Sashe 91
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Iman kiyi haƙuri, a baya nayi ƙoƙarin goyon bayan uncle J, duk da ba kya son sa, sai daga baya na fuskanci lallai, akwai ƙalubale idan ki ka aure shi, na yadda da maganar rumaisa, wanda bai tausayawa mahaifinsa ba, yaushe zai tausaya miki. Kin san kodayaushe ni mai sonki ce, ban so ki da jabir, dan muzguna miki ba my Iman"
Iman ta tura baki ta ce "Gaskiya i feel bad, na ga kamar yayata ta daina so na, ba ta son abun da nake so"
Nusaiba ta dafata ta ce "Haba my iman, ke kin san ban da kamar ki, kawai dai wanda ki ke so ɗin ne, nake ganin kamar baku dace ba, ya fiye tsauri da jin kai. Kuma bana son mutane su yi miki dariya, ace duk wannan gwagwarmayar baki auri mutum na mussaman da zaki samu kwanciyar hankali ba, ba dan ina ƙyamar sa ba, amma kin san zaku fuskanci ƙalubale"
"Anty Nusaiba ba yadda ki ke tsammani bane, mutumin kirki ne, ba wulaƙanci ne da shi ba, miskili ne, ba jin kai ne da shi ba, kama mutunci ne da rashin son raini, amma mutum ne mai tausayi sosai. A yanzu ba dukiya nake nema ba anty nusaiba, kwanciyar hankali da soyayya.ki yi mini Addu'a, idan shi ne allhairina, Allah ya tabattar mini, amma kar ki gayawa ammi tukuna, sai yazo yau na ji me zai ce mini"
"Kar ki damu, ina yi miki fatan alkhairi ko yaushe ƙanwata".
"Na gode yayata ta kaina" Nusaiba ta yi murmushi ta fice daga kitchen É—in.
Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daÉ—i, sai dai an rasa wanda zai yi magana, kasancewar shi wannan ne zuwansa na farko zance, ita kuma yayi mata kwarjinin da ya saba, ko É—aga kai ta kasa, sai kallon wuri É—aya kamar mara gaskiya.
"Ki yi tayi mini surutu a waya, har na rasa abun cewa, amma yanzu kin sakani a gaba kina sunkuyar da kai, kamar kinga dodo, daga gaisawa kin yi shiru".
Muryar nan ba ƙaramin narka mata zuciya take yi ba, murmushi ta kuma yi ta sunkuyar da kai.
"Shikenan, Khadija ɗago in gaya miki dalilin zuwana wurinki" da ƙyar ta ɗan ɗaga kai.
"Kallona zaki yi, bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ƙanwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taɓa gwadawa ba ma.
Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?"
'Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji' ta tambayi kanta.
"Ba kya son talaka ko?'
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Talk"
"A'a yaya umar" tayi maganar muryarta na rawa.
Umar ya É—an tsura mata ido ya ce "Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faÉ—a, ba ta ji ne, but am good person ko?"
Ta ce "Yes you are".
"Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu"
Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daɗe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi baƙin tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba.
Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ƙamshin turaren mai sunan baba take ji.
Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku.
Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama.
Suna zaune a falon, suna kallo, suna taɓa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye baƙonta ya kuma suka yi da shi?.
Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama.
Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ƙarasa gaban iman, ya bata envelope ya ce "Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki"
Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar É—in yake nufi ba.
Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce "Wanda ya zo wurinki É—azu" sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope É—in.
Laila ta ce "Iman, sai ɓoye-ɓoye ki ke yi, yakamata ayi mana ƙarin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki" tayi maganar cikin wasa.
Mahmud ya kalli Ammi ya ce "Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?"
Jiki na rawa ammi ta ce "Ni, eh mana Mahmud mai ze hana".
"Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?" Rumaisa ta faÉ—a lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi.
Bai ce komai ba ya É—an murmusa, ruma ta ce "Waye ya kawo mana lemo?"
Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce "ko ciki zamu shiga ne?"
Ya ce "To"
Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin É—aci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru.
A ɓangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ƙwace mata shi, ta ƙarfin tsiya.
A bedroom ɗin ta suka tsaya, ta ƙarasa ta saka hannunta, tana sake kaɗe masa makeken gadonta, da yake a ɗame da bedsheet fes da shi ta ce "Bismillah zo ka zauna"
Ya nemi wuri ya zauna a ƙasan carfet, ya ce "ki zauna, ni nan ya isa"
"To nima bari na zauna a nan ɗin, ai ba wani abu" ta zauna a ƙasa kusa da shi.
Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, farincikin ta ya kasa ɓuya, sai ƙoƙarin mayar da hawaye take yi.
Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce "Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma É—an mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman É—in zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaÉ—an ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo".
Ammi ta ce "In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wulaƙanta mini ita ba, ba damuwa, zan iya ɗaukar ɗawainiyar komai ni nayi masa".
"Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ƙoƙarin sa a kan kula da ita."
"Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haÉ—a mana kanku gaba É—aya Æ´aÆ´an galadima".
"Amin ammi na gode" ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshsheƙar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye.
Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi.
Ruma ta ce "Ammi, me yayi miki me ya ce miki? Æata miki rai yayi?"
Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta riƙe hannun ruma ta ce "Bayan tsawon shekaru, da fidda ran ɗa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, ɗa na ya kusa dawowa gareni, duk ƙoƙarin ki ne rumaisa na gode"
Rumaisa kasa riƙe hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce "Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi"
Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu'a, da ita da iyayenta.
"Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke Æ´a ta".
Laila ta ce "To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani".
Nusaiba ta ce "Muna zaune ta yi mana wayo, ta ƙwace mana ammi ba".
Bisa kasada umar yayi proposing É—in Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji.
Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan.
Ta ɗan numfasa ta ce "Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da baƙonta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa"
Laila ta ce "Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai"
Ammi ta É—an waro ido ta ce "Mai sunan baba wai?"
"Eh ina ga shi ne"
Ammi ta ce "Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara'a baya son mutane, mamansa na yawan faÉ—ar zafin ransa".
Laila ta ce "Ammi ki yi musu addu'a kawai, ke ba ga É—anki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin "