← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 124

Sashe 56

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ita ma dai, ta na da azabar taurin kan tsiya, ni ina girki kawai na ga ta shigo da gudu, ta tura abu a wuta, zan yi magana ta ce in yi shiru, sai ga shi ya biyo ta, amma na ji yana magana a kan Aisha, wataƙila abu ne mai muhimmanci da ya shafe ta".

"To waya sani, ni dai fatana kar ya illata kawai".

Bayan sa'oi uku, Adam ne ya fara yin juyi, dan ji yake kamar barci yake yi, kawai ya ga rumaisa a kwance a ƙasa, ita daban towel ɗin ta daban, da ga ita, sai gajeren wando.

Tashi ya yi zaune yana ƙoƙarin tuna abun da ya faru, kawai dai ya iya tuna yadda ya janyota har ɗakinsa, amma daga nan komai ya goge a kansa.

Tsura mata ido ya É—an yi, yana tunanin ko barcci take yi ne? Amma sai ya ga yanayinta bai yi kama da haka ba.

'Ko wani abun na yi mata?' ya tambayi kansa.

Matsawa ya yi kusa da ita, ya É—agota, ya ga jikinta a sake.

A gigice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, i lose my sense again?" Rabon da ya fita completely daga hankalinsa haka, an kai shekaru goma, ko ya yi loosing control, ya na iya tuna abun da ya faru, amma completely yau ya kasa tunawa.

Wuyanta ya kalla, duk shedar an karceta da farce.

Ya É—an girgiza ta ya na kiran sunanta.

"Rumaisa!" Amma shiru ba ta motsa ba, ya taɓa hannunta, ya ji zuciyarta na bugawa, numfashi da take yi a hankali.

Ya kwantar da ita ya shiga banɗaki, ya ɗebo ruwa a hannunsa, ya dawo ya shafa mata a fuskarta, ya ƙure gudun Ac da na fanka.

Bai ɗaura mata towel ɗin ba ya ƙyaleta, ya lulluɓe ta da shi, ya tsura mata ido yana fatan Allah ya sa ta farka, dan kuwa idan ya ɗauketa ya kai ta asibiti, asirinsa zai iya tonuwa, dan babu lallai ta yi shiru, kuma dole a tambayi mai ya sameta, ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta tashi.

Babu tsammani, kawai ya ga ta tashi zaune, tana ganinsa ta ja da baya, ta kare jikinta da hannunta.

Sai a lokacin ya yi ajiyar zuciya "Ki É—aura towel É—in mana" ya faÉ—a a sanyaye.

"Dole ka ce na ɗaura mana, bayan ka yi mini tsirara, za ka kasheni, wallahi gida zan gudu, ba zaka kasheni ba? A hakan zan gaya maka abun da na sani ɗin? Dama ban san komai ba ma, wallahi ba zaka kasheni a banza ba, ka shaƙeni kamar wata ɓarauniya".

A hankali ya ce "Ya ilahi, i attempt to kill her?'

Ta saka hannu ta ja towel ɗin, ta rufe jikinta, ta yinƙura ta tashi, ta fice daga ɗakin.

A hankali ya lumshe idanunsa, ya bawa hawayen da suka taru a idonsa damar zuba, ba zai so ammi ma ta ji wannan maganar ba, iya rayuwarta a hanyar nema masa magani take, ana murna abu ya ɗan yi sauƙi sai abun da ba a rasa ba, kwatsam yau abu ya dawo kamar da.

Sai ya ji tashin ciwon nan nasa, ya shafe abun da rumaisan ta aikata masa.

"Mahaukaci ne ni? Ko kuma maye? Ko kuma namiji mai mutanen ɓoye, wato aljanu?" Tambayar da tun da ya shekara takwas a duniya, yake yi wa kansa da ya gaza samun amsarta.

Ba shi da tabbacin rumaisa ta rufa masa asiri, haka zalika bai san ta ina zai fara yi mata bayani, ta fahimce shi ba, sai a lokacin yake ganin rashin kyautawar da aka yi, na rashin yi musu bayanin larurarsa.

Madigar kuwa ta na zuwa É—akin ta, gado ta hau ta cigaba da bacci.

Baba uwani kuwa, ta fita ta zagaya, jikinta na tsuma, ta kira lambar Mummy.
Aka yi sa'a mummy na kusa, ta É—ag wayar, gulma na cin ta ta ce "Allah ya taimake ki"

"Ina jin ki".

"Akwai abun da ya faru".

"Je ki kai tsaye".

Baba uwani ta waiwaya sannan ta ce "Ranki ya daɗe, muna cikin aiki muka ga ya biyota afujajan, a kan wani littafi, sai dai kan ya cimmata ta tura shi a wuta, na ji yana magana cewa, abun da ya shafi aisha ne, baki ga shaƙar da yayi mata ba, ƙarshe dai ya shiga da ita ɗakinsa, ya rufe su, sai yanzun nan ta fito".

Mummy ta ce "Good, kin fuskanci ya yi mata wani abu ne?"

"Ban san me yayi mata ba da ya rufe su, amma na ga ta fito tana kamar magagin bacci".

"Kin sanar da samha ne?"

"A'a Allah ya baki nasara".

"Kar ki sanar da ita komai, sai abun da na umarce ki".

"In Allah ya yarda".

"Ki koma, ki cigaba da sanya mini ido a kan duk wani motsinsu".

Baba uwani ta ce "An gama uwar É—akina". Ta katse wayar ta koma.

Adam kuwa ya yi sallar azahar, ya jingina da jikin gado, ya yi shiru yana tuna abubuwan da suka shuÉ—e, gaba É—aya jikinsa ya yi sanyi.

Kiraye-kirayen, sallar azahar ne ya tashi rumaisa, ta je ta yi alwala, ta saka kaya, ta tsaya a gaban mudubi, ta na kallon wuyanta, da ya shata yake mata zafi.

Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta taɓa ganin wannan abun a mafarki, ko kuma ya taɓa faruwa.

"Wallahi sai na gaya wa mama, tun da kasheni zai yi, sai na gudu na bar gidan nan"

Can kuma sai wata zuciyar ta tunatar da ita, muddin mama ta ji a kan meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, faÉ—a za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta faÉ—i abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba.

'Subhanallah, na fasa faɗa, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan faɗa masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lallaɓa na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta ɗan yi shiru ta ce "To da ya shaƙe ni kuma sai na yi bacci, oho dai? Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji.

Adam ya tashi ya nufi É—akinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen.

Ya leƙa kitchen ɗin, ya hango ta taka kujera, tana saka ɗan wake, kamar babu abun da ya sameta.
Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita.

Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lallaɓo ta hawo benen.

"Sannu Æ´ar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?"

Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?".

"Ai ganin yadda ya janyo ki ɗin nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake buƙata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya ɓaci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa. Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?"

Rumaisa ta juyo gaba ɗaya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin haƙƙi kuma?".

"A'a haƙƙin aure mana".

"Meye haƙƙin aure kuma?"

Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai".

Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?"

A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?"

"Kin ji me na ce ai".

"Ke waye ya gaya miki?"

Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu"

Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki? Ki ji tsoron Allah"

"Ke ki ka faÉ—a, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi".

"Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa"

Rumaisa ta juya ta cigaba da saka ɗan wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwaɓarta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan ƙuriciya, har da wauta ke damun rumaisa.

***
"Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu". Mummy ta yi maganar da waya a kunneta.

"Ya aka yi ne?".

Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne".

Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?".

"Ɗan maje ne ya turo mini saƙo, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bunƙasa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya ɗauki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar".

Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba"

"Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke ɗaukar al'amuran nan da sauƙi, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a ɗau kowa ba sai shi? A dalilin me?".

"Kuma fa da gaskiyarki Jamila"

"Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai".

"Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba É—aya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri".

"Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu haÉ—u kawai".

***
Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon.

Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna haÉ—a ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce É—akinsa.
Chapter 56 · 0% Book details