Sashe 70
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi duk wadda ta kuma zuwa ta zageni, sai na rama, kayi zuciya ka mayar da ni gidanmu, sai ka tattaro su su dawo gidan nan su zauna, gida zan tafi dan ni ba banza ba ce, da za su din ga zagina ina jin su ba, me na yi musu? Nima ƙanwar wasu ce, kuma suna sona, dan wallahi ko za su kasheni, suka zageni sai na rama, ita kuma baba uwani ta cigaba da yi mini sharri" ta yi maganar tare da shigewa toilet.
Har dare taƙi ko sake fitowa, dan ko abincin dare ba ta nema ba, ta yi kwanciyarta.
Sai da takawa ya nemi, Asiya da barira ya tambayesu abun da ya faru, amma suka ce ba su sani ba, baba Uwani ta hana su hawa saman, amma sun jiyo su Fauziyya suna zagin rumaisa tana ramawa.
Daga nan gidansu ya wuce, bai ko je sashin Ammi ba, ya nufi sashin Mummy.
Ya tarar da su gaba ɗayansu, har da Mahmud da Mummy, da ruƙayya da Fauziyya, sai dai babu Samha.
Mummy na ganinsa ta ce "Ahh, takawa barka da wannan lokaci, ƙaraso mana, ya jikin naka, tun da na shiga ban sake zuwa ba, ashe ka samu sauƙi".
Ya ce "Eh"
"Sabuwa, ƙaro plates, a zubawa takawa abinci shi ma".
Ya girgiza kai ya ce "Na gode, Fauziyya"
Ta kalleshi ta ce "Na'am yaya"
"Kun je gidana É—azu?".
"Eh yaya mun je, zamu sake dubaka ne kuma baka nan, matarka ta yi mana rashin mutunci, har da zagin baba uwani".
Adam ya ce "Daga yanzu, idan har ba alkhairi ne zai kai ku gidana ba, kar ku sake zuwa, ina baku wannan saƙon ne har Samha, idan ma baku gaya mata ba, ni zan gaya mata. Kar ku sake zuwar mini gida ku ci mutuncin mata ta, ni na ajiyeta ba ita ta ajiye kanta ba, kuma ban aurota, dan ku je ku ci zarafinta ba, ita Aisha dama taku ce, kuma mai haƙuri ce. Wannan kuma tawa ce, sannan ba zata iya jure abun da Aisha ta jure ba, yarinya ce ba zan lamunci a saka mata tension depression ya kamata da ƙuruciyarta ba".
Baki a sake Mummy ta ce "Yanzu matarka ka fifita a kan ƙannenka, duk da sun gaya maka ta wulaƙanta su? Bayan kai suka je dubawa?".
"Mummy ko dabba na ajiye na ce nawa ne, bai kamata a je ci mutuncinsa ba, idan har ina da kima a idon su ba, balle ɗan adam na ajiye, idan banda rashin girma, me zai saka su biye mata, tun da ba sa'arsu ba ce ba, na san rigimammiya ce, amma ba ta yi haka kurum, ku kiyaye, aje a ci mata mutunci ace mata ƙwaila, ko ba mace ba ce, ni a idona mace ce kamar kowa. Dan haka Please allow her to enjoy her marital home. Ko ba ku yi zumunci da ita ba, ni na isheta, na san yadda nake bi da ita mu zauna lafiya"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Hmm, wannan dai kashedin na samha ne, zuwa aka yi a gaya mana ana son ta kenan".
Ya tashi yayi murmushi ya ce "Ta cancanci hakan Mummy, a rashin Aisha ita ce uwar ɗana, idan na bari aka wulaƙanta ta, ni aka yi wa, dan haka a kiyaye"
Mummy ta yi shiru, tana saƙa wani abu a ranta, lallai akwai ƙura ba ƴar kaɗan ba, Samha tana ruwa, dan ba ta tunanin baba uwani na abun aka sakata yadda yakamata.
Mummy ta ce "Gaskiya ne, tayi rawar gani kam, ta cancanci a kula da ita. Duk da ka ɓoyewa duniya ita, da muhimmancin abun da tayi maka"
"Ni ta yi wa, ba duniya ba, dan haka ni yakamata na girmama abun da tayi mini".
Mahmud kuwa, ya kammala cin abincinsa, danna wayarsa kawai yake yi.
Har Adam ya wuce shi, ya dawo ya zauna a kusa da shi, yayi ƙasa da muryarsa yadda shikaɗai zai ji me yake cewa ya ce "Am warning you, stay away from my family, da ɗana, da kuma matata"
Mahmud ya É—an kalli Adam ya ce "Ban ji zan iya ko É—aya ba, ina son É—anka, ina girmama matarka, kasancewar tana girmamani, we are having a deal together, dan haka you should stay away from us"
Wani irin zafi maganganun sa, suka yi wa adam, amma ya shanye ya ce "Shikenan, idan ka ƙi ji, ba ka ƙi gani ba" ya tashi ya fice.
Mummy kasa zama tayi, ta tashi ta bar falon, Fauziyya kuma suka cigaba da caccakar rumaisa, suna bawa Mahmud labari.
Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu'a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi.
Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan.
Yau ya ji ƙwarin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa ɗaki, idak bai tashi ba ma, ta din ga ƙwale-ƙwale kenan sai ya tashi ko baya so.
Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba.
Kai tsaye ya tafi É—akinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa.
"Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?"
"Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori"
"Dalla tashi ki shirya zan makara"
"Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka ɗora mini laifi, kai ƙannenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida" tayi maganar cikin tsan-tsar takaici.
"Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin zaɓi mu rabu, abu ne mai sauƙi, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki" saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice.
Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe.
A ransa ya ce "Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?".
Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara.
Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa ƙofar makaranta, ta buɗe ƙofar motar ta ɗau alawarta ta fice.
Yayi murmushi ya ce "Su mimi ba zuciya in dai a kan kwaÉ—ayi ne" tana jin sa a ranta ta ce "So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba".
Ana tashinsu ya je ya É—aukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin daÉ—in hakan nan, saboda yana É—ebe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir.
Ammi ta ce "Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi, sun je jiya da yamma"
"Ina fatan dai ba wata matsala"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan"
Ammi ta yi murmushi tana dafa kafaɗar ruma ta ce "Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya ɓoye abu. Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar. Babarsu ta zo ɗazu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba ƴan uwansa ba".
Rumaisa ta waro ido ta ce "Papan? Amma ni kuma jiya yayi mini wulaƙanci, suka ɓata ɗaki wai ni zan gyara".
Ammi ta ce "Ki yi haƙuri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani"
"To Ammi in sha Allah"
Ammi kuwa daÉ—i ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren.
"Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun ƙi zuwa gidanmu".
Ammi ta ce "Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba".
Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita.
Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce "Ahh babar sabir, Æ´ar gidan amminta"
Ruma ta ce "Mama na tabattar kin daina so na gaba ɗaya, baki taɓa zuwa gidana ba".
"Ai na san kina lafiya ne, ya É—an naki ya maigidan?"
"Ɗana lafiya ƙalau, maigidan kuma mun yi faɗa bama magana"
Mama ta ce "Kun yi faÉ—a ba kwa magana saboda baki da hankali?"
Cikin sangarta ta ce "Mama faÉ—a yake yi mini a kan abun da ba laifina ba"
"Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki faÉ—a ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci, Æ´an uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki faÉ—a sai ki daina yi masa magana? Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba? Kin ga ki kiyayeni".
"To mama kawai sai na bashi haƙuri"
"Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai É—a'a, tun da ke ba kya ji"
Rumaisa ta ce "Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai ƙara aure ba, daga ni shikenan".
"Kar ki canza hali, na fasa zuwa gidan naki ma, sai kin yi hankali"
Kan ta yi magana, mama ta katse wayarta, ruma ta ajiye wayar tana tura baki.
Tayi shiru tana nazarin maganar mama, ba ƙarya duk abun da take so yana bata, ko bai amsa mata ba, za taga abun ya bata.
Kuma ga ammi ta ce ya je ya yi wa ƙannensa faɗa.
"Ai shikenan, zan daina fushin, amma ba zan bashi haƙuri ba"
Har yamma tana gidan Ammi, sai magariba, sannan takawa yayi waya, ya ce Sidi ya mayar da ita gida.