← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 124

Sashe 21

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta kalli Sabir ta ce "Rigimamme, kai ba ka gane iyayenka ne, kowa ma ba zai É—auke ka ba?"

Iman ta tashi daga kan kujerar, ta karɓi Sabir ta bar falon, yadda ya ɗan shagala yana kallon iman ne ya sanya ammi jinjina kai a ranta ta ce "Yaushe wannan lamarin kuma ya kunno kai? Akwai ƙura idan Hajiya Lubabatu ta sani, amma da zan so faruwar hakan jabir ba shi da matsala'

"To ya gidan ya hajiyar taka?"

"Tana nan ƙalau Ammi, na je na duba Mahmud ne, na ji abun da ya faru sam bai yi mini daɗi ba ammi"

Ammi ta nemi wuri ta zauna ta ce "Kai dai bari jabir, lamarin É—an uwan nan na ku sai addu'a kawai, dan ku din ga yi masa faÉ—a, yanzu a garin wannan zafin zuciyar ta sa da ya yi masa illla ko ha salwantar masa da rayuwa fa?"

"Kai, ai takawa sai haƙuri, iya masa sai Allan da ya yi shi, amma iya ƙoƙari muna gaya masa gaskiya, sai dai ayi ta yi masa addu'a, Allah ya yaye masa wannan azababbiyar zuciyar"

"To Amin, Allah ya iya mana"

Nan suka cigaba da hira da shi da ammi, sai dai hankalinsa ya fi karkata ga yadda yake jin iman a ransa.

***
Cike da zullumi Samha ke cin abincin da yake gabanta, ba dan yana yi mata daÉ—i ba, sai domin zullumin abun da Jamil zai zo ya gaya mata, tun da ya gaya mata sun yi magana da turaki adam zai yi aure ta rasa nutsuwarta, so take ya zo ya gaya mata idan har hakan da gaske ne.

"Wai Samha ba zaki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki ci abincin nan ba, sai jagwalgwala shi ki ke yi?"

Samha ta ce "Mama yaya jamil nake jira, hankalina ba zai kwanta ba sai na ji abun da nake son ji".

Ƙanwar Samha, wadda daga ita sai ita mai suna Zainab ta ce "Ni wallahi Samha mamaki ki ke bani, wallahi babu yadda za a yi namiji yayi mini abun da Adam yayi mini na sake kallonsa, ke kam kamar mara zuciya, shiyasa na koma zaman hostel ma na bar miki gidan, yadda ki ke zubar da classic ɗin ki a kan gayen nan yana bani haushi, kamar wani ɗan gold"

"Enough zainab, kar ki sake saka mini baki a maganata, idan ba so ki ke na yi miki rashin mutunci ba".

Mama ta ce "Ya isa haka, ni bana son faÉ—a, daga dawowarki".

"Mama kin san dai babu yadda za a yi ina ganin gaskiya in ƙi faɗa, Allah ya taimaki soyayyar wahala" ta ƙarasa maganar tana tashi ta bar dining ɗin.

Samha gaba É—aya ba ta yanayi na yin faÉ—a, dan haka ba ta tankawa zainba ba ta shareta.

Jamil ne yayi sallama, mama ta amsa masa, Samha kuwa kasa amsa masan ta yi sai bin sa da ido da ta yi.

Ya nemi wuri ya zauna a É—aya daga cikin jerin kujerun falon.

Samha ta taso cikin sauri, ta ce "Yaya Jamil ya ake ciki ne? Tun É—azu nake jiranka"

Yayi shiru bai ce mata komai ba, "Yaya magana nake fa"

Ba tare da ya kalleta ba, ya ce "Samha ki na ji na?"

"Eh ina jin ka"

Ya taso ya zauna sosai ya ce "Samha, ina son ki saurareni da kyau, ki yi haƙuri ki cire Adam a ranki, a wannan karon ma ba zai aureki ba, domin kuwa ya tabattar mini da cewa mahaifiyarsa ta zaɓa masa wata matar, kuma turaki na dawowa za a kai masa kuɗin aure"

Ras! Gaban Samha ya faɗi, ta dafe ƙirjinta ta ce "What, again ta sama mata? Iman ko? Iman ce na sani, wai dan Allah me na yi wa matar nan ta tsaneni haka? A wancan karon ma ita ta yi uwa da makarɓiya ban auri Adam ba, a wannan karon ma ta kuma yi mini, na san ba wadda za ta zaɓa masa sai Iman"

Mama ta ce "To, ai a wannan karon sai ki kwantar da hankalinki, tun da an kuma kwatawa, sun nuna muraran ba sa ƙaunarki, sai ki ƙyale mata ɗanta ko?"

Samha ba ta iya cewa komai ba kawai ta tafi ɗakint, tamkar wadda take shirin zarewa, kaiwa ta din ga yi tana komowa a ɗakin, cikin zafin rai ta furta "Giwa me na yi miki, ki ke ƙyamar haɗa zuriya da ni ne? To wallahi a wannan karon ba zan yadda ba, ko ni ko ke ko mu rasa Adam daga ni har ke, har wadda zaki aura masan" ta yi maganar tana zubewa a kan gadonta cikin ƙunar rai.

***
Dukan teburin gabansa yayi, tare da tura kujerar da yake kai baya, ya ce "Aikin banza kawai, wai shi adam ɗin wanene da ganin ƙarshensa ya gagara, duk wannan abubuwan da aka yi a kansa, na gidajen jaridu da social media, yayi burus ya ƙi cewa uffan, sai ma wasu da yake turowa suna kare shi, wannan wane irin abu ne haka, ta ina kuma ya rage a ɓullo masa?"

Usman wakili yayi murmushi ya ce "Yaro man kaza, kai fa ka ce da na sakar maka ragamar komai, zaka iya komai ka san ta yadda zaka ɓullowa lamarin"

Khalifa ya ce "Haka ne Daddy, na yi duk iya yi na, ka sani na zaci yadda maganganun nan suka yamutsa hazo za su gigita shi, amma ya mayar da mutane mahaukata wato mu je ma mu yi ta yi kenan"

Senator ya yi murmushi ya ce "Na jinjinawa ƙoƙarin ka Khalifa, ban taɓa zaton zaka iya wannan ƙoƙarin ba ma, ka bani mamaki sosai kuma na yabawa ƙoƙarin ka, labarin da yake zuwar mini, hankalin yaron nan ba ya kanmu yanzu, kuma waɗanda suke jagorantar aikin tare da su, na saye wasu daga cikinsu, sannan kuma dama shi yake jagorantar aikin, kuma hamkalinsa ba ya kan aikin yanzu, na yi magana da shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, mun gama magana ba wani abu zasu wanke ni"

"Amma daddy kana ganin hakan ya wadatar, kar fa ya kuma ɓallo mana ruwa".

"Ai ba haka zan bar shi ba, ba ka da wata damuwa, na san abun da nake yi"

Khalifa yayi murmushi ya ce "To shikenan daddy"

***
Adam yana zaune yana aikinsa a office É—in sa, ya É—au wayarsa ya kira Bashir.
Suka gaisa Adam ya ce "Ka je ka maƙale ka ƙi dawowa, akwai update ne?"

Bashir ya ce "Babu wani update, sai dai na haɗu da barrister Sa'ad, ya ce akwai yiwuwar kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa a kan senator Usman wakili ba zai yi wani tasiri ba"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na sani, dama ban ji a raina za su yi wani abun kirki ba, amma babu damuwa, zuwa next week ko upper in sha Allah zan shiga Abuja, ina son zuwa EFCC".

Bashir ya ce "Meyasa ba zaka shigo next week ba?"

"Wallahi ammi ce ta sakoni a gaba da wani batu, yanzu da na ce zan yi tafiyar nan, za ta ce ban É—au abun da muhimmanci ba"

"Eh kuma haka ne, to shikenan Allah ya kaimu upper week É—in, ni ranar sunda in sha Allah zan shigo kano, dama da zaka zo next week É—in ne sai na jiraka, duk yadda ake ciki dai za mu yi waya"

"To shikenan Bashir, Allah ya yi mana jagora "

"Amin ya rabb, a tashi lafiya".

Ya ajiye wayar kenan, Jabir yayi sallama a office É—in Adam, Adam ya kalleshi ya ce "Me ka ke yi a nan lokacin aiki?"

Jabir ya harare shi ya ce "Ban sani ba, sai avoiding É—ina kake, ba na samunka a gida, gidanka ma baka nan, na ce bari na zo na ritsaka a nan"

"Amma dai ka san lokacin aiki ne yanzu ko?"

Jabir ya ce "Ai lokacin salla ne kawai ba zan datseka ba, kuma sai ka saurareni, ai ka san abun da ka yi ba ka kyauta ba, dole ka yi ta gudun haÉ—uwarmu"

Adam yayi masa shiru, ya cigaba da aikinsa.

"Adam, ka san yanzu kaf idon duniya a kan kan ka yake, amma na lura kai ba ka damuwa da hakan, baka gudun janyo wa kan ka magana, yanzu dan Allah da wani mummunan abu ya faru da Mahmud saboda zuciyarka me zaka ce? Yakamata ka sassauta wa zuciyarka wannan ƙiyayyar da ka ke yi masa, ko kana so ko ba ka so ɗan uwanka ne shi"

Adam ya yi masa shiru, wanda wannan shirun shine halayarsa da ta fi ɓatawa makusantansa rai.

"Ko ka kulani, ko kar ka kulani, na san dai kai ba kurma bane ba, kuma ka na jina, jibi in Allah ya kaimu zan je duba galadima" sai a yanzu Adam ya É—ago ya kalli Jabir ya ce "Ubangiji Allah ya tsare hanya, ka ce ina gaishe shi" Jabir ya girgiza kai ya tashi ya fice, dan halin Adam sai shi wasu lokutan.

***
Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba.
Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya ɗauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata alƙawarin yin hakan, a duk lokacin da ta buƙata.
Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faɗi, saboda tana matuƙar fargabar haɗuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba ɗayansa tsoro yake bata.

Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini.
Chapter 21 · 0% Book details