← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 124

Sashe 105

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Papa, yau ko nemana ba ka yi ko, ka sallama ni in gama gararambata, sai yanzu aka gama gyaran gas.... Sai dai rumaisa ba ta ƙarasa ba, idonta yayi mata mummunan gani, Samha a tsaye a gaban mijinta ta turo ƙirji, kamar ta rungume shi, shi kuma daga shi sai dogon wando, da riga armless.

Zagaye su tayi ta wuce, yayin da ya ji wani irin abu mai kama da tsoro da rikicewa ya kama shi.

"Kin ga Samha, dan Allah ki kama hanya ki fita, kar ki haddasa mini matsala a gidana tsakanina da matata muna zaman lafiya"

Samha ta yi murmushi ta ce"Kamar gaske, wai matarka, ayi dai mu gani" ta figi jakarta tayi waje, tare da mamakin girman da rumaisa ta yi, ga abun arziki duk ya fito dai-dai da jikinta.

Rumaisa kuwa kai tsaye ta shige ɗakinta, ta jefar da jakarta da mayafinta, kawai ta faɗa toilet ta shiga ta rufe ƙofa, tana jin yadda zuciyarta take yi mata zugi da raɗaɗi, ta dinga kokowa da wani abu mai zafi da ɗaci, da yake mata kai komo, yaƙi wucewa.

A rikice Adam ya shiga ɗakin yana kiranta, amma tayi masa banza a banɗaki, yafi ƙarfin mintuna ashirin, yana yi mata magiyar ta fito, amma tayi burus da shi.

Sai haƙura yayi ya tafi, tana jin fitarsa ta fashe da kuka, saboda yadda take jin zuciyarta tamkar tana ci da wuta, saboda ɓacin rai.

Adam bai ga rumaisa ba sai bayan sallar magariba, ya faɗo ɗakin unexpectedly ya tarar da ita a zaune tamkar zata fashe, gashin nan ya sha gyara, ya kwanta sai ƙyallin mai yake yi. Gashi ta wani ƙara fresh, dan gyaran jiki suke sha tare, an yi mata lalle kamar ita ce amaryar, ɗakin kansa sai ƙamshin turare yake yi.

Cikin sanyin jiki ya ƙarasa, ya ce "Mimi dan Allah ki saurareni, i will explain to you"

"To hell with your explanations, bana son ji" ta yinƙura za ta tashi, ya sha gabanta.

"Rumaisa kin fi kowa sanin ni ba mutumin banza bane ba, wallahi bani na gayyato Samha gidan nan ba, kawai ganinta nayi unexpected".

"Dama na ce kai ka gayyato ta, idan ma gayyato tan kayi ina ruwana? Dan Allah ka rabu da ni, bana son jin duk wani bayani naka"

"Kiyi haƙuri dan Allah"

"Ai ni baka yi mini komai ba, ƙarewa saura tayi tsirara ka kalleta, shi ma duk cikin kuskure ne" Duk yadda ya so ta tsaya ta fahimta ta ƙi, tayi mursisi ta din ga yi masa rashin mutunci.

Tun da ake faɗar fitsararta, bata taɓa gwada masa tijara muraran ba kamar yau, sam tayi burus taƙi fahimtar sa.
Ƙarewa ma, yana fita ta kulle ƙofarta.

Gaba É—aya Adam ya rikice, ya rasa abun da yake yi masa daÉ—i, rarrashin duniyar nan, ruma tayi burus da shi, da sassafe ta fita ta tafi gidan ammi, aka cigaba da shirin biki, tamkar babu abun da ya faru.
Rashin ganinta a gidan bayan ya tashi, ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, ya fara zuwa gidansu, amma ya tarar da ita tamkar ba abun da ya faru, tana ta hidimominta, ƴan uwan su ammi na gombe, duk sun hallara. Daga nan gida tayi tafiyarta gidansu, nan ma gida ya cika mutanen katsina duk sun hallara.

Ana ta shirin biki, da daddare su habiba suka zo ita da mamanta, idan da aikin da za a kamawa su mama, ga su Hauwwaliya, ai tuni ruma ta manta da damuwarta, ta shiga cikinsu suka cigaba da taɓararsu.

Aliyu tun da yaga Habiba yake shiga yana fita.

Ruma ta ce "Habiba baki da mutunci fa, ki ke soyayya da yaya Aliyu ba labari, kuma ko gaisheni ba kya zuwa yi"

Habiba ta ce "Sannu mama" suka tuntsire da dariya.

Habiba ta ce "Kamar in janyo lokacin candy rumaisa, ina ƙaunar Yaya Aliyu kamar me, Ruma aure da daɗi dan Allah?"

Hauwwaliya ta ce "Eh É—an gaya mana"

Ruma ta ce "Eh to, ba nace babu ba, bana ce akwai ba, idan kun je kwa gani, idan ku ka yi sa'a ku ka auri irin mijina, to kun dace, ni da mijina bani da matsala, sai danginsa 'yan bala'i. Ku san kowa da kalar jarrabwarsa a gidan aure".

Hauwwaliya ta ce "To, Allah ya sassauta mana"

Suka amsa da Amin.

Da Adam ya koma gida, aka ce masa ruma ta tafi gidansu, dan haka ya tafi yana fatan Allah ya sa ba ta faÉ—i wani abun ba.

Wayar mama ya kira, suka gaisa ya ce mata rumaisa ta zo, zasu tafi.

Ba ta son tayi musu ko wani abu da zai sanya, a gane saɓani suka samu, dan laila ta gargaɗeta sosai a kan haka, ta ce mata duk wata matsala, in dai za su iya warwarewa a tsakanin su, kar ta bari wani ya ji, balle ya shiga. Galibin aure yana samun matsa a dalilin sako mutum na uku a cikin matsalolin auren.

Bayan motar ta buÉ—e ta shiga, ko kallonsa ba ta yi ba.

Har suka je gida ba ta kula shi ba, shi ma kuma bai iya ce mata komai ba, duk da ƙasan zuciyarta har ta fara jin tausayinsa, dan a kiɗime yake sosai da sosai.

Da suka je gida ma, a buÉ—e ta bar masa motarsa ta yi shigewarta cikin gida.

Ko tayi niyyar daina fushin, da ta tuna yadda ta ga Samha a tsaye a gaban sa, ta turo ƙirji sai wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta.

Wanka tayi, ta je kitchen ta damo kununta, ta koma É—aki tana sha. Ita kanta missing É—in sa take yi sosai da sosai, saboda sun yi wani irin sabo sosai da sosai.

Kamar mara gaskiya haka yayi sallama a ɗakin, ta amsa masa ƙasa-ƙasa.

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Rumaisa".

"Na'am" ta amsa a daƙile.

"Yanzu kina tunanin zan iya aikata abun da bai kamata ba kenan? Yakamata ki fahimce ni, ya ci ace kin san halina, wallahi rumaisa babu wani abu da ya faru, abun da ki ka gani ma is not intentionally ban san me ma zan ce miki ki yarda da ni ba. Amma dan Allah kar ki kawo komai a ranki".

"Amma fa tsayawa ka yi kana kallonta, fisabilillahi".

"Rumaisa a rayuwata bana tunanin akwai wanda na taɓa bi ina bawa haƙuri, kamar yadda nake binki a yanzu, dan Allah ki yi haƙuri, ko sai na durƙusa ɗin a kan gwiwoyina?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki dube ni mana, kiyi haƙuri Please" yayi maganar yana riƙe hannunta cikin nasa.

"Na haƙura amma dan Allah kar ka sake kulata, wallahi ji na yi kamar na je kitchen na samo taɓarya na zo na rotse mata kai. Kawai ta wani tsaya ta gantsare a gabanka, wallahi na ji haushi"

Ya ce "Subhanallah, duk ba ta kai ga haka ba, nima ban ji daÉ—i ba amma ki yadda da ni, ai ni namu sun isheni, me zan kalla a na wata"

"Abun da bai fi murfin jarkar faron ba?"

Yayi murmushi ya ce "Har laifukana na baya za'a tayar kenan?".

"Eh É—in, ka je ka kalli naka ko na Samha"

Yayi murmushi ya ce "Allah dai ya bada haƙuri"

Ta amsa da "Amin"

Ya rungumeta ya ce "I so much miss you, smile please"

Ta lashe cokalin hannunta ta ce "ba zan iya ba yanzu, idan na ce zan yi murmushi yanzu, yaƙe kawai zan yi. Ka ci abinci kuwa?"

"A ina zan ci, tun da baki bani ba?"

Ta ce "To mu je na sama maka abun da zaka ci"

"Yauwwa my dear, ana so na ana kaiwa kasuwa, an damu da ni amma ana ta wahalar da ni"

Ta kalleshi ta ce "Ka ke dai so na"

Ya ce "Na yadda".

Ta ce "To amma sai dai ka goya ni, ka kai ni kitchen É—in"

Ya durƙusa ya ce "Zo ki hau"

Aikuwa ta miƙe ta hau bayansa tana dariya, ya goyata a bayansa, har kitchen.

A ranar dai suka shirya, rumaisa tayi iyakar ƙoƙarin ta wurin bin shawarar da anty laila ta bata, na cewa idan har namji zai iya yi miki laifi ya baki haƙuri, to ba ƙaramin kimarki yake gani ba, ba kowann namiji ne zai yi ba dai-dai ba ya nemi afuwarki, sai ma yayi ƙoƙarin nemo wani laifin ya jingina miki, duk dan kar ya nemi afuwarki.

Sosai aka shiga hidimar biki, ka'in da na'in, mai sunan baba kai ya É—au caji sosai da sosai, abunka da wanda bai saba da hayaniya ba, nan da nan sai ciwon kai.

Gidan marigayi galadima Sharif ma, ya cika ya tumbatsa, mutane sai kaiwa suke suna komowa.

Mummy kuwa ba gaira ba dalili take tsinewa auren, tare da mummunan baki a kan haka.

Rumaisa kuwa ba ta a nan bata a can, takawa sai mita yake a kan ta nemi wuri ta din ga hutawa, kar sai an kammala biki, ta zo tana ciwon jiki.

Ranar da aka yi dinner rumaisa tayi kyau, haka amarya Iman da mai sunan baba, shi gaba É—aya ma kunya yake ji, ko É—aga kai baya son yi ya kalli taron jama'ar nan.
Yazo wurin nan ne kawai saboda iman ta matsa. Kamar da bikin rumaisa a wannan karon ma, kaiwa da komowa zaratan samarin gidan maman suka din ga yi, sanye da kaya iri ɗaya a jikinsu gwanin sha'awa ango ba shi da wasu abokai, sai classmates sai ƙannensa.

Ƙawayen ammi sun yi mata kara sosai da sosai, suka din ga liƙi suna kaiwa da komowa, duk wanda ya ga couples ɗin sai ya ce masha Allah, saboda kyau ne ya haɗu da kyau, duk da bai kai iman haske ba, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka ce kyakkyawa ne.

Bayan an kammala dinner suka taso, Mahmud ne ya É—aukko su a motarsa, Iman sai hamma take yi, saboda ta gaji.

"Kin gaji ne?" Ya tambaye ta lokacin da ta kashingiÉ—a da seat É—in motar.

"Eh yaya umar, ko ina ciwo yake mini"

Yayi murmushi ya ce "To sannu, idan kin je gida ki kwanta ki huta sosai"

Ta ce "To ango"

Yayi murmushi, suka fara kaita gida, sannan suka wuce Mahmud ya kai mai sunan baba gida.
Chapter 105 · 0% Book details