Sashe 68
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har kusan ƙarfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta kuɓuta da Sabir.
A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?.
Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai 'Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba ɗaya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki taɓa ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da ƙani ga larura. Ashe ni kukan daɗi nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya.
Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure ɗan haƙuri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a ƙwace mini ɗa a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
Ga ɗan ta ba shi da lafiya, ɗayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ƙwace mata ɗaya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ƙwace Sabir ya auri ƙanwar anty aisha ya bata. Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'.
Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.
Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ƙasa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ƙarshe a nan ƙasa ta yi bacci.
Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaɗi a ƙasan zuciyarsa, dan ƙoƙari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan yaƙi yadda ya sallama cewar ya faɗa soyayya, haryanzu tantama yake yi.
Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta É—auke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba É—aya.
Wajen ƙarfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a ɗakinsa, ta zo a kaita makaranta.
Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.
Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi É—akin nasa.
Ciwon kwana É—aya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.
Ta ƙarasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe ɗin jallabiya ta ce "Sannu ka warke?".
Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya ƙalau, ya jiki?"
Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?"
Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na É—auka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?"
Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.
"Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ƙi amsawa wai sai an yi maka irin taka". Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.
"Barka da wannan lokaci ranka ya daÉ—e, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.
"Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta".
Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.
Sai dai a harabar gidan, ta haÉ—u da Mahmud, yana shirin fita.
Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?".
"Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi"
"Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta"..
Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buÉ—e motar ta shige.
Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya daÉ—e, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne".
Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi.
Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.
Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaɓa ta, in ta sai mata abubuwa".
Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a".
"Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde É—an bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu'a da fatan alkhairi"
Ya ce "wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki".
"Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu'a, tsakanin Ammi da wannan matar?" Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa.
"Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?"
A dai-dai nan, ya iso ƙofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru.
Ta ce "Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?"
Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faÉ—a mata ba"
Ta buÉ—e motar ta ce "Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy" ta nufi cikin makaranta.
Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ƙasa, gaba ɗaya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an ɗora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama.
Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ƙi auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daɗe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba.
Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya É—auki rumaisa zai kaita makaranta.
"Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi haƙuri mana".
"Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haÉ—insa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti ne da ita ba, kar a cutar da ita*.
Ammi ta ce "Kana da gaskiya, amma na ga ta su ta zo ɗaya, in sha Allah babu wani abu da zai faru, tun da ka ji sauƙi ma, sai ku tafi amma dan Allah kar ka ce zaka yi faɗa, kaga ba ka da cikakkiyar lafiya. Kuma ka sani ko a dalilinta komai ya dai-dai ta tsakaninka da ɗan uwanaka?"
Kallon idon ammi yake, tuni har hawaye sun cika mata ido.
"Shikenan ammi, ba zan yi magana ba, ki yi haƙuri, amma dole in raba shi da iyalina".
***
Da aka tashi daga makaranta, Adam ne ya zo ɗaukar ta, saboda ya ji sauƙi sosai, ciwon bai kuma tashi ba.
Tana ganinsa ta hau dariya "Ka warke ne ka zo da kanka, da adaidaita sahu zan hau na tafi ai".
Fuskar sa babu walwala, yayi mata banza, ya ja motar suka tafi, sai dai ta ga ya nufi gidansu, maimakon na Ammi, ganin ya na ta cika yana batsewa, ya sanya ba ta kula shi ba, ta cigaba da harkokinta.
Ko da suka je gida, su Asiya suka din ga yi musu sannu da zuwa, suna yi wa Adam sannu, dan baba uwani ta gaya musu, maigidan ne babu lafiya.
Ya wuce É—akinsa ta wuce nata, ta yi wanka, ta kwanta baccin da ba ta samu yi jiya ba.
Sai da aka yi la'asar, sannan ta tashi, taje kitchen ta haɗa shayi, ta zuba madara fal da milo, ta dafa ƙwai ta ci abunta, sannan ta ɗau littafinta, ta tafi ɗakin Adam.
Yana zaune a kan kujerar É—akin sa, yana dudduba wasu takardu, ta yi sallama ya amsa mata a ciki, ba ta damu ta je gabansa ta tsaya, ta ce "Albishirinka?"
Ya kalleta ya ce "Ya aka yi?".
Ta nuna masa littafinta, na assignment É—in da ta yi, ta zana malaminsu, ta ci 10/10.
Ya É—an kalli littafin da mamaki, sannan ya kalleta, alamar yana jiran bayani.
"In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing ɗina, ya ɗaga littafin ƴan ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ƙirƙirar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu ɗalibai masu ƙoƙari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa"
ÆŠan murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa.
Ya ce "You try".
"Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma Æ´ar tsana babba, sai lunch box É—ina"
Yayi mata kallon ba zaki girma ba.
"Ya naga kana kallona?"
"Mahmud, Alaƙarki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka".