← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 124

Sashe 35

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam ya ce "Ammi, wai takamaimai me yake damun iman ne?"

"Takawa ina zan sani? Na ga na asibiti sam baya yi mata ma, na rasa in da zan saka kaina ma. To ya aka yi, kun tattauna ɗin, ya ka baro rumaisa? Ina son a satin nan idan iman ta warware a fara haɗa lefe, dan na turawa laila kuɗi, ta yi wasu sayayyar a can ƙasar"

"Babu lafiya" ya faÉ—a a hankali.

Ammi ta ce "Kamar yaya?" Nan ya kwashe komai ya gaya mata, ammi ta yi shiru ta ce "Ikon Allah, Adam akwai aiki ja a gabanmu, babban fatana yanzu shine in ga an yi auren nan, kuma bana fatan a É—aga ko da rana É—aya".

Adam ya jinjina kai Sannan ya ce "Bari na je na ga sabir, daga nan na wuce masallaci".

Tun da ya fita yake ta jujju
***
Rumaisa sai magariba sannan suka samu kanta, ta tashi daga wannan baccin, ba ta iya tuna komai ba, ta cigaba da sabgoginta.
Mama hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, saboda gani take rumaisa aljanu ne ke son su hanata aure. Babu wanda yayi yinƙurin gaya mata abun da ya faru, suka biye mata aka cigaba da harkokin gidan kamar yadda suka saba.

Washegari Ammi ce ta kira mama da kanta a waya, tana tambayarta jikin rumaisa.

Mama ta ce "Jiki da sauƙi hajiya, na ce ko ɗaga bikin nan za ayi, a nema mata magani, alamu sun nuna iskokai suna damunta, kar ayi aure da larura".

"A'a maman rumaisa, Allah zai bata lafiya, wataƙila da an yi auren ta samu lafiya, wallahi kin ganmu nima iman haryanzu jiki yaƙi daɗi, na rasa abun da yake yi mini daɗi, ciwon kai ko sauka ba ya yi".

Shiru mama ta É—an yi, kenan maganar rumaisa gaskiya ce?.

Mama ta ce "Allah ya basu lafiya baki É—aya, in anjima zamu zo mu sake duba jikin nata"

Ammi ta ce "Ba sai kun wahalar da kanku ba, ayi mata Addu'a kawai".

Mama ta ce "Haba, ai babu wannan a tsakanin mu, bari ayi sallar magariba, rumaisa ta dawo daga islamiyya sai mu zo"

Ammi ta ce "To shikenan, ta samu ta ga É—anta ma".

Bayan sun gama wayar, mama tayi ta Addu'a Allah ya sa ba aljanu ne suka buÉ—ewa rumaisa ido ba, take gane-gane.

Da magaribar, tare da mai sunan baba suka je gidan su takawa, rumaisa na ta murna za ta ga Sabir.

Har É—akin iman, aka yi musu izinin shiga, suka tarar da ita kamar mai shirin zarewa saboda surutai, duk suna kanta ciki har da Jabir.

Rumaisa ta ƙarewa ɗakin kallo, ta ce "Mama, ɗakin nan na yi mafarki fa jiya, ku cirewa iman pillown nan, mafarki na yi wata ƴar tsana tana soka mata allurai a kanta, yauwwa ba na ce muku iman ba ta da lafiya ba jiya?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin tuna abun da ya faru jiyan.

Ammi ta ce "Rumaisa a ina ki ka ga Æ´ar tsanar?"

"Mafarki fa na yi, ki dafa pillown, ki karanta mata bisimillah da fatiha, amma dai wata Æ´ar tsana na gani a mafarki"

Abun sai da ya É—aurewa kowa kai, Mai sunan baba kuwa tuni ya bar É—akin, saboda yadda iman take, zaka san tana jin jiki ba kaÉ—an ba.

Ammi ta dafa pillown, ta karanto adduoi, Rumaisa ta riƙe hannun iman tana yi mata sannu.

Jabir ya tashi ya ce "Ammi, bari na je gida, Allah ya bata lafiya"

Suka amsa da Amin ya tafi.

Tattaunawa ammi da mama suka cigaba da yi, ammi tayi ta bawa mama ƙwarin gwiwa, a kan kar a fasa wannan auren.

Bacci iman ta samu, mama ta kalli Adam ta ce "Takawa, kai rumaisa part ɗina, ta ga Sabir, sai ka tambayeta abun da take buƙata na bikin"

Adam bai fiye yin jayayya da ammi ba, balle kuma yanzu da yake a gaban mutane ne, bai ce uffan ba, ya tashi ya fita, rumaisa ta bi bayansa tana murna, jin an ce za ta ga Sabir.

A hanyar sashin ammai, suka haɗu da baba uwani, cikin girmamawa ta risuna ta ce "Takarwarka lafiya magajin galadima, baƙuwa muka yi ne?"

"Eh" ya amsa a taƙaice yana fatan kar rumaisa ta yi wani shirmen, amma ga mamakinsa, ko kallon baba uwani ba ta yi ba balle ta gaishe ta.

Sai da suka yi gaba sannan ya kalleta ya ce "Baki iya gaisuwa bane?"

"Wa zan gaisar?"

"Matar da muka wuce, meyasa baki gaisheta ba? Gidan sarauta ba wuri ne da zaki gwada rashin É—a'a ba, akwai girmamawa da karamci, ko da kuwa kai ne kake gaba da mutum"

Ba kunya ba tsoro ta ce "A hakan? Sau nawa na gaisheka a rayuwar nan baka amsawa, gidan sarautar da watarn wanda kake gaisarwa daban masu amsawa daban, ana ce maka an gaisheka ɗan talakawa, wannan ba wulaƙanci bane ba, ban kula kowa ba balle ayi mini wulaƙanci na ji haushi, ammi da wanda suke amsawa kawai zan din ga gaisarwa"

Wato ya fuskanci ita dai wannan yarinyar, defeating ɗin ta, ba abu ne mai sauƙi ba.

Sai da suka shiga ɗakin ammi, in da babu idon mutane, sannan ya dubeta ya ce "Idan ki ka cigaba da wannan taurin kan, ina gaya miki abu kina mayar mini da martani, zaki yi dana sanin aure a gidan sarauta, dan zai zame miki tamkar kurkuku mafi azaba, kowa zai yi ƙoƙarin yin amfani da ke wurin cimma burinsa, dole ki kiyaye".

Rumaisa ta ce "Na sani, gidan sarauta ba irin normal gida bane, ina gani a film, na indiya da sauransu, daga tsafi sai munafunci, abun ban tsoro, kowa ba abun yadda bane ba, da an ga baka da wayo, sai a cuceka, da ka yadda da wani, sai ya nemi ganin bayanka. Ai ni a duniyar nan kurku mafi azaba ita ce zamana a hannun 'yan bindiga, abu mafi razani kuma ganin mutuwar matar da ta bani kulawa kamar ƴar ta a lokacin da ake yi mini ƙamshin mutuwa. Abu mafi tsayawa a rai shi ne tunanin idan har gawarta tana da muhimmancin da za a kasheta a ɗau gawarta a mota a bar wurin da ita, saɓanin sauran mutanen da ake kashewa wurin, to waye ya saka ayi garkuwa da ita a kasheta, kuma ayi umarnin kashe ɗan ta? Abu mafi ban tausayi shi ne haihuwar jaririn da bai san komai ba, na din ga wahalar da shi da sunan kulawa, har koko na bashi, ya shafe kwanaki da ƙazantar haihuwa a jikinsa, bayan mun kuɓuta a ka yi yinƙunrin rabani da shi.
A tunaninka akwai wani abu mai wahalar mantawa kamar wannan? Ko wani irin ƙalubale ne, zan jure shi na rayu da sabir, kamar yadda na yi wa anty aisha alƙawari, amma ka ƙyaleni a yadda nake, ni ba ƴar sarauta bace ba, lokaci ɗaya ba zan iya zama irin ku ba". Tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta taka a hankali ta ƙarasa gaban gadon Sabir, ya ƙara zama ƙato sosai, sai bacci yake yi.

Takawa kuwa kamar an gina shi, wasu gaɓoɓi ta taɓo masu muhimmanci, amma ya san yanzu da yayi yinƙurin ya cigaba da yi mata maganar, zata koma masa ainihin rumaisanta, ta fara rashin kunya.

Ta riƙe ƙafar sabir, tana kallonsa tana murmushi.

Adam yayi gyaran murya ya ce "Ammi ta ce, na tambayeki idan da abun da ki ke buƙata na shirin biki"

Maimakon ta amsa kawai sai ta hau dariya ta ce "Ni fa mantawa nake yi aure za ayi mini, ni bana buƙatar komai, su yaya Aliyu suna saya mini kaya, su mama kowa sai mini kaya yake yi".

Ya jinjina kai ya ce "Good, that's their part, a ɓangarena nake nufi, wanda ni yakamata na yi"

Ta girgiza kai ta ce "Za a saya mini komai, ni fa bana son ayi mini abu azo daga baya ana yi mini gori, komai za su saya mini, har da turmin ƙarfe"

Ya ce "Shikenan, na gaya mata ba kya son komai, tashi mu tafi na san ke suke jira"

Ta sumbaci goshin sabir ta ce "Ka yi mafarkina babyna" sannan ta yi gaba ta bar takawa a baya.

Aikuwa ta tarar da su a falo har sun fito, Ammi ta ce Adam ya mayar da su gida, mama ta ce ba ta yadda ba, ba zata iya hawa motar siriki ba, ƙarshe aka saka direba ya mayar da su, mai sunan baba ya ce za shi wani wuri, dan haka bai bi su ba.

A daren sai da baba uwani ta kai wa mummy tsaigumin zuwan su mama, tare da sanar mata ba ta san ko suwaye ba amma suna yawan zuwa gidan.
Mummy ta ce lallai ta sanya ido, ta gane ko suwaye, ta zo ta gaya mata.

Tun da Allah ya sa rumaisa, ta gaya wa ammi abun da ta gani a mafarki a kan iman, suka dage da addu'a, kuma cikin ikon Allah ta samu lafiya.
Ɓangaren su mama shiri suke sosai da sosai, a kan bikin da yake gabato su, sai dai rumaisa ta cigaba da mafarkai barakatai, da razana, har da ganin ta a wurin ƴan bindiga.

Mama ta sanarwa da Gwaggo, in za Gwaggo ta yi ta faÉ—a a kan ta sha cewa a nemawa rumaisa maganin tsari, amma maman tana yin burus da ita.

Danginsu rumaisa kowa da abun da yake kawo wa na gudunmawarsa, sai dai Æ´an unguwa basu san me ake ciki ba.

Kwanci tashi asarar mai rai, ya rage saura kwanaki goma sha uku, auren rumaisa da adam, yayyen rumaisa da dangin mahaifinta, da na mama sai rawar gani suke yi.
Gefe ga masu kawo gudunmawar magunguna na gyaran jiki, da gyara aure, mama ta kasa bawa rumaisa, gani take kamar idan aka bata za a cutar da ita, shekarunta basu kai ba, ba ta da tabbacin ma shi kansa mijin ya saurareta.
Sai dai mussaman babar hauwwaliya, ta biya mai gyaran jiki, take zuwa gida yi wa rumaisa gyaran jiki, shi ma ta din ga tamɓele kenan tana guje-guje tana ihu, wai ana azabtar da ita, za'a rina mata fata da azaba.
Chapter 35 · 0% Book details