← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 124

Sashe 14

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin takaici malam shamsu ya ce "Au haka ma zaka ce? Ta rotse mana ƙwan lantarki na tsakar gida, ta fashe mana glass ga zubarwa da matata jini, amma ka gaya mini wannan maganar?".

"To me zance maka, yanzu dai idan baka haƙura ba, kai ma ka tsinto duwatsu ka yi mana jifa a cikin gidan, ko in kirawo maka rumaisa ka daketa ko? Sai ka huce" aikuwa malam shamsu ya harzuƙa ya fara zage-zage, Usman kuwa ya zage shima yana ramawa, suka nemi bawa hammta iska.

Mama har ta manta da Usman ya fita, ta jiyo zage-zagen usman, yana idan baa rufe masa baki ba, sai ya falla masa mari, kuma ya ɗaga shi ya buga da ƙasa.

Cikin tsananin faÉ—uwar gaba mama ta taso, hankali a tashe za ta fita, Huzaifa ya ce "Mama ba zaki fita ba, yaya usman bai fiye faÉ—an rashin gaskiya ba, kuma yaya Abubakar yana kusa, na san zai raba"

Mama ta ce "Kai dan ubanka bani hanya, kar ya janyo mini magana, na ji da malam shamsu suke yi, ba zai wuce a kan abun da rumaisa ta yi bane, usman in dai a kan rumaisa ne, ko ba ta da gaskiya goya mata baya yake yi, shi ba ya bin komai a sannu, wani fannin halinsu ɗaya da ita, zuciyarsu babu afuwa" mama na cikin maganar yaya Abubakar ya shigo hannunsa riƙe da na usman yana yi masa faɗa.

Usman ya ce "Haba yaya, mu bamu suka fi yi wa illa ba, sun yi mana baƙin fenti a unguwa, bamu yi magana ba sai shi, wai shi tattabara wanda ya yankewa ƙauna cibiya, shi ga mai mata, banzar matar da fuska kamar baƙar jaka, wallahi da namiji ce sai na yi mata shegen duka".

Rumaisa ta ce "Ƙazama da ita ba, mai bleaching"

Mama ta dungurewa rumaisa kai, Abubakar kuma ya cigaba da yi wa usman faÉ—a.

Usman ya ce "Da ne nake adawa da aurar da rumaisa, amma wallahi yanzu na zubar da makaman yaƙi na bi, wallahi party zamu shirya na tashin hankali a unguwar nan, mu hayo dokuna ayi ta kilisa, zamu kaita gidan manyan mutane, mu ga ƙarshen munafurci, mu rufe bakin munafukai" ya kalli rumaisa ya ce "Ke, dan ubanki na daina adawa da auren nan, ki yarda kawai, kuma daga yau daga ita har mijinta kar ki sake gaishe su, ta kuma yi miki maganar banza, zan samo miki duwatsu, daga nan har bamfai ba mai shari'a da ke yarinya ce, na tsaya miki ayi da ni".

Mama ta ce "A'a babu ruwana, kai maimakon ka saita yarinyar nan, ku bi komai a sannu amma kana yi mata huÉ—ubar tsiya, Nuraini har da kai fa kake zigata take rashin ji, babu ruwanka da mutumin nan ku fita sabgarsu, ni ba zan iya tashin hankali da mutane ba".

Usman ya miƙe ya ce "Mama irin masu haƙurinki ake cuta, komai ki ce ayi haƙuri a barwa Allah, da haƙurinki muka ɗauko, muna zaune za a fille mana wuya ki ce mu yi haƙuri"

Dariya rumaisa ta yi, mama kuwa ta rarumi takalmi, ta jefawa usman, ya goce tare da shigewa É—akinsu.

Ruma ta ce "Allah ya biya yaya usy nawa, Allah ya bar mini kai".

"Ki cigaba rumaisa, yayi ta ɗoraki a keken ɓera ya kai ki ya baro, tun da ke dai ba namiji bace ba".

***
Ko da ammi ta koma gida, Nusaiba da Iman suka tareta suna tambayarta yaya suka yi da turaki?
Nan ta kwashe komai ta gaya musu, iman ta ce "Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya mai girma turaki ya shawo kansu komai ya tafi cikin sauƙi, ni dai ina sonta wallahi"

Nusaiba ta ce "Mhmm, ni kam kawai yadda za ayi zaman nan nake hangowa, ba fa sa shiri ammi, kin ga ita tana da tsiwa, shi kuma akwai faÉ—a"

Ammi ta ce "Ke rabu da shi, rayuwar aure ta fi ƙarfin wasa, idan suka zauna za su nutsu, sannan a rayuwarsa da ita akwai wani darasi da nake fatan ya koya, kuma kan ayi auren ai dolensa ya dinga zuwa wurinta su saba"

Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai rikici kenan?"

Ammi ta ce "Ta bani tausayi É—azu da muka yi waya, wai an ce ta yi cikin shege, ana yi mata kallon Æ´ar iska, saboda ta zo da sabir, idan ban saka takawa ya aureta ba, shikenan an yi mata mummunan tambari, mutane É—a idan ba na su bane ba, sun din ga janyo masa jafa'i kenan"

Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya shirya, ya tabbatar da alkhairi" suka amsa da amin.

Baba uwani da take laɓe ta ji hirar ta su sama-sama, sannan bakomai ta ji ba, amma a abun da ta jin, ta ƙudurce za ta je ta sanar da Mummy.

Rumaisa mita a cikinta, kamar an yi mata gori, yau wuni ta yi tana cigaba da mitar abubuwan da ake yi mata a unguwar nan, mama tun tana yi mata nasiha tana cewa ta bar wa Allah, har ta yi mata banza ta ƙyaleta, Abdallah ya sakata a gaba yana cigaba da kunnata, tana mita. Bayan fitar Abdallah rumaisa ta shiga ɗakinsu, ta duba wurin da yake ajiye fensiransa na zane kasancewar sa architect.

Ta zauna ta nutsu sosai, ta hau zane-zane.

Mama ta ce "Uban me ki ke yi musu a É—aki, ki ka shiga ki ka yi shiru?"

Rumaisa ta ce "Bakomai"

"To fito musu daga É—aki, tun basu dawo sun tarar da ke ba"

"Mama zan fito ina zuwa"

Sai da ta gama abun da Allah ya nufeta da yi, sannan ta fito ta fice ba tare da sanin mama ba.

Maƙwabciyarsu ta zana, kuma zanen ya fita sosai, ta yi headline da munafukar unguwa, a ƙasa ta rubuta by Rumaisa Mahmud ƙanwar maza. Ta je ta liƙe a ƙofar gidan matar, ta nausa ta tafi gidansu Habiba, ba tare da mama ta san ta fita ba ma.

Ayshercool.

paid book ne, ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
*PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

Jin shirun yayi yawa ya kuma sanyawa mama ta ƙwalawa rumaisa kira, amma har ta kira kusan sau uku shiru, ba ta amsa ba, mama ta kaste abun da take yi, ta fita domin duba me rumaisa take aikatawa ta ji shiru. Sai dai da ta fito tsakar gida babu rumaisa ba alamarta.
Mama ta leƙa ɗakin ƴan maza, amma babu rumaisa ƙarshe ma sai shiga Maman ta yi ta kwaso kwanukan ta, da suka kai ɗakin suka bar su, ta fito ta duba banɗaki da kitchen duk babu rumaisa, tsayawa ta yi tana tunanin ina rumaisan ta tafi ba ta gaya mata ba?.

Tana cikin jimamin in da rumaisa ta tafi babu izininta, shamsiyya maƙwabciyarsu ta yi sallama, ita da wata mata.
Mama ta amsa musu cikin sakin fuska, ba tare da nuna mata ta san ta yi wa ƴarta ƙage ba.

"Maman rumaisa ni ba zama zan yi ba, ki shiga tsakanina da yarinyar nan, kalli abun da ta yi mini jiya a fuskata, da ɓarnar da ta yi mini a cikin gida, maigidana ya kawo ƙararta, ƙarshe ba wani mataki da kuka ɗauka, sai ma cin mutumci da ya biyo baya, yau kuma ta je ta yi zane ta liƙe mini a ƙofar gidana ya ƙi fita, wai munafukar unguwa, me na yi muku haka ne?"

Cikin dattaku mama ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yaran zamani ne sai godiyar Allah, wallahi da kaina na yi niyyar shigowa na baki haƙuri, wallahi ban san ta yi ba, kin san dai ni ba zan goyi bayan ta yi wannan rashin kyautawar ba, ban san ta yi miki ba, dan Allah dan annabi ki yi haƙuri, bari ta shigo gidan, zan hukunta ta kuma zan sanya ta je ta cire, dan Allah ki yi haƙuri"

"Wallahi banda ina jin nauyinki, Allah da sai na kama rumaisa na yi mata shegen duka".

Mama ta ce "Ashsha, ba za ayi haka ba, ai ke ma ƴarki ce, yanzu kina taɓata komai zai ɓaci, yayyenta ba sa ganin laifinta, amma dai ina baki haƙuri, da kaina zan hukunta ta, kuma zan aikota ta baki haƙuri".

Haka Jamila ta yi ta farfaɗar maganganu, mama tana bata haƙuri, da alwashin hukunta rumaisa, bayan tafiyarta mama ta dafe kai, haryanzu rumaisa babu alamar hankali a tare da ita, tuno damben da suka sha da ƴar ajinsu ta yi, abu har wurin ƴan sanda saboda wannan shegen zane-zanen da take yi, shi kansa Abdallah dan ba yadda za ta yi da shi ne, abun da yake karanta kenan, ga rumaisa na neman gadarsa, in dai zane-zanen banza da na wofi ne, a litattafan makarantar ta ma yi take.

Mama ta rasa mai ma yakamata ta yi, ba ta san ta ina zata fara neman rumaisa ba.

Rumaisa kuwa gidansu habiba ta tafi, suka shantake suna ta hira, ta bawa habiba labarin abun da ta yi wa maƙwabciyarsu.
Habiba ta ce "Kin mini daidai, da nice ba zan iya ba, tsoro nake ji, kin ji yadda matar nan ta din ga yayata maganar nan a cikin unguwar nan, ummanmu ce ta fara taka mata burki ta ce ƙarya take yi, daga nan ta je ta gayawa mamanku"

Rumaisa ta ce "Hmm, ai sai ta gane ba ta da wayo kan ma bar unguwar nan, da ina mutunta ita da mijinta, amma tun da ta taɓo ni, za ta gane bata da wayo"

Cikin rashin fahimta habiba ta ce "Ki bar unguwar nan ki koma ina?"

Rumaisa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Ke share kawai, na san zuwa yanzu wataƙila ta je ta kai ƙarata gidanmu"

"Me ki ka yi mata?"

Cikin ƙwarin gwiwa rumaisa ta ce "Zanata na yi, na rubuta munafukar unguwa, na liƙe mata a ƙofar gida, na san yau za a azabtar da ni a gida, amma ba zan koma yanzu ba"

Habiba ta ce "Wai ruma ba kya jin tsoro ke? Mama ba ta san kin zo nan ba?"
Chapter 14 · 0% Book details