← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 124

Sashe 119

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta ce "Ba dai rumaisa ba, takawa ya ce da saura ai"

"Wallahi ammi da gaske nake, yanzu yaya umar ya shigo ya gaya mini".

Nan da nan aka cika asibitin, Æ´an barka, sai dai ba ganin jariri, rumaisa kuma ba baki, duk wanda yayi mata sannu, sai dai ta jinjina kai kawai, amma ta san halin tashin hankalin da ta shiga a haihuwar.

Mama ta kalli rumaisa ta ce "In ce dai ta bakin ki ka haifo É—an naki, yau mata sun ga ta in da ake haihuwa" ruma tayi murmushi kawai.

Da ƙyar ta iya cin abincin ma, ta fara cewa ita a kawo mata ɗan ta fa, saboda lokacin da ta haife shi, tana gani ana ta fama, ya ƙi yin kuka yadda yakamata.

Abdallah ya sha tambaya a babbar headquarter Dss ta Abuja, dan sai da aka karɓi zanen aka sa shi sake yin wani, suka yi iya binciken da zasu yi, babu ko shakka Jamil ne, Wanda dama already yana hannunsu, takawa yayi kamar ya gaya musu da sanya hannun wakili, amma tayaya meye hujjarsa? Rumaisa ce kawai ta ji sun ambaci wakili, idan da wanda zai faɗi da sanya hannun wakili, to Jamil ne yakamata ya faɗa.
Duk wani report na bincike lokacin ɓatan aisha da suka yi, sai da suka gabatar da shi a wurin hukumar, laifin Jamil ya zama biyu, da na tuhumar fitar da sirrin hukumar, da kuma haɗa baki tare da yin garkuwa da ƙanwarsa, ga kuma ɓatawa Adam suna da yayi.

Ko da ana nunawa Jamil zanen nan, da Abdallah yayi, sai da ya zabura, saboda tabbas ya san shi ne.

Adam ya ce "Jamil ka tabattar wannan kai ne? Jamil me muka yi maka ni da Aisha? Idan ma wani abun na yi maka, meyasa zai shafi aisha? Ka haÉ—a kai da wakili ka cutar da ni?"

"Adam jin dalilin hakan ba shi da wani amfani a gareka, tun an riga an kama ni, sai ka je ka cigaba da rayuwarka, ka ƙyaleni. A kan me mahaifinmu zai fifita aisha a kanmu? Kuma duk wani abu na cigaba, ko na masarauta sai dai ya sanya ka a ciki alhalin gani. Wallahi da na san yarinyar nan ta gane ni, da ban barta ta rayu ba"

Adam yayi murmushi mai ciwo ya ce "Na gode sosai Jamil, sai dai ka sani, duk da ciwon hauka da nake fama, na tsaya ga Allah, shiyasa nake cigaba, kuma na barka da Allah Jamil, Jabir ma har shi da duk wanda ku ka cutar da ni, kamar yadda rumaisa ta faÉ—a, ta ce in bar ku da Allah, zan ga yadda zai yi da ku, na bar ku da Allah"

Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir.
Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ƙwarin gwiwa.
A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi.
Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce "A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke ɗin. Amma ina ga kamar yadda madam ta faɗa, ka yi ƙoƙarin gano wanda suka yi maka maƙarƙashiya, amma hukunta su sai Allah".

Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba.

Adam kansa abun ya ɗaure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ƙalau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba.

Gashi bai bai gama da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a buƙaci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin.

Sai dai cikin ƙudura ta Ubangiji mai kyauta da ƙari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, yaƙi kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba.

Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ƙular da ita, ta fara zaginta.

Mama ta ce "Ba zaki rufe mini baki ba?"

"Mama baki san me nake ji ba ne"

Mama ta ce "Dan ubanki Æ´aÆ´a biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba".

Ammi ta ce "Maman rumaisa ki yi haƙuri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daɗi"

Aka naÉ—o jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa É—aya sak da Adam.

Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce "Mimi, baby ya buÉ—e ido" yayi maganar cikin yarinta.

"Boy babynmu ya mutu"

Ammi ce ta karɓi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura.

Ƙarfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho, ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ƙarasa asibitin jikinsa duk a sanyaye.

Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa.

Ya durƙusa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?.

Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ƙarasa.

Ammi ta miƙa masa jaririn, ya karɓe shi ya buɗe zanin, kamar mai bacci, kamar sa ɗaya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne.

Ya miƙawa ammi shi, ya ce "Allah ya sa mai ceto ne" suka amsa da amin.

Mama tuni ta tashi ta bar ɗakin, ya ƙarasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta.

Kawai ta fashe da kuka ta ce "Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi"

Ya rungumota jikinsa ya ce "Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daɗi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi haƙuri ki daina kuka"

Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai.

"Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani" rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai.

Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune.

Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taɓrar da ruma take ba ta damunta.

Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman "Ina mai sunan baban?"

"Ƙarfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi"

Ammi ta ce "To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake ɓallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba.

Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda É—inkin da aka yi mata.

Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a É—aukko mai kula da ita.
Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti.

Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!.

Ayshercool.
08081012143.

*WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK*

Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can.

Mai sunan baba ya ce "Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba"

"Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba"

Ba tare da wani ɓata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba.

***
Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda biƙi, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru.
Tana zaune a É—akinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu.

Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai buƙatar ta gyara jikinta sosai.

Rumaisa ta ce "To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir".

Laila ta ce "Yaya bacci yake yi bai tashi ba"

Ruma ta ce "Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?"

"Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daÉ—in zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daÉ—in da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna"

Ruma ta ce "Sai wani yabon sa ki ke yi"

"Dole in yabe shi mana, dole a sarawa mama, yaranta gaba É—aya masu tarbiyya ne da nutsuwa, ke ce kawai mara ji"

Ruma ta ce "To nima papa yana yabona, yana sona a haka"

"Ai shi dama ba zai ga rashin jin da ki ke ba. Yauwwa mimi ya hatsaniyar gidan kuwa ta lafa?"
Chapter 119 · 0% Book details