← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 124

Sashe 39

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ƙure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ƙafarsa ba zaki hango ba, let's join hands together"

Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faÉ—in "Shashasha kawai".

Iman ita kaÉ—ai a É—akinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faÉ—i, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.

Ɓangaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. Taɓe baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.

Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.
Ta wuni a uwar ɗakan mama, tun ƙarfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ƙarfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.
Maƙwabta na ta mamakin wani hamshaƙin ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.

A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ƙi tsayawa.

Mai kwalliyar ƙawar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.

Ƙarshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.
Ya je ya tarar duk an yi wa ƙawayenta kwalliyar ban da ita.

Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?".

"Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka.

Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi".

Adam dai ya ƙule ƙarshe, Bashir ne yayi ta bata haƙuri, sannan ta tsaya aka yi.

Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri É—aya da na Adam.

Hauwwaliya har da tsalle, tana koÉ—a rumaisa.

Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.

A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haÉ—e cikin shadda iri É—aya, hatta huluna da agogo iri É—aya suka saka, motar na tsayawa, ta buÉ—e ta fice ta nufi wurin su Usman.

Abdallah ya din ga É—aukar rumaisa a hoto.

Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da É—an hasken da ba zai ishemu ba"

Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki"

Bisa ga al'ada, ƙawayen amarya da ƴan uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ƴar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ƴa da uba.
Abun ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ƴar mitsitsiyar yarinya.

Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maroƙa da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.

Rumaisa ta kalli yadda hall É—in ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba É—aya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na É—ibarta.

Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya riƙe hannunta, sai da ta ɗan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ƙoƙarin ɗaukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Adam amma ya riƙeta sosai.

Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ƙanwar zaratan maza har bakwai.

Iman ce ta fito stage, ta karɓi mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.

Jabir ba ƙaramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ƴar talakawa mara kunya.

Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ƙawayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.

Dangin su Adam sun so su farfaɗi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya riƙe gulmarsa.

Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta É—au ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin Æ´an mata.

'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta.

Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ƙawar amarya an sha ɗauri, ƴar baƙa kyakykyawa.

Iman ta ƙarasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku ɗaya, koda yake na san yaya Aliyu"

Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske, Æ´ar balarabiya ya aka yi ne?".

Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa".

Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri ɗaya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ƙamwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi haƙuri da ita, idan aka taɓata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza "

Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taɓa haɗata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.

Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.

Jabir ya ƙaraso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ƙarasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane".

"Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan ɗazu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaɓa.

"Yes na ji, zo mu je dai, ko na É—agaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a É—aura auren da namu"

Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.

Suna yin gaba ya hau ta da faÉ—an, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta É—aga kai suka yi ido huÉ—u, da sauri ta koma cikin wurin dinner.

Kwaɓe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".

"Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta ƙarasa maganar bilhaƙƙi za ta yi kuka.

"Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?"

Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ƙi fasawa, wayyo mama ni na gaji"

A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faÉ—a.

Mc kuwa koɗasu kawai yake yi, saboda shagwaɓa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga yaƙe, dan kar a fahimci wani abu.

Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.

Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?"

"Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare"

"Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.

Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya É—ebi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.

Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.

An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta É—aga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.

Hatta ammi ta je wurin, an yi mata liƙi sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi liƙi.
Chapter 39 · 0% Book details