← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 124

Sashe 5

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ammi ta yi tana faɗin "Ƴar gidan ammi, maman sabir"

Ta durƙusa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska.

Mama ta ce "Bisimillah ku zauna"

Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska.
Ruma ta ce "Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?"

"Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya"

Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna.
Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan.

Ammi ta ce "Ke maman sabir ya ki ka bar Æ´an maza da aikin gida?"

Ruma ta ce "Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su. Ammi wannan wacece?" Ta yi maganar tana nuna iman.

"Ƙanwar takawa ce, ita ce ƴar autana"

"Tubarkallah mai kyau da ita" iman ta yi murmushi ta ce wa ruma "Ina wuni?"

Ruma ta zaro ido ta ce "Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo". Dariya suka yi mata ammi ta ce "Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce" ruma ta yi dariya ta ce "Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni".

Ammi ta ce "Yau ba zaki É—au sabir É—in ba?"

"Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake É—aukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne"

Ammi ta ce "Subhanallah, me ya yi miki?"

"Ƙyaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi" ta ɗauke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma baƙa ƙirin ta cika masa kai. Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama.

Wata irin razana iman ta yi da ya shigo É—akin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba.

Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya durƙusa ya riƙe mata kunne ya ce "Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?" Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce "Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili". Ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya ɗau sabir a kan cinyarta ya yi waje.

Ammi ta din ga murmushi, gaba É—aya rayuwar rumaisa burge ammi take yi.

Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba.

Ammi ta dubi mama ta ce "Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma"

Mama ta ce "A'a, jinina ne ya hau"

"A tunanina zuwa yanzu mun zama ɗaya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki ɓoye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu'a"

Mama ta nisa ta ce "Babar ƙawar rumaisa ce ta zo, take gaya mini maƙwabtana na ta yaɗa jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta  haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne kaɗai ya san yadda muka yi da ɗan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maƙwabta kuma?"

"Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun ɓata mini sunan ƴa, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki".

Ammi ta ce "Wallahi ba sai kin faɗa ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi haƙuri basu isa su ɓata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama" shigowar rumaisa ɗakin ce ya sanya ammi sauya maganar.

Suka miƙe zasu tafi, rumaisa ta ce "Ammi, an ɗora mana abinci fa, ku tsaya a gama"

Ammi ta ce "Tuba muke, muna sauri ne, ayi haƙuri" rumaisa dai ba haka ta so ba.

Suka fito zasu tafi, mama ta ce ina ga mai sunan baba yana waje da sabir.

Suka fito aikuwa yana wajen, ammi ta ce "Iman karɓo sabir"

Jikinta har rawa yake yi, saboda gaba É—aya mai sunan baba tsoro yake bata.

Kamar munafuka sai sunkuyar da kai take, ta miƙa hannu za ta karɓe shi, amma shiru bai bata shi ba.
Sai da ta É—aga kai suka yi ido huÉ—u, gabanta ya sake faÉ—uwa, har numfashinta ya tsaya na wucin gadi.

Ganin yadda ta tsorata ta rikice, sai da ya bawa mai sunan baba haushi, shi ba dodo ba meye na wani tsorata.

Ammi ta saka sidi ya buÉ—e booth, ya É—ebo cartons na lemo da kayan marmari, na dubiyar mama.

Ammi ba ta tsaya ba, dan ta san mama cewa za ta yi yayi yawa, suka shiga mota suna É—aga musu hannu.

Tun da suka tafi ammi take saƙawa da warwarewa a zuciyarta, dole mama ta shiga damuwa, babu uwar da za ta ji daɗin a ɓata sunan ƴa a cikin unguwa dan wannan kawai sai ya hanata auruwa.

Suna tafe Nusaiba da iman na ta yi wa rumaisa dariya, yadda take gudanar da al'amuranta da yadda yayyenta ke kula da ita.

Tun a hanya ammi ta kira adam a waya, ta ce idan an yi sallar magariba tana son ganinsa.

Kamar yadda ta buƙata ya je ya sameta, ta idar da salla tana lazumi, bayan ta kammala ta dube shi ta ce "Mai ka yi wa rumaisa ne? Take cewa da tana da zuciya ba zata sake ɗaukar sabir ba?"

Ya kalli ammi ya ce "Wani abun ta ce na yi mata ne?"

"Ba ta ce ba, amma abun da ta faÉ—a ya tabattar mini da wani abun ka yi mata"

"Ba wani abu bane ammi, na mata gargaɗi a kan zuwa gidan nan ne? Idan aka fuskanci wacece, za'a iya ƙoƙarin citar da ita ko cutar da sabir ta hanyar ta".

"Na ji, yanzu ba wannan ba ma, wata shawara na yanke a matsayina na uwa na kira ka na sanar da kai, ba dan kana da hakki a kan abun ba ma sai dai ka ji na zartar".

"Wane hukunci kenan?"

"Ina son ka auri rumaisa!!!"

Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Chapter 5 · 0% Book details