← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 124

Sashe 57

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta É—auka ta mayar musu.
bacci sai ɓarawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa saɓanin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba ya jin daɗin komai, ko abinci ya kasa ci, ya rasa ta ina zai fara.
Sai gefin asuba barcci ya É—auke shi, ana kiran salla shi ma ya tashi.

Ko da ya dawo daga sallar asuba, neman wuri ya yi ya zauna, ya cigaba da Adduoi, sai da rana ta É—aga, sannan ya tashi ya shiga wanka.

Har ya kammala shirinsa, bai ji motsin ruma ba, gashi yau Monday.
Gaba É—aya ba shi da kuzari, balle karsashi, ya nufi É—akinta.

Ta na tsaye a gaban mudubi, yau ta fara saka uniform ɗin ta, ta saka skirt ɗin ya zauna a jikinta cif, da taimakon jigidar da ke ɗaure a ƙugun na ta.

Ta saka ƴar cikin, ta ɗaga kai tana ƙarewa wuyanta kallo, ta na shafa wurin da ya yi mata rauni. Uniform ɗin sun yi mata kyau sosai.

ÆŠan gyaran murya ya yi ya ce "Haryanzu ba ki shirya ba, balle ki karya yau monday fa"

"Na gama shiryawa, uniform nake ƙarasa sakawa".

Ya juya ya tafi dining ya zauna, da niyyar ko yaya ya ci wani abu, dan ya na jin yunwa, amma ya ji bakinsa babu É—anÉ—ano.

Ta fito ta ajiye jakarta a kan kujera, ta nufo dining É—in.

Ta buɗe food flask ɗin abincin, soyayyiyar doya ce da miyar ƙwai.

Ta ce "Bari na yi bisimillah, na ci abincinka, yau ban yi girki ba, ko sallar asuba ba ka tashe ni ba, da safe na yi salla kuma alhaki a kan ka".

Ta kama kujera, ta haye saman dining ta zauna.

Kallon ta yake, yana jiran ta yi maganar abun da ya faru jiya, amma ya ga ba ta yi ba, ta haÉ—a shayi ta tura masa kofin gabansa, ta É—au na ta.

Jujjuya cokali ya din ga yi, amma ya gaza kai wa bakinsa ya sha.

"Wai da zafi ne shayin?" Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kallon shayin.

"To in ƙara maka madara?" Sai a wannan karon ya girgiza mata kai alamar a'a.

"To ka sha mana, ka ci abincin"

A hankali ya kai kofin bakinsa, sai dai zuƙa ɗayan da ya yi, sai da yayi ta fama sannan ya haɗiye shi, ƙarshe ya tashi ya ce mata, ta same shi a mota.

Kasancewar rumaisa tana son shayi, haka ta haÉ—e nasa da nata ta shanye abun ta, ta É—auki jakarta, ta ga tasa jakar ma ya bar ta a wurin, ta É—auki jakarta da tasa, ta fita.

Ta tarar da shi, ya kifa kansa a sitiyarin motar, sai da ta buɗe motar, sannan ya ɗago. Idanunsa sun yi ja, kamar am zuba masa abu a cikin su, har sai da ta fara fargabar ko hayaƙin ne zai fara fitowa, amma ta ga idon ya tsaya a haka, ya fara jan motar a hankali.

"Wai zazzaɓi ka ke yi ne?" Bai amsa ba, sai lumshe ido da yake ya na buɗewa.

"Yauwwa papa ka san me? Na san ba zaka amsa ba, haka mai sunan baba yake yi, shiyasa bakomai ka ke yi mini na ji haushi ba, na san ka na ji na. Dan Allah ka sai mini lunch box mana, in din ga zuba abinci ina tafiya da shi makaranta".

"Lunchbox na Æ´an primary ne"ya faÉ—a a hankali.

"Eh, ni shi nake so, ƙarami mai kyau" tana cikin maganar traffic ta tsayar da su, sai ga mai alawar madara, rumaisa ta tsayar da shi ta kalli Adam ta ce "Papa ɗan sai mini". Ya kawar da kansa gefe, yana kallon wajen window.

Ta saka hannu ta zuge jakarsa da ke hannunta, ta ga kuɗi a ciki, ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Allah ya kama ka, ga jakarka a hannuna ai, na ranci dubu ɗaya, idan na gama makaranta, na samu aiki, salaryna na farko zan biyaka" sai da Adam ya kalleta jin abun da ta ce, ta bawa mai alwar madara, ta ce ya bata ta duka.

Gaba É—aya ba shi da kuzarin da zai biye mata, dan haka bai ce mata uffan ba.
Ita kanta ta lura shirun nasa ya yi yawa, shi kuma mamaki yake yadda duk surutunta, da mitar tsiya amma ta yi shiru, ba ta ce masa komai ba, a kan abun da ya faru.

Suna tafe ta cika masa kunne da waƙoƙin indiya, ga abun da yake damunsa, ga waƙarta da ta addabe shi, kuma ya san da ya kuskura ya ce ba ya so, za ta tsiri wani abun.

Sai kuma ta koma waƙe-waƙe, masu kama da habaici "Idan mutum ma bashi da lafiya, shan kunu ba magani bane ba. Idan kuma wani abu ne yake damunsa, rashin cin abinci ba maganin matsala bane ba. Cikin mutum ne zai gaya masa, ulcer ta kama shi na ruwan rumaisa, lalaaalallaaa, alawar madara da daɗi".

Duk ta yi ta gama ya na jin ta, ya kaita ƙofar makarantarsu, ta sauka ta ɗau jakarta, ta shiga.

***
Ya na tsaye ya na saka lense ɗin rigarsa, sai kokowa yake ya saka, amma ya kasa sakawa saboda hankalinsa ba a kan abun da yake yi, yake ba, jin zuciyarsa yake tamkar a kan wuta, wata ƙishirwar baɗini ce ke addabar ruhinsa, abun da yake ji a jikinsa, zai iya rantsuwa da abun da zai kashe shi, tun da Allah ya sa mama ta kawo shi duniya, bai taɓa jin irin sa ba, duk yawon zuwa makaranta da yake yi, da yadda ƴan mata, ke kaiwa suna komowa a gabansa, bai taɓa damunsa ba, amma yau ba gaira ba dalili ƴar mutane ta tsaye masa a tunaninsa.
Mussman jiya da ya ga status É—in ta, ta yi video ita da sabir, ta É—ora, ya kalli status É—in nan, bai san adadi ba, sai da ya fara bawa kansa haushi. Kuma ya kwanta bacci ya din ga mafarkinta, mafarkin da sai ya kai shi ga danganawa ya tsarkake jikinsa kan ya yi salla.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar da hankali, ya gama abun da yake yi, ya fita ya yi wa mama sallama ya tafi.

Sai dai a ƙasan zuciyarsa ya na jin, da zai samu dama ya ganta, wataƙila atleast, zai rage abun da yake ji a tsakanin ƙirjinsa zuwa zuciyarsa, amma ta yaya?.

***
Sanin halin rumaisa na rashin isasshen saiti, ya sanya ba ya wasa da abun da ya shafeta, duk da halin da yake ciki, da lokacin tashi ya yi, haka ya tafi É—aukota.

Sai dai ya shafe mituna goma sha biyar, a tsaye, bai ganta ba bai ga alamarta ba.

Sai da ya É—an tsorata, ya fara addu'a Allah ya sa ba tafiyarta ta yi gida ba, saboda abun da ya faru.

Har zai shiga mota, ya shiga cikin makarantar yana duddubawa, can ya hangota, a cikin liluka, ta ajiye ɗan ƙaramin hijjabinta, sai fama take yi kai ka ce wata ƴar primary 2.

Sai da ta hango shi, sannan ta saukko, ta É—auko jakarta da hijjabinta, ta zo ta wuce shi, ta tafi mota, ba tare da ta ce masa uffan ba.

"Wallahi idan ka kuma daɗewa ba ka zo da wuri ba, sai na tafi gida, idan na ɓata a hanya shikenan"

Ganin ya zame mata tamkar kurma, ya sanya ta É—an fara tsorata, shirun na sa yayi yawa, dan kafin su yi aure ne yake da yawan shiru, da suka yi aure ta fuskanci yana da baki, amma daga jiya zuwa yau, shirun ya wuce hankali.

Ta yi shiru ta zuba masa ido, damuwa kwance a fuskarsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi, ta daina yi masa surutun, da neman magana.

Har suka je gida, tana tunanin, ko dai wani abun ta yi masa, yake jin haushinta, har ya daina cin abincin?.

A karo na farko tun da ya kaita makaranta, ya tarar da ita a falo, ta duƙufa ta na rubutu, bai san me take rubutawa ba, ya nufi in da take ya tsaya a kanta, takardar kifi ce, da wani math a jiki, da gani question paper ce, take ta fama sai ta yi soloving, ko a ina ta samo takardar oho mata.

Ƙafarsa ya saka ya daki ƙashin bayanta, take ta banƙare tare da ɗan yin ihu, dan ta ji zafi.

Ya zauna a kan kujera, ya ce "Samo mini abun da zan ci".

Sai da ta É—an tura baki, a ranta kuma ta ji daÉ—i da ya kulata, har ya nemi cin wani abu.

Bayan ta tashi ya zauna ya na duba litatafan ta, maths dai gashi nan, ta na cin abun ta, daga assignment har classwork.
Sauran subjects kuwa, har 2/10 ruma ci take.
Assignment ɗin ma ba yi take yi ba, babu wanda ya fi kunna shi, har haushi ya saka shi dariya, irin subject ɗin basic technology, an basu assignment a kan cewa, a matsayin ka na matashin ɗan makaranta, wani abu ne zaka iya ƙirƙira, da ka ke ganin zai amfani al'umma da ƙasa baki ɗaya.

Shafi guda ta ware, ta zana malamin nasu, riƙe da maka a hannunsa, yana bayani, sai dai a real portrait of him, kai ba ka ce ita ta yi zanen ba, very accurate, a matsayin amsar tambayar.
Ya yi shiru yana shafa haɓarsa, wasu lokutan yarinyar kamar bil'adama ba.

Ta dawo da plate a hannunta, ta ajiye masa a gabansa.

"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata litattafanta"

"Me na yi?"

"Karatun ne ba kya ganewa, ko kuma meyafaru ki ke cin wannan makin".

"Ni fa bana gane turancin da ake yi, kuma ba za ayi wa mutum bayani da hausa ba, wai ba a hausa a makarantar, yanzu haka kuÉ—in vanacula ya kai dubu uku ake bi na, wai idan ka yi hausa É—ari biyu, ina zan iya na ce idan ka zo a gaya maka zaka biya".

"Saboda ke ki ke nemo mini kuɗin ko? Kin taɓa ce mini ga abu baki gane ba, in koya miki?"
Chapter 57 · 0% Book details