← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 124

Sashe 37

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can kuma ta hau murna, tana lissafin ƙawayenta da zata bawa ankon da zasu ɗinka, ga uban kuɗi kuma tana gani.

Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuÉ—in da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa'a ya sanya mata albarka.

***
Bin invitations É—in yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara É—oki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba.
Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima.

Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ƙarasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce "An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci".

Adam ya ce "Masha Allah, that's good ina godiya sosai, ina sidi?"

"Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji"

"Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na É—auki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan".

Bashir ya ce "Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba".

Adam ya É—an yi jimm sannan ya ce "Wallahi Bashir sam bana É—okin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events É—in da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini"

Bashir ya yi murmushi ya ce "Ka yi haƙuri, ammi ba zata zaɓa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka ɓoyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin"

"Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da É—a na daga hannun Æ´an bindiga".

Bashir ya ce "Mafita ɗaya ce, duk yadda zaka yi ka ɓoye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da ɗoki a fuskarka".

Adam ya yi murmushi ya ce "Yadda za a ji daɗin cewa, saboda na auri yarinya ƙarama na kashe matata ko?"

"Ai dama dole sai an faɗi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ƙaramar yarinya ka ɓoye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ƙarama kamarta ta kuɓuta da jariri a hannun 'yan bindiga"

Adam ya yi ajiyar zuciya, ya É—an murza goshinsa ya ce "Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana".

"Amin ya Allah"

Wayar takawa ce ta fara ringing, ya É—auka ya duba ya ga sunan Aliyu.

Ya É—aga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce "Barka da wannan lokaci, ya hidima?".

"Alhamdilillah, ya taku hidimar?"

"Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai"

Adam ya ce "Ok, ba ta".

Rumaisa ta karɓi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido.

Ta karɓi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana.

Ya daki ƙafarta ya ce "Ba zaki gaishe shi ba?"

"Ina wuni?"

Maimakon ya amsa ya ce "Ya aka yi?"

"Gaisheka fa na yi" ta yi maganar a ƙule.

"Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, riƙe kayarki, ina jin ki"

Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala'i ba.

"Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana".

"Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuÉ—in da ka bani sun yi yawa, sannan......"

"Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ƙoƙari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuɗi kuma ki zubar" ya kashe wayarsa.

Dungurar da wayar ta yi a ƙufule, ta ce "Yaya usy kalli abun da ka janyo mini"

Dungure mata kai yayi ya ce "Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba É—an karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme.
Ke, tashi mu je ɗaki, na yi miki bayanin me auren ya ƙunsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon.

Aliyu ya ce "Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?".

"Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya".

Aliyu da dariya ta ƙwace masa ya ce "Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai".

Usman ya ce "Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune Æ´ar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara Æ´a Æ´a kuma".

Aliyu ya ce "Wani irin ta fara Æ´aÆ´a wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka"

Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce "Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuɗin makaranta ko? You don't get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a  sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka".

Aliyu ya ce "kai haba, she's too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka".

Usman ya yi dariya ya ce "Uban calm da decent É—in, that thing don't get sense, don't fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuÉ—i ya auri Æ´a ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce"

Aliyu ya yi tsaki ya ce "Zaka ɓata mini rai "
Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce  "To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ƙila kin san komai, ki ka yi wani kasaƙe da kai".

Aliyu ya ce "A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin".

Usman ya ce "Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki".

"Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba" a guje Usman ya faÉ—a É—akinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba.

***
Jabir ya din ga juya invitation É—in, sannan ya kalli Adam ya ce " da gaske Adam saura kwanaki a É—aura maka aure, amma ban sani ba?"

"Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai haƙuri".

Jabir ya sake kallon invitation É—in, sannan ya ce "To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan".

Adam ya ce "Zaka ganta very soon".

"Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai".

Adam ya ce "Please, don't raise that issue here, ku daina ganin laifina, ƙaddara ce ta zo a haka".

Jabir ya ce "Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai".

"Jabir, this is an arranged marriage, ku yi mini uzuri".

Jabir ya ce "Arranged marriage, to Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu".

"Amin, addu'arku nake buƙata dama, yanzu ka tashi mu je gidan mai girma turaki, zan kai masa nasa katin, da zai bawa mutanensa, da na jamil da gidan gaba ɗaya".

Jabir ya ce "Ok, ba damuwa bari mu yi salla tukuna"

Bayan sun idar da salla, suka tafi gidan turaki, kai tsaye sashinsa suka shiga, bayan sun tarar da babu kowa a falon.

Yayi murna sosai yayi addu'a da fatan alkhairi, sannan ya yi wa adam nasiha sosai mai shiga jiki. Sai dai kamar haÉ—in baki suka tarar da mama da Samha, har ma da zainab a falo.
Samha jikinta har tsuma yake da ta ga Adam, ga soyayya ga kuma kishi, ya gaida mama ta amsa masa sama-sama, ta saki jiki ta amsa gaisuwar Jabir.

Su Samha suka gaishe shi ya amsa, ya ajiye wa mama katuna, ya ce "Gashi nan, ammi ce ta ce in kawo miki, na taron wunin da za ta yi, na bawa mai girma turaki nasa".

Da ƙarfi Samha ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam wai dama da gaske ne, ta tabatta aure zaka yi?" Ya ɗaga kai ya kalli Samha da tsoro da kishi ya bayyana a fuskarta, ya jinjina mata kai a hankali cikin tausayawa.

"Shikenan, bakomai na gode " ta tashi ta bar falon. Jikin Adam ya yi sanyi, mama kawa jan tsaki ta yi ita ma, Zainab kuwa cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi.

Ɓangaren ammi ma, da ta bawa mummy katin gayyata, masifa mummyn ta din ga yi, wai har ace adam zai yi aure, amma a kasa sakata a cikin lamarin bikin, sai dai ta zo a ƴan gayya, saboda ba a mayar da ita a bakin komai ba.
Chapter 37 · 0% Book details