← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 124

Sashe 114

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma ta ce "Dan Allah zuciyar mutum ce a jikinka? Ka san me ake nufi da uwa da É—a kuwa? Kai banda dalilin sihiri da nake da tabbacin shi ya raba ammi da daddy, kai kana zaton akwai dalilin da zai sanya ta zuba ido ta barwa wata mata É—an ta.
To ai ko ni da abun da ke cikina bai zo duniya ba, da shi da Sabir, ban ga wanda ya isa rabani da su ba, kai idan aka ce za ayi asirin ma, sai na haÉ—a asirin da bokan na ci ubansu wallahi.
Dan Allah papa kaima ka sassauta wannan ƙiyayyar, yanzu bari in saka kaya in bika".

Ya ce "No, ki zauna a gida, zan je kawai"

Ruma ta ce "Hankalina ba zai kwanta ba, ka tafi da ni dan Allah, idan ba haka ba zan biyoka idan ka fita".

"Mimi kina da matsala, cikin nan ne bana son a gani".

Ta kalleshi ta ce "Saboda me?"

"Kin fi kowa sani ai, ba na son wani abu ya samu cikin nan naki, kullum cikin Addu'a nake yi Allah ya sa ki haihu lafiya, kin san komai ai"

"Babu abun da zai faru sai ikon Allah, ka tafi da ni saboda zatin Allah, hijjabi zan saka, ba wanda zai gan shi ai" kasancewar rumaisa ta ƙware a iya magiya, tamkar ƴar maroƙa, haka ya sanyata a gaba suka tafi.

Da shi da Nusaiba, da Ammi, haka suka rankaya asibitin da aka ce Mahmud yana can.

Gaba É—aya Ammi ba ta cikin nutsuwarta, takawa ya ce "Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin San ki na da high bp".

A rikicen dai Ammi ta ce "Kai ka san sani high bp, ka tambayar mini É—akin da yake dan Allah "

Ruma ta din ga kallon ammi cikin tausayawa, haka ta shafe shekaru da soyayyar nan da tausayi suna nuƙurƙusa zuciyarta, ruma ta jinjinawa mugunta irin ta mummy.

Ba ƙaramin razana ammi tayi ba, ganin Mahmud a kwance ba ya motsi, ga ruwa an saka masa, ga kuma oxygen da take taimaka masa yana numfashi, gefensa kuma mummy ce a zaune.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mahmud meya sameka haka?" Ammi ta yi maganar cikin rawar baki.

Jin muryarta ya sanya shi ya motsa, ya fara yi wa ammi nuni da hannunsa ta zo.

Cikin hanzari ammi ta ƙarasa, idonta na ta zubar da hawaye.

Ya miƙa hannunsa ya riƙe nata, sai dai ba baki, sai hawaye da yake zuba ta gefen idonsa.

Ammi ta riƙe hannunsa tana jejjera masa sannu.

Ya É—ora hannun a kan cikinsa.

Ruma ma ta ƙarasa gaban sa cikin kuka ta ce "Daddy meyafaru? Meya sameka?"

Wata irin miƙa yayi bakin sa yana zubar da kumfa, cikin sarƙewar numfashi ya ce "Daughter mutuwa zan yi. Ammi. Amm....Ammi na faɗa yau rumaisa, Ammi ki yi mini Addu'a cikina" yayi maganar tamkar numfashin sa zai bar gangar jikinsa.

Daga rumaisa har Ammi kuka kawai suke, Nusaiba ma kuka take.

Cikin kiÉ—imewa Mummy ta tashi cikin azama, ta ce "Mahmud ciwo ba mutuwa bane ba, kar ka sake cewa zaka mutu, haba Mahmud kar ka yi mini haka dan Allah " tayi maganar tana fashewa da kuka.

Ya buɗe ido a galabaice ya kalli Mummy, ya zare hannunsa daga na ammi, ya riƙo nata "Mummy na gode, na gode Mummy"

Ya sake zare hannunsa daga na Mummy, ya miƙawa adam, sannan ya cewa ruma "Ki ce masa ko sau ɗaya ya riƙe hannuna Daughter" ya yi maganar yana sake mimmiƙe wa.

Cikin matsanancin kuka da tashin hankali rumaisa ta kalli Adam ta ce "Papa dan Allah"

Adam da tuni ya karaya, kuma ya tsorata da lamarin, A  hankali  ya tako, ya zauna a kusa da rumaisa, ya saka hannunsa a na Mahmud ya rungume shi.

"Ina son ka ɗan uwana, Ƙaddara ce"

Mummy ta rasa in da zata sanya kanta, dan lafiya ƙalau Mahmud ya kwanta, idan har ta ce ba ta ƙaunar Mahmud ƙarya take yi. Saboda yayi mata biyayya fiye da yaran da ta haifa, kuma ta saka an ƙwace shi an bata shi, dan mugunta, amma kuma sai ta fara son sa daga baya.

Likita ne ya shigo, ya din ga yi wa Mahmud wasu allurai.

Bayan fitar likita, duk sun yi shiru sun zuba masa ido, Adam yana rungume da shi, rumaisa ta miƙe zumbur, dan tamkar ana mata raɗa ta ji komai.

"Me ya haÉ—a shi da jabir ne?"

Takawa ya ce "A ina?" Duk suka tsaya suna kallonta.

"Meyasa ya daki Jabir ya kulle shi?"

Duk suka zubo mata ido.

ganin da Mahmud yayi Mummy, tana cikin damuwa, ya sanya ya sakata a gaba, a kan ta gaya masa meke damunta, ta kasa ɓoye masa ta gaya masa komai. Ba ƙaramin girgiza yayi ba da jin abun da Jabir ɗin ya yi ba shi da ruƙayya, tun da ya fita a fusace, sai wayar Hajiya Lubabatu ta gani, ta tabattar mata da zata ga abun da za ta yi wa Mahmud muddin bai saka an sakar mata ɗa ba domin kuwa ta san muddin asirin jabir ya tonu ba zai yi sarauta ba, kuma ta fuskanci kamar yanzu Mummy ƙoƙari take taga Mahmud ne ya samu sarauta.

Sai a yanzu Mummy ta tuna da furucin hajiya Lubabatu.

Tashi rumaisa ta yi ta fara tashin Mahmud.

Takawa ya ce "Ya samu bacci fa"

"Tashe shi kawai, daddy"

Ya buɗe ido a matuƙar wahale ya kalleta.

"Meya haÉ—aka da jabir?"

"Bakomai" ya furta yana numfarfashi.

Ta ce "To koma me ka yi masa, babarsa ta ce zaka gani"

Takawa ya ce "Mimi bana son rigima fa, ke a ina ki ka ganta?"

Ruma ta ce "ÆŠazu da asuba ina bacci, na gansu su na faÉ—a, ban san a kan menene ba, amma ita ta ce zai gani, jabir yana police station ko?"

Ammi ta tashi ta kamo ruma ta zaunar da ita, ta ce "yi shiru da bakinki" shi dai takawa a iya sanin sa, suna tare da ruma, kuma ba wani wurin suka je ba, balle ace ta ji.

Mummy ta hau bala'in cewar mahmud sun yi faÉ—a da Jabir, amma ba wani abu da Hajiya Lubabatu ta yi masa.
Tayi maganar tana karewa saboda kar a gane sun samu saɓani da Hajiya Lubabatu, kuma muddin asirin lubabatu ya tonu, na ta ne ya tonu.

Takawa ya ce "Mimi ba ta ƙarya a cases irin wannan, zan yi bincike a kai, duk wanda na gano da saka hannunsa wani abu ya same shi, wallahi sai ya fuskanci hukunci ko waye shi".

"Matarka ba ta ƙarya ni nake yi kenan?"

Ammi da sauri ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ku yi haƙuri Takawa kar in sake jin bakin ka, rumaisa ku yi shiru mu yi masa addu'a".

Ruma ta ce "To ammi, amma wallahi ba ƙarya nake yi ba"

Mai sunan baba ne yayi sallama ya shigo, hankalinsa a tashe, "Subhanallah" yake ta maimaitawa saboda halin da ya ga Mahmud a ciki, dan kuwa sun yi waya jiya da safe, yake ce masa zasu haÉ—u yau.

Bai iya yi wa kowa magana ba, ya ƙarasa gaban gadon yana ambaton sunansa.

Gashi da an kira sunansa yake amsawa, ya buÉ—e idonsa ya kalli mai sunan baba.

"Mahmud, meyafaru haka ne? Wayarka na kira wata yarinya ta É—auka ta ce mini wai kana Asibiti" ya cewa mai sunan baba "ÆŠago ni"

Mai sunan baba ya sanya hannu biyu, ya É—ago shi, ya jingina da jikinsa.

Ammi ta din ga ajiyar zuciya ganin Mahmud a zaune.

"Ku yi haƙuri duk na tayar muku da hankali"

Mai sunan baba ya ce "Kar ka damu sannu ya jikin naka?"

"Da sauƙi, zan sha ruwa"

Mai sunan baba ya kalli Adam, Adam ya ɗaukko roba ya tsiyaya ruwa ya bawa umar, ya karɓa ya bawa Mahmud, ya karɓa ya sha sosai.

Ya ce "Alhamdilillah, ina ƙanwata tana lafiya?"

"Lafiya ƙalau, bata san me ke faruwa ba, na riga na fito sannan na kira wayarka, sannu Mahmud"

"Yauwwa yaya" kasancewar haka yake kiran umar.

Ammi ce ta ce "Mai sunan baba ya gida?"

Ya ce "Afuwan ammi, hankalina ne a tashe wallahi, ya gida ya mai jiki kuma?"

Ammi ta ce "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"

Mummy kuwa sai cika take tana batsewa, Fauziyya ba ta taɓa ƙarewa mai sunan baba kallo ba sai yau, lallai Iman ta auri mai kyau, da cikar zati.

"Me zaka gaya mini ne ka ke nema na?"

Mai sunan baba ya ce "Ka ji da jikinka ka samu lafiya, kana tambayata me zan gaya maka" yayi maganar yana murmushi.

"Am curious about it" yayi maganar yana lumshe idanunsa, saboda allurar baccin ba ta sake shi ba.

"Zan gaya wa yayanka ya gaya maka"

"Wai Takawa? Ba zai gaya mini ba"

Mai sunan baba ya ce "Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Bari sai na gama farfaÉ—owa, idan kuma na mutu....

"Shhhh, zaka farfaÉ—o in sha Allah, har aurar da kai sai na yi"

Ammi bakinta ya ƙi rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo ɗaya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu.

Ya kwantar da Mahmud, ya ce "Ka yi bacci, zan je gida ƙanwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka"

"Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci".

"Ba wata Mummy, na ammi zai ci" Rumaisa ta faÉ—a tana harare-harare.

Fauziyya ta buɗe baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san ƙarya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya ƙyale ta.

Ya kalli Adam ya ce "Ina son yin magana da kai"

Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita.

Fauziyya ce ta É—ora da rashin mutunci.

"An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa".
Chapter 114 · 0% Book details