abun da zai yi kenan daddy. Kuma mun ji, ni da yayana talakawa ne, amma masu mutunci da sanin darajar kai.
Kuma idan har za a bawa mutum aure saboda nagartar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faÉ—a, wallahi sai an bawa mai sunan baba sau dubu ba a baka ba".

Jabir ya kalli Mahmud ya ce "Ni ka mara?".

"Waye kai É—in da ba zan mareka ba?"

Jinjina kai yayi ya fita, yana huci, sai dai ya san ko a ido, ba zai iya dukan Mahmud ba.

Kasancewar baba uwani tuni mummy tayi bikonta, domin kuwa ta gane cewa dole-dole tana buƙatar baba uwani a cikin al'amuranta, domin sai ta na sanin halin da ake ciki a sashin ammi, sannan za ta san ta ina za ta dinga ƙulle-ƙullenta.
Ita ma baba uwanin Kasancewar ta rayu da mugun son abun duniya, ya sanya babu tunanin komai, ta komawa mummyn.

Dan haka ko da wannan al'amarin ya faru, ita ta lallaɓa ta kira Mummy a waya ta labarta mata.

Ammi kuwa ta rasa meya kamata ta yi ne? Farincikin ɗan da aka rabata da shi, aka cusa masa ƙiyayyarta ya damu da ita, har ya shigar mata faɗa? Ko kuma fargabar abun da ka iya biyo bayan abun da ya aikata ɗin?

Washegarin da abun ya faru, shine lokacin da suka shirya tafiya gombe, wanda tafiyar har da ammi, har da laila da rumaisa, nusaiba iman da kuma sabir.

Rumaisa taga karamci, kamar su cinyeta, ko ina ta shiga ayi ta nunata ga matar takawa, ga kuma É—an sa É—an marigayiya Aisha.

Haka zalika sun yi murnar zancen auren iman, da yayan rumaisa, da ammi tayi musu, maman laila ta daɗe rasuwa, sai mahaifinta da ƴan uwanta, kasancewar saukar su iman an ƙara sati guda, ya sanya ammi ta kashe wayoyinta, dan kar ma a kirata a ɗaga mata hankali, a kan abubuwan gidan nan, sai da suka kwana uku, sannan suka dawo kano.

Rumaisa ta samu abun arziki kashi-kashi.

Mummy kuwa ta rasa in da zata saka ranta ta ji daɗi, domin kuwa alkadarinta ya tasan ma karyewa, tun da labari ya isaketa cewar Mahmud ya mari  jabir, saboda ya kare ammi, abun ya dungunzuma hankalinta ainun, me hakan yake nufi kenan? Asirin giwa ya fara cin sa? Zai karkata ya koma wurinta, domin shishshigin da yake yi a sashinta yayi yawa, dan ko kai kuɗin auren iman, labari ya isketa, shi ne ya jagoranci ƴan uwan su rumaisa har gidan turaki.
Sai dai ta lura, kamar rumaisa ke taka muhimmiyar rawa, wurin rusa mata shirin da take yi, ta hanyar ziga Mahmud, sai dai ta rasa ta ina yakamata ta yi maganin rumaisa. Sannan ta ƙudiri yadda ta ƙwace Mahmud, ba zata bari ya koma ga ammi ba, dan ba zata gama wahalarsa ba, sannan rana tsaka ya koma wurin uwarsa ba, dan idan haka ne, gara ta nakasta shi yadda ba zai moru ba.

Mummy na tsaka da tunanin meye abun yi, Hajiya Lubabatu tayi mata dirar mikiya, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, a kan marin da Mahmud ya yi wa jabir.

Aka yi sa'a kuwa yana nan, mummy ta ce "Haba lubabatu, mutuwa ma na kunyar idon mahaifi, ya a gabana zaki zo kina zagar mini É—a? Ai sai ki haÉ—a su ki yi musu nasiha, tun da duk Æ´aÆ´anki ne".

"Ba wani ƴaƴana, kema ki daina Wannan ƙumbiya-ƙumbiyar, ki fito kan ki tsaye ki daina wannan munafuncin, kina riƙon Mahmud ne da cikar naki muradin".

Mummy ta ce "Ni tsakani da Allah na riƙe shi, sai ma dai tayaki da nake yi, naki muradin ya cika"

"Jamila, wallahi kar nake kallonki. Kai kuma zaka ga abun da zai biyo ba, ban da tsabar wulaƙanci, uwar me uawar taka binta ta tsinana maka a rayuwar, da har zaka mari jabir saboda ita? Ƙarya yayi an kama an cuce shi, a kan wannan banzar yarinyar to wallahi ahir ɗin ka, shi da yake jiran gadon sarauta, ai mace ma sai wadda ya zaɓa".
Mummy ta ce "Lubabatu yakamata ki san abubuwan da ki ke faÉ—a fa".

"Ba wani, ni ki ƙyaleni, kashedi nayi da babbar murya, idan kallon uwa yake yi miki, to ki ja masa kunne, ya kiyayi ɗa na" Mummy tayi mamakin abun da hajiya Lubabatu ta zo tayi mata, wato hakan yana nufin ita ma tunanin da yake ranta, shine a nata ran, na lokaci yayi da kowa yakamata ya kama gabansa, tun da haryanzu kusan za a iya cewa ita hajiya Lubabatu ba wani benefits da ta samu a tafiyar nan ta su.
Chapter 94 · 0% Book details