← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 124

Sashe 108

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke rabu da ni, nima aure nake so rumaisa, ke kin yi aure, mai sunan baba yayi, Aliyu da yaya Habu suna hanya, jiya dan abun takaici, rige-rigen katifar mai sunan baba muka din ga yi, da tsofaffin kayansa. Kin ga yadda yake wani basarwa yau da muka je, wai shi maigida. Ke ma kina ta ƙarshe a gidanmu, amma ƙiri-ƙiri daga sunanki rumaisa an mayar da ke mimi, saboda aure, kallemu ni da Abdallah aka bawa kwanukan abinci muka kai musu. Allah ka aurar da ni, ko babyn nan a din ga ce mini"

Rumaisa dariya har da tuntsurawa, "Zaki yi dariya ne, wato ke kin tsallake, mijinki na ta lallaɓa ki, zuwa zan yi mu dai-daita da Hauwwaliya, daga baya mu yi kuɗi a tare, dama mutuniya ta ce, tun da yanzu mata sun fi son mai kuɗi muyi tuwona maina, kar na je na lalace"

Shi har ga Allah yake maganar, takawa da yake jin su ya ce "Usman idan ka lalace ina muka kama? ka samo mata, in dai aure ne zan yi maka na baka jari"

Usman ya ce "Subhanallah, Allah ya taimake ka dan Allah ka ce ba ka ji abun da na ke cewa ba, har kunya ta kama ni".

Suka yi tayi masa dariya.

***
Baƙi suka fara watsewa, saboda an kammala biki.

Gidan Iman ma mutane suka yi ta sintirin zuwa gidan ta, mai sunan baba yayi burus da ita, har ta É—an sake daga tsoronsa da take ji.

Yau kiran sallar farko na asuba, ya tashi yayi nafilfilinsa da karatun Alkur'ani, ana daf da fara kiran sallar asuba, ya tashi da niyyar tashin Iman ta yi alwala.

Sai dai zancen ya canza, maimakon first night shi first asuba yayi, ƙarshe sai da hasken rana ya hudo, sannan sallar asubar nan ta yiwu.

Mai sunan baba kenan, komai nasa daban ne, sai dai kamar wanda ya yi laifi, duk ya diririce, mussaman ganin tana kuka.

Bayan ta idar da sallar asuba, ta kifa kanta a kan sallaya, a hankali ya kira sunanta "Khadija"

"Na'am"

"Ki tashi ki kwanta mana".

"A'a bakomai, ai gari ya waye ma"

"A'a ki kwanta dai ki huta, kina buƙatar wani abun ne?".

Ta ce "A'a"

"To tashi ki kwanta"

Ya É—agata ya rakata kan gadon ta kwanta.

Har zai tafi ya ce "A cewa Nusaiba ta zo tayi aikin nata, ta kawo ruwan zafin duk da ma dai na yi da kaina".

Rufe fuska kawai ta yi ta, lumshe idonta tana murmushi.

Ƙiri-ƙiri mama ta kira mai sunan baba, ta ce masa maƙwabta za su zo, amma ya ce kar su zo, ba ta jin daɗi.

Abun da Iman tayi tsammanni, da kuma wanda mutane suke jiye mata, ba shi ta tarar a gidan mai sunan baba ba, mutum ne matuƙar kulawa.

Aikace-aikacen gidan kuwa ba ruwansa, tashi yake yayi abun sa, da ta motsa sai ya ce ta zauna ta huta, shi tausayin ta yake ji.

Ranar da zai koma kasuwa kuwa, shagwaɓa iri-iri a wurin Iman, kamar kar su rabu.

***

Ihun da rumaisa take yi ne tana salati, ya sanya takawa fitowa daga toilet a hargitse, ya nufota.

"Menene lafiya?"

Ya tarar da ita bacci take yi, tana ta fizge-fizge tana son ta tashi, ta É—aga murya tana "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin".

Da sauri ya ɗagata ya din ga karanta mata adduoi, yana tofa mata, ko da ta buɗe ido ta ganshi, ta saka ihu ta ƙwace tana haki.

"Mimi lafiya kuwa? Menene?"

"Ba kaine ka zo idonka na hayaƙi ba, zaka huda mini cikina da faratanka ba".

Gabansa ne ya faÉ—i ya ce "Ni kuma mimi?".

Eh mana tayi maganar hawaye sharkaf fuskarta.

Jiki a sanyaye ya ce "Mafarki fa ki ka yi, ni ina banÉ—aki".

"Da gaske mafarki ne, ba ka fasa mink cikin ba?"

"Duba ki gani".

Ta shafa cikin ta ta ce "Ni fa tun ina gida nake mafarkin idonka na ci da wuta, zaka soka mini farce a wuy, har a gaske fa watarn idonka yana yin hayaƙi"

Ya É—an yi jimm sannan ya ce "Ki yi addu'a ki cigaba da baccinki mafarki ne"

Ta ce "Ba zan iya ba tsoro nake ji"

Ya rungumeta ya ce "Ki yi ta Addu'a"

Yayi shiru yana tunanin kenan rumaisa ciki ne da ita? In dai Aisha tayi irin wannan mafarkin, to ɓari take yi, amma rumaisa ta ce masa tun a gida take irin mafarkin.

Wata guda da auren su Iman.
Mai sunan baba bai taɓa zaton zai iya zagewa ya yi soyayya haka ba, babban abun da yake ƙara masa son Iman bai wuce matuƙar biyayyarta ba, da soyayyar da take yi wa mama, da ƴan uwansa ba, dan haka yake ƙara iya ƙoƙarin sa wurin ganin ya kyautata mata.
Tuni ta cigaba da zuwa makarantar ta, wasu lokutan kan ta dawo ya zo gida ya rage mata aiki, ranar kuwa da zata kai shida a makaranta, har makarantar yake zuwa kai mata abinci babu ruwansa.

Ƙawayenta suna yawan faɗa mata, tayi dacen miji mai son ta. Idan za ta tafi makaranta idan ba zai samu kai ta ba, shi ne yake bata kuɗin mota.

Tana zaune a falo da daddare tana shige -shigenta a system ɗin sa, tana typing ɗin wani assignment, ya fito daga bedroom ya kwanta a kan kujerar da yake, ya ɗora ƙafafuwansa a kan cinyarta ya ce "Me ki ke nema a computer ta?"

Ta shagwaɓe ta ce "Dubawa nake ko zan ga hoton ƴan mata"

Dariya yayi ya ce "Ni ina ruwana da wasu ƴan mata, ke ma dan kin liƙe ne ki ka same ni"

"Ko kuma mun liƙe ba" tayi maganar tana tura baki.

Tashi yayi zaune ya rungumota jikinsa ya ce "Na yadda ni na liƙe, tun a kallon farko da na ganki, na zata ma da aljana ce za ta aure ni, ashe ƴar autar ammi ce"

Tayi dariya ta ce "Ni fa da tsoro ka ke bani my, i just felt for you, ashe duk fasa aurena da ake a baya rabonka ce ni, Alhamdilillah for having a good husband like you my faruk" tayi maganar tana shafa sajensa

Murmushi yayi yana jin wata annashuwa, da soyayyarta na ratsa shi, ya sake rungumeta ya ce "Deejana, my pretty yellow girl, gaskiya kina so na da yawa".

"To ka ce kana so na nima"

Wata Æ´ar dariya ta bashi, ya ce "ÆŠaukko carbi, ina faÉ—a kina lissafawa, har sai kin ji kin gamsu da ina son ki"

Iman ta sake narke masa ta ce "Ni waƙar soyayya ma zaka yi mini"

"Taɓɗijan, ai muryata ba ta waƙa ba ce, ban ma iya ba deeja"

"Muryar ka ta tsorata mutane ce" tayi maganar tana yi masa dariya.

"Eh ai an fi son haka, monster haka ba raini, tashi mu je mu kwanta, zaki school gobe in Allah ya kaimu"

Ta ce "To, bari na kashe system É—in"

"Ahh, Baby an yi maka Gmail"

Mai sunan baba ya ce "Ba zaki daina babyn nan ba ko? Baby kamar É—an daudu, gara ki ce mini faruk É—in ai".

"Ai a waje ne ake maka kallon monster, ni a wurina babyna ne"

"DaÉ—inta ke ma a da monster ki ke gani ai".

"Eh yanzu kuma baby ba" tayi maganar tana duba Gmail É—in.

Message ne a kan ana nemansa a Lagos zai je interview.

Ya ce "Anya wannan message É—in nawa ne? Bana tunanin nawa ne"

"To na waye, naka ne mana"

Zai yi magana sai ga message É—in Mahmud.

"An kiramu interview lagos, ban sani ba ko ka ga message É—in, ranar Sunday zamu tafi, za ayi interview Monday, mun samu aikin nan"

Nunawa Iman yayi yana cigaba da mamakin abun, tamkar dai mafarki.

Iman ta din ga murna, tana addu'a, tamkar tun farko ba ta san zancen ba.

***
Duk da haryanzu bai gama komawa cikin nutsuwarsa gaba ɗaya ba, amma yayi ƙiba sosai abun sa, da gani ya samu nutsuwa sosai yanzu.

Sallama da aka yi a office É—in ce ta sanya ya É—ago, ya amsa sallamar.

Jamil ne ya shigo fuskar nan babu annuri, shi ma Adam ya haɗe fuska yana jiran ya ƙaraso.

"Wurinka na zo"

"Ina saurarenka"

"Zuwa na yi na ji ina ka tsaya"

"Ina tsaye a in da ka sanni"

Jamil ya ce "Magana nake so mu yi ta fahimta, zuwa yanzu yakamata ace ka kammala binciken da zaka yi, ka wanke ni daga zargi da kuma zullumin da ka jefa ni a ciki kai da matarka".

"Jamil a kan me zaka yi zullumi, idan har ka na da gaskiya? Ka cigaba da harkokin ka kawai"

"Ba zai yiwu ba Adam, ya zama dole ku wanke ni, kuma ku tabattarwa duniya, bani da laifi".

"Jamil kana bani mamaki fa, ni da na dawo ban tayar maka da hankali na cigaab da bibiyar matata a kan lallai ka samu wasu bayanai ba, sai yanzu zaka zo ka cigaba da titsiyeni?"

"Dole in titsiyeka Adam, tun kan ayi mini wani sharrin, ka je ka ce mata akwai filin mai girma turaki, da ya sanya sunan aisha a matsayin magajiyarsa, ta na nema ta fara yi mini barazana da haka, ta sake ƙulla mini sharri"

"Duk da ba ka cigaba da bibiyarta ba, she won't go this far, amma duk abun da rumaia ta sanya a gaba, akwai ƙamshin gaskiya a cikin sa, dan haka ka fitar mini daga office"

"Adam ni ka ke kora daga office É—in ka?"

"Na kore ka ɗin, a duniya ban taɓa tsammanin kai da Jabir zaku yi mini abun da ku ka yi mini ba, dan haka ka fitar mini daga office ".

Ringing É—in wayarsa ya dakatar da shi da cigaba da magana, ganin kira daga makarantar su rumaisa, ya É—aga kiran yayi sallama.

Shugabar makarantar su ta ce masa sun kai rumaisa asibiti tana ciwon ciki.

Bai sake bi ta kan Jamil ba, ya fice daga office É—in.

Mai sunan baba kuwa har gari ya waye, yana doubting idan maganar nan gaskiya ce, sai da ya je gida ya samu Mahmud, Mahmud ya tabattar masa da hakan.
Chapter 108 · 0% Book details