Sashe 17
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adam har mamakin ƙaunar da Ammi take yi wa rumaisa yake yi, tabbas da so samu ne, Samha ta maye gurbin aisha, dan ita ta isa mace da hankalinta da iliminta, kuma Samha ta daɗe tana son shi, ya san hakan, amma ammi ta dage a kan wannan ƴar yayyiyar Yarinyar.
Ya numfasa ya ce "Allah ya kyauta"
Ammi ta miƙa masa leda ta ce "Gashi nan, sabuwar jakar makaranta ce, da litattafai da turare, ka kai mata ka ce ina gaisheta"
Adam ba yadda ya iya, ya karɓa ya amsa da to.
Ya fita riƙe da ledar kayan a hannunsa, ya san zuwansa wurin Yarinyar nan, ba abun da zai ƙara masa sai raini.
A harabar gidan ya tarar da Mahmud, tun da ya dawo yana ganin shige da ficen motocinsa, amma basu ta ɓa haɗuwa ba sai yau, yana tsaye a wurin parking space ɗin Adam, kusa da in da zai ɗau motarsa.
Adam bai kula shi ba, shi ma bai kula shi ba, ya je ya buɗe motarsa ya kunna, ya ɗan jima a ciki, amma ya ga Mahmud ba shi da niyyar matsawa, ya din ga danna horn, amma Mahmud ya yi burus, ba tare da wani ɓata lokaci ba Adam ya bawa motar wuta, yayi reverse, ai kuwa ya buge Mahmud, ko kaɗan Mahmud bai kawo Adam zai yi masa haka ba, kan ya ankara ya ga Adam yana ƙoƙarin bi ta kansa, ba shiri ya mirgina, Adam ya ja motar da gudu ya bar gidan.
Ma'aikatan gidan suka yo kan Mahmud suna yi masa sannu, suna ƙoƙarin ɗaga shi, sai dai ciki gwasalewa ya nuna musu shi zai iya tashi, sai dai abu kamar wasa, da ya miƙe ɗin ƙafa taƙi takuwa.
***
Rumaisa tana hanya tana addu'a, Allah ya sanya yaya Aliyu ya dawo, Allah ya sa komai ya wuce, sai dai ko da ta iso gida, ta tarar da Usman da mai sunan baba amma babu Aliyu. Cikin damuwa ta ce "Yaya usy ina yaya Aliyun yake?"
"Ke, case ɗin nan fa maƙabcinmu malam shamsu, ya yi uwa yayi makarɓiya yana ta kambama abun, gaba ɗaya ma sun ƙi saurarmu a station ɗin, wai sai DPO ya zo, DPO na zaci wanda ku ka yi case ɗin nan ne kwanaki, ashe an canza wani, sun kafi wai sai an je state cid tun da aka yi iƙrarin kisan kai".
Rumaisa ta ce "Na shiga uku, ba fa yaya Aliyu ne ya ce zai kashe shi ba, shi ne ya ce zai kashe shi".
"Koma menene ba ke ki ka janyo ba rumaisa, duk abun da mutum zai gaya miki sai dai ya shiga ta kunnen dama ya fita ta hagu, saboda wautarki kin jefa É—an uwanki a wahala"
Usman ya ce "Dan Allah mama ki daina faɗar haka, ƙaddara ce"
A fisace mama ta ce "Rufe mini baki, ko na make ka, ai duk gidan nan babu mai koya mata rashin ji irin ka"
"Allah ya baki haƙuri, ba ri mu yi salla mu koma".
Adam kuwa ko kaÉ—an bai ji babu daÉ—i ba abun da ya yi wa Mahmud, dan a lokacin nan yadda ya hasala, da ya samu dama sai ya taka shi da mota uban kowa ya huta, ya sauke masa wannan girman kan da rashin mutuncin da yake ji da shi.
A haka yake wurin aiki, ya gama abun da yake yi ya fito, yana da niyyar zuwa gidan gona, sai dai dole ya je ya kai wannan saƙon kan mama ta ɓata ranta.
Mahmud kuwa ƙarshe, sai ka shi sashin Mummy aka yi, a rikice take tambayarsu maiya same shi, suka gaya mata Adam ne ya buge shi da mota.
Nan da nan ta hau ta fara bala'i "Wannan wane irin wulaƙanci ne, anya Adam bai fara shaye-shaye ba? Ko dai haryanzu haukar ce a kansa, tayaya zai taka ka da mota? Wallahi ba zan lamunta ba sai na ɗau mataki"
Mahmud ya ɗan cije lips ɗin sa ya ce "Ki rabu da shi zan rama ne, yanzu ni dai ƙafata zafi take yi ki yi wani abu a kai"
"Wallahi ba zan ƙyale ba, Fauziyya ɗauko key mu tafi asibiti kawai, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu ƙafar ba"
"Mummy, dan Allah ki rabu da shi, am just testing his anger, ashe yana nan a yadda yake bai canza ba" yayi maganar cikin zolayar Mummy.
Cikin fushi ta ce "Ka rufe mini baki, this is an serious issue, ba zan bari ba" ganin yadda ta ɗau zafi ya sanya shi yin shiru yana kallon ƙafarsa.
A ƙofar gidan su rumaisa, Adam ne a tsaye, yake kiran wayar Aliyu, amma shiru bai ɗauka ba, wayarma a rufe take, ya kira har ya gaji, ya aika yaro ya ce ace ana sallama.
Usman ne ya fito, domin duba waye, ya tarar da Adam a tsaye, ya ƙarasa yana wani basarwa, suka gaisa sama-sama.
Adam ya ce "Aliyu nake nema, na kira wayarsa ba ta shiga"
Usman ya kalleshi, ya lura ta su ta zo É—aya da Aliyu sosai.
Ya ce "Ya ɗan haɗu da tsautsayi ne" ya bashi amsa a taƙaice.
"Wane irin tsautsayi kuma?"
"Eh waccan yarinyar ce ta tsokano ɗan daba, ya je tare mata, kuma dama ta yi rigima da maƙwabta, shi ne mai gidan ya saka aka kama su, tun jiya muke zuwa police station, an ƙi sakinsa, yanzu ma komawa zamu yi"
Mamaki ne ya sha kan Adam, duk rumaisan ita kaÉ—ai ta janyo wannan tarzomar.
Cikin mamaki ya ce "Wai duk ita wannan Yarinyar ce ta yi faÉ—a da É—an daban?"
Usman yayi wani irin murmushi ya ce "Wannan ta wuce tunaninka, ka san ƙanwar maza ce, bamu raineta da tsoro ba"
Adam har cikin ransa ya ji babu daÉ—i kama Aliyu da aka yi, ya ji da rumaisan aka kama ita da ta janyo abun.
Ya ce "Ko zan iya magana da maman?"
Usman ya ce "Ok, bari na yi mata magana".
Bayan an yi wa Adam iso ya shiga gidan, ya tarar da rumaisa a takure a falon mama, sai rarraba ido take yi, suka gaisa da mama ya sanar mata da Usman ya gaya masa abun da ya faru"
Mama ta ce "To, yakamata ka sake tunani a kan auren nan naku, ku gidan sarauta ba kwa son shirme, rumaisa kuma Allahn da yayi ta ba ta ji ko kaɗan, faɗa da maƙwabta faɗa wai har da ɗan daba, yaron da har kisan kai yake yi"
Adam ya kalli in da rumaisa take, ta haÉ—e rai saboda yadda mama ke kwance mata zani a kasuwa, ya ce "Me ya haÉ—aki da Æ´an daba, har aka kama Aliyu?"
Shiru ta yi tana wulƙita ido, mama ta ce "Zaki yi bayani ko sai na mareki?"
Ƙasa-ƙasa da murya ta faɗi abun da ya faru, ta wani fannin tana da gaskiya, a kan me zai aiketa sayen sigari.
Adam ya ce "Ba damuwa mama, bari mu je a fito da shi, ba wani state CID, wani station É—in ne?"
Usman ya ce "Dama yanzu zamu koma da mai sunan baba sai mu tafi gaba É—aya " wani mugun kallo da mai sunan baba ya yi wa Usman ya sanya yayi shiru, Sarai Adam ya ganshi, dan haka ya ce "Bari mu je da wuri, kuma dole ita ma a tafi da ita".
Mama ta ce "Idan ma sun ƙi yarda, ku basu ita ku dawo mini da Aliyu" sanin ba ta da gaskiya ya sanya ta sunkuyar da kai ta yi shiru.
Mama ta so bin su, amma kasancewar yanzu magana ake ta siriki, mama ba zata iya shiga motar Adam ba.
Bayan tafiyarsu mai sunan baba ya ce "Amma ba kya ganin yawan shigarsu cikin al'amuranmu da yi mana alfarama, ba zai saka nan gaba su cigaba da kawo buƙatunsu ba, kuma ba yadda muka iya sai mun bi ba?"
Mama ta ce "Babana ka san na fi kowa taka tsantsan da gudun duniya, bana jin hakan, shi ya sanya na amince"
Ya É—an rausayar da kai ya ce "Shikenan, bari na bi su a napep"
Suna tafe Adam yana kallon rumaisa ta mudubi, sai wani gyatsine baki take yi, tana harare-harare kamar mai shirin iskokai.
Cikin station É—in suka shiga, aka yi musu iso wurin DPO, cikin sa'a suka tarar da malam shamsu a station É—in yana ta cigaba da zigar kai su Aliyu CID.
Adam ya ce "Case ɗin ƙanina na zo mu yi magana a kai, na san shi ba mai laifi ba ne"
Malam shamsu ya ce "Ta ina, yana mana iƙirarin kisan kai a cikin unguwa"
Usman ya ce "Wai kai malam shamsu meye yake damunka, meye ribarka idan an rufe Aliyu ne?"
Mai sunan baba ne yayi sallama ya shiga, suka amsa masa ya nemi wuri ya zauna.
Adam bai ko kalleshi ba ya cigaba da magana ya ce "Da ku ka caje Aliyu kun same shi da makami?" DPO ya ce "A'a"
"Good, É—ayan fa, abokin rigimar ta sa"
"Eh, mun kama shi da wuƙaƙe da tabar wiwi"
Suna cikin maganar aka shigo da su Aliyu.
DPO ya kalli rumaisa ya ce"Ni mamakina ma da wai duk a kan wannan Yarinyar ce ta haÉ—a faÉ—an, ke meye ya haÉ—aku?"
Ta cunkusa baki ta ce "Cewa yayi na sayo masa sigari, kuma ni ba ƴar iska ba ce ba da zan taɓa sigari ina ƴa ma ce mai mutunci "
Adam a ransa ya ce "Ko wa ya tambayi jinsinta kuma oho'
Malam shamsu ya kada baki ya ce "Ƴar iska kum ta nawa, zance da ya cika unguwa"
Zabura rumaisa ta yi ta ce "Yaya usy ka ji ko? Yanzu idan na yi magana ace ba na jin magana, da kunnenka ka ji yana ce mini Æ´ar iska, ni fa bar Æ´ar iska ba ce ba, bana wasan banza da maza, meyasa ake ce mini Æ´ar iska?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska.