← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 124

Sashe 112

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi ajiyar zuciya ta sake cewa "Papa, jaridar da suke wallafa ci maka mutunci, lokacin da anty aisha ta rasu, Yasir ya bi diddigin gidan jaridar, daddyna ya gano wakili ne suke ɗaukar nauyinsa, dan ya ce mini sun taɓa kiransa har aka nemi ya bayar da haɗin kan cutar da kai, ya ce ba ruwansa. Kaga dole a cikin family ba za a rasa wanda suka haɗa kai da shi ba, ake cutar da kai"

Ya lumshe idanunsa ya ce "Mimi kaina ya daina É—aukar wannan abubuwan ma, bari na samu nutsuwa"

"Idan ka samu nutsuwar, ka yi bincike sosai a cikin gida. Sannan ka sani tun a yanzu ka sanya wa ranka cewar, zaka iya gano su waye, amma samun hukunci da adalci sai a wurin Allah, amma ba a wannan ƙasar ba"

Ya numfasa ya ce "Ina sauraren Bashir ne, na ji me za su ce mini, nayi magana da su barrister ma, waÉ—an da ki ka ce mini kin yarda da su, muna kan faÉ—aÉ—a bincike"

"Nima ni da ƴan team ɗina muna ta ƙoƙari, Allah ya yi mana jagora" ya jinjina kai ba tare da iya yin magana ba.

Abu kamar wasa mai sunan baba yake ta ƙoƙari akan kayan Alhaji Aminu ɗan fulani, kuma kasancewar an samu sauye-sauye a wurin, cikin ikon Allah komai ya zo masa da sauƙi, dan ana daf da releasing ɗin kayan.

Alhaji Aminu yana yawan kiran sa, su gaisa, shi kuma mai sunan baba, sai ya tambaye shi ina Ade, ya ce masa tana nan tana rigima.

Alhaji Aminu ya matsawa mai sunan baba, a kan lallai ya zo gidansa su gaisa, dan yana bawa Ade labarin sa, ita kuma ta ce tana son ganin sa.

Mai sunan baba ya ji a ransa yana son sanin ahalin Alhaji Aminu, ko zai samu abun da yake son tabattarwa, ko Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman.

***
Tamkar za su kacame da dambe, haka suke musayar yawu, tamkar ba aminan da suka kwashi shekaru suna cin mushe ba, tamkar ba tare suke ƙullawa da kitsa duk wani hatsabibanci ba.

Mummy tamkar za ta ari baki, saboda haƙilo da bala'i.

Hajiya Lubabatu a fusace ta kira Jabir a waya, a kan lallai ya zo tana son ganinsa, ta ajiye wayar ta kalli hajiya jamila ta ce "Kar ki sake kiran É—a na da mazinaci É—an iska, idan ma hakan ne, sai ki ce mazinata Æ´an iska".

"Na faÉ—a É—in, koda yake barewa ba ta gudu É—an ta yayi rarrafe ba, tun da sai da ki ka yi yawon tazubar ki ka gama ki ka tuba aka yi auren. Kin yi wa mijinki asiri, kin ya da shi a Germany, kin cigaba da watsewa a gefe, ke ki yi É—an ki yayi".

"Jamila kina nufin ni ce nake biye² ni zaki yi wa sharri? Ko kin manta kema irin abubuwan da ki ka shuka, yayan giwa da ki ka din ga sadaukarwa, da ƴaƴan Adam, ai ni ban kai ga aikata kisan kai kamar ke ba"

Jabir ne yayi sallama, suka yi shiru suka waiwaya.

"Sannu munafukin Allah ta'ala"

Jabir ya ce "Mummy lafiya kuwa?"

Mummy ta ce "Saboda kai watsatstse ne, mara mutunci, na amince maka na amincewa uwarka, amma ku ka zalince ni, wace irin alaƙa ce tsakanin da ruƙayya har ka ke iƙirarin yaɗa hotunanta?"

Yayi shiru yana kallon Mummy.

"Wallahi lubabatu sai kun yi dana sanin abun da ku ka aikata mini, kai ba da ni ka ke zancen, dabba É—an akuya".

"Kar ki sake kiransa ɗan akuya, ruƙayya ce babbar akuyar da ba ta san ciwon kanta ba"

Mummy kawai ta fice, zuciyarta na wani irin zafi, kuka take son yi amma ba ta son bayyana karayarta a fili.

***
Mai sunan baba ya amsawa Alhaji Aminu cewar zai kai masa ziyara ya gaida Ade, sai dai yana fargabar kar ya ga abun da bai yi tsammanni ba, zai fi kowa farin ciki, idan aka ce a sanadinsa Iman ta samu ko wani ne a danginta, duk da rashin hakan ba ya nufin zai juya mata baya ne.

Kiran Iman yake yi yana zancen zuci, ta É—aga video call É—in ta ce "Hi dear"

"My yellow, how are you?"

"Fine Alhamdilillah, ya aiki?"

"Ai akwai shi, yanzu salary ya shigo, na ce let me call the person close to my heart"

Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, mun godewa Allah" kallonta yake sake yi, hatta yanayin gashin girar iman, irin na Alhaji Aminu ne.

"Ya naga kana kallona ne, na canza ne?"

"Bakomai, yanzu ya za ayi da salaryn nan ne?"

Iman ta ce "Ai zaka shigo kano ko? Ka ce fa ƙarshen wata zaka zo".

Ya ce "Eh, ranar Alhamis zan shigo"

Ta ce "To Allah ya kaimu, idan ka zo sai ayi shawara, ka turawa mama dubu É—ari a sai mata abun da take so kan ka zo na neman albarka".

Ya ce "To Æ´ar mama, za ayi in sha Allah, zan cigaba da waya, zamu yi magana anjima"

Ya ajiye wayar yayi shiru, yana cigaba da fatan Allah ya sa Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman.

Har gida Alhaji Aminu ya aika da direba, aka ɗaukko mai sunan baba, yana da matuƙar karamci da son mutane, kamar ya goya mai sunan baba da ya ganshi a gidansa.
Aljannar duniya, an kashe dukiya an zuba kayan alatu a gidan nan, kamar ba za a mutu ba, karen da yake gadin gidan kuwa bayan mai gadi, shi kansa ba na Nigeria bane ba.
Ga iyayen motoci a parking space.

Ya ce wa mai sunan baba "Mu je ka fara ganin Ade, ka gaya mata ta haƙura da tafiya ƙauye ko Allah ya sa ta yarda".

Tsohuwa ce, a ƙalla zata shekara tamanin da biyar, tana zaune a ƙasan carfet, tana shan fura, sai mita take da fulatanci ita da jikokinta.

Ta ɗaga kai ta ƙure mai sunan baba da ido, har ya ƙarasa gabanta ya zauna.

"Ade, ga wanda yake ta yi mini ƙoƙari a kan kayana, shi ya ce a baki haƙuri, dan Allah kar ki koma ƙauye".

"Au jibo gulmata ka ke yi kana yamaɗiɗi da ni kenan, yaro na bar shanu da dabbobina a ƙauye, an zo nan ƙwam an ajiyeni, sanyi na neman yi mini illa, ga wannan yaran da suka addabe ni, ai zaman ƙauye yafi daɗi".

Mai sunan baba ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba, wannan matar na da alaƙa da matarsa, duk da tsufanta, tsananin kammaninta da iman ba su ɓuya ba, sai a yanzu ma ya ga Iman ba kama take da Alhaji Aminu ba.

Ade ba ruwanta, ta din ga zuba tana bashi labarin yadda take son shanunta, tun da a cikinsu aka haifeta.
Kayan marmarin da ya zo da su, ya din ga ɗauka yana ɓarewa yana bata, tana karɓa tana ci.

Ta ce "Kaga yadda ka ke yi mini ɗin nan, shi ba ya yi mini, kullum cikin rubutu yake da lissafin kuɗi, Euro ya leƙo mun gaisa, sai ya kama hanya ya tafi yawonsa"

Alhaji Aminu ya ce "Sai ka ce a ƙauyen hakan suke yi miki"

"Eh amma dai idan na ga nagge, zuciyana na sanyi sosai"

"Yallaɓai kai baka da ƴan uwana ne?"

Alhaji Aminu ya ce "Kowa ya kama gabansa, ka san ainihi daman mu fulanin tashi ne. To ƴan uwan nawa galibi wasu suna wasu garuruwan, wasu ma wasu ƙasashen. Ni ne ɗan autan ta, ƙauyen fa a gidan wani ƙaninta take, wai an rabata da ɗan uwanta, kamar ɗan uwanta ya fimu"

"Ya fika mana, shi yana zama mu yi hira, kai sai shegen son kuÉ—in tsiya".

"Ni zaki tozarta a gaban baƙo ko, saboda ya baki ayaba, da lemo, to yasin a daina yin ƙosai a gidan nan, tun da ba kya so na"

Alhaji Aminu kamar kakarsa ya ɗauki Ade, su yi ta faɗa wasu lokutan, saboda shi ne ƙaramin ɗan ta.

Mai sunan baba ya ɗan jima a gidan, sannan baba ya ce zai tafi, Ade ta din ga tambayarsa yaushe zai dawo, idan bai dawo ba, za ta ƙulle takalmanta a zaninta, ko ta katanga ta bi, ta gudu ta koma ƙauye.

Mai sunan baba ya ce "Ai ba za ayi haka ba"

"Ka rabu da ita, karen nan zan kawo É—akinta na É—aure, na ga ta wurin fita"

Ta galla masa harara ta ce "Tashi ke je É—akina, ka samo masa É—an biskit É—in nan"

Alhaji Aminu ya ce "Biskit kuma? Ade kyautar nagge zaki bashi, me zai yi da wani biskit"

Mai sunan baba ya ga ƙoƙarin ta ma, rikicin taufan na ta ba na zage² bane ba.

Mai sunan baba har ya koma gidan da yake, yana al'ajabi, kuma ya yanke shawarar zai yi wa Mahmud zancen, koma ya zo lagos ɗin, ya je su ganewa idonsu, su san ta in da za a ɓullowa lamarin.

Dan baya son yayi gaggawa, a zo a gane cewar ba su da wata alaƙa.

***
Ammi ta kasa mantawa da matsananciyar cin amanar da babu uwani ta yi mata, har ta kai ba ta iya sakin jiki tayi magana a gaban kowa yanzu, saboda tsoro da tunanin kowa ma ba son ta yake yi tsakani da Allah ba.

Ranar da mai sunan baba zai koma, Iman gyara kala-kala, aka ƙalƙale ko ina, ta shirya girke² ta sha kwalliya.

Dama har kirari yake yi mata da É—awisu sarkin ado, Iman akwai ado da kwalliya.

Sosai suka yi missing É—in juna ita da shi, sai dai da ya kalleta, Alhaji Aminu yake tunawa da mahaifiyar sa.

Ya din ga jin tamkar yayi mata zancen, amma ya kasa.

Washegarin dawowarsa, da yamma ya shirya su ka yi wa mama siyayya, suka je gida gaisheta.

Mama tayi ta yi masa faÉ—a a kan yanzu yana da iyali, yakamata ya mayar da hankali a kan gidansa, Æ´an samarinta sun É—auke mata komai, kuma dubu É—arin ma da ya turo tayi yawa, jiransa take yi ya dawo dama.

Ya ce "Ni fa ba ruwana, Æ´ar ki ce ta ce ayi haka"

Mama ta ce "Kuma sai ka biye mata?"
Chapter 112 · 0% Book details