Sashe 84
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buɗe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin ɗa, ki rasa da wanda zaki haɗa shi, sai auren ƴar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta riƙe shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaɓa zaki aura mata ɗa na, to ba zai yiwu ba wallahi"
Ammi ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan"
"Ni ina na san ana yi, ana ƙulla mini kitimurmura, ina ɗan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ƴar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini"
Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataɓus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaɓa.
"Lubabatu shi É—a na kowa ne, iman kuma Æ´ar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?".
"Ba wani ɗa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ƙallafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi ɗa na yafi ƙarfin auren ƴar tsintuwa, baƙin halinki ne yake bibiyar ki da yaranki".
Tuni rumaisa ta hasala ta ce "Wai jabir ɗin banza Jabir ɗin wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ƙaddara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir ɗin mana, wani sololo kamar an mari ɗan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?".
"Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, Æ´ar matsiyata ban saka da ke ba, sa'arki ce ni?"
Ruma ta ce "Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan ɗan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir'auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da ɗan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ƙullace da ke"
Ammi jikinta har rawa yake, ta ce "Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki" dan ammi ba ta taɓa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau.
Laila ta ƙaraso falo ta ce "Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ƙasar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da ɗan ta mara tarbiyya.
Ƴar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da alƙibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ƙi yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da alƙur'ani, cigaba yanzu muka fara"
Ruma ta ce "Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud"
Laila ta ce "Dan Allah malama kwashi banzayen ƙafafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa".
Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce "Laila har da su kaza a cin danƙo, ni ƴar riƙo za ta gayawa magana haka".
"Ƙwarai ƴar riƙo ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa'a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan ɗuɗɗura miki, zaki iya fita"
Su biyun duk suka ƙureta da ido, ba wanda ya fi ɓata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata.
"Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faÉ—a ba zan bari É—a na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba É—aya biyu, Æ´ar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya" ta fice tana huci.
Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce "Laila mey....."
"A'a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir ɗin nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ƙaunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka ɓare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke ɗauke da ita".
Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman sha'awar auren jabir, amma halin mahaifiyarsa ne sai a hankali, kuma wani point da ruma ta kawo abun dubawa ne, mutumin da mahaifinsa yake ƙasar waje yana jinya, an bar shi shikaɗai sai mai kula da shi, tilon ɗan sa namiji kuma yana nan yana gararambarsa.
Sai dai ba a fi mintuna arba'in, da tafiyarta ba, wambai ya kira ammi a waya.
Suka gaisa, gabanta na faÉ—uwa, ko wani abun hajiya Lubabatu ta je ta kitsa masa, sai dai ta ji ya ce mata "Mun yi magana da jabir galadima, idan turaki ya dawo, zuwa ranar lahadi idan Allah ya kai rai, zamu kai kuÉ—in auren yarinyar wurinki iman wurinsa, ya ce mini kun gama magana, zamu sanya watanni biyu ne kawai auren"
Gaba É—aya sai ta ji ya É—aureta ta da jijiyoyin jikinta, ammi ta ce "To ranka ya daÉ—e, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Laila ta ce "Lallai ma jabir munafuki ne, yana sane da uwarsa ba ta so, amma yake maganar kai kuÉ—i? Kodayake hakan shine dai-dai, ta auri jabir É—in, mu ga ta tsiya, Allah ya tabbatar da alkhairi, ai Allah ya fi su"
Ammi ta ce "Subhanallah, Allah ya kawo mini ƙarshen wannan fitintinu, ni abubuwan ma sun isheni, Addu'a dai nake tayi, Allah ya shiga lamarin nan, bai kamata a hukunta jabir, da laifin mahaifiyarsa ba, tun da shi mutumin kirki ne".
Ruma ko sunan jabir ba ta son ji, dan haka ta bar falon gaba É—aya, ita zaman gidan duk ya isheta, gida kullum cikin tashin hankali da bala'i, an saka mutum É—aya a gaba da masifa.
Harabar gidan ta fita shan iska, tana ta zazzagawa, tana kallon fulawoyi, ga sanyin la'asar, yanayin yayi mata daÉ—i sosai.
Daga sashin Mummy ta hango jamil, ta tsaya tana kallon sa, su kullum suna gidan nan, kodayake ba abun mamaki bane ba, tun da Æ´an uwa ne, amma ita a wurinta duk wanda ya fiye zuwa wurin Mummy ba shi da gaskiya.
Ga mamakinta taga yana tunkarota, dan haka ta haÉ—e rai zata juya ta tafi, ya cimmata da sauri ya ce "ÆŠan tsaya mana, yau Allah ya sa mun haÉ—u, magana zamu yi"
Ta ƙare masa kallo ta ce "Maganar me?"
"Magana a kan abun da ki ka cewa mjinki na kina zargina da kisan Aisha"
Ruma ta ce "Ba rami meya kawo rami,? Ni ban ce ka kashe anty aisha ba, kuma da mijina ku ke magana ba ni ba, dan haka babu ruwanka da ni"
"Amma ko menene ke ki ka kitsa misa, daga auroki Æ´ar mitsitsiya da ke, kin rikita mana zaman lafiya family"
"Dama can ba zaman Allah da annabi ku ke yi ba, kuma na faɗa ɗin, idan kana da gaskiya, maiyasa a da baku damu da anty aisha ba, sai yanzu kake damun baban sabir, wataƙila ma da kai ake haɗa baki ake ɓata masa suna"
Jamil ya ce "Kin san me ki ke faÉ—a kuwa?"
"Malam danginmu babu mahaukaci, ban yi gadonsa ba, kuma babu Æ´an shaye-shaye"
Jamil ya ce "Ni fa jami'in tsaro ne, zan iya amfani da kakina wurin ladabtar da ke, da tursasaki a kan kiyi bayanin abun da ki ke ɓoyewa".
"To meya hanaka yin hakan tuntuni? Ka yi mana, amma ka sani na san da batun saka sunan anty aisha, a matsayin magajiya da mai girma turaki ya yi, a kan filin sa, da wani kamfani da haɗin gwamnatin tarayya suka karɓa jingina, ake amfani da shi, ana bashi wani kaso, na kuɗi, wanda kai tsaye yake shiga asusun anty aisha. Ka ga idan baka kiyayeni ba, zaka tsinci talatarka a laraba"
"Wa..ww..waye ya gaya miki wannan maganar? Kenan adam saboda wannan maganar, ya fara tunanin É—ora zargin sace matarsa a kaina?"
Rumaisa ta ce "Kai ma kenan saboda ka wanke kanka daga zargi, ya sanya ka ƙirƙiri cewa ya kashe matarsa yayi tsafi da gangar jikinta?"
Mamakin rumaisa ne ya mamaye shi, ya ce "Kuma aka ce miki ni ne na yaÉ—a wannan maganar? Me ki ke nufi ne?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "Ba ina nufin kai ne ba, kawai na yi tunanin, kowaye ya saka aka sace anty aisha, shi ne ya yi wa mijina sharri, ni ba ƴar sanda ba ce ba, amma ƴar baiwa ce, garkuwa da aka yi da anty aisha shiri ne, kuma idan ba ka da hannu, kar ka damu kanka, sai dai ita rayuwa, iyawa ce, abu ƙailalan zaka yi, ya jefeka cikin masifa a gaba, har ƙarshen rayuwarka, ka sani iya wuya ina bayan mijina, kuma kar ka sake tunkarata da wannan maganar"
Dafe kai Jamil yayi, ya ja da baya,gaba ɗaya ya ma rasa ta ina zai fassara maganganun rumaisa ne? Ta hargitsa masa zance cikin zance wace irin yarinya ce ne haka? Kamar ana controlling ɗin ƙwaƙwalwarta da remote?.