← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 124

Sashe 64

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta din ga yaÉ—a cewar, Bintu ce take bawa bokaye Æ´aÆ´anta su cinye, shi ne wannan karon ta haÉ—a da tata Æ´ar, tun da dama Æ´ar gidan malaman tsubbu ce.

Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ƙaunar ɗan sa takawa ba, sannan ya na ɗaukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai ɗau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata ɗan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba.
Iyayen ammi suka yi ta bata haƙuri, da nuna mata dama aure, sai an yi haƙuri ibada ne, ta yi haƙuri da ɗan nan Allah ya bata wani.

A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karɓi abun sa, al'umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naɗa sarki a 'yaƴan sa, sai aka naɗa ƙanin sa.
Hakan ba ƙaramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taɓu.
Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naɗa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban ɗaki kan ta rasu, shi yana ɗan ƙarami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar ɗan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban ɗaki da marigayi, dan haka shi duk ɗaya ne a wurinsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ƴa macen, bayan sun gana ɓata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba.

Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba.
Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huÉ—u da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su É—aya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haÉ—u kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka.

Baba Uwani ta yi ta bata haƙuri, ta ɗauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faɗa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuɗi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ƙoƙarin ta wurin kyautatawa baba uwani.

Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ƙanwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiɗen da yake yana cewa "Maraba da kai babana, abun ƙaunata kuma magajina, galadima ɗan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai"

Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam ɗin dariya, wani dunƙulallen baƙin ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran ɗan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu.
Tun daga nan ta fara turawa Mahmud aƙidar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba.

Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.', za su koma mahaifarsu.

Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta shaƙu da Ade da ƴan rigar, kamar danginta.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still Æ´a ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so.

A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban ɗaki ta wancan lokacin da ta riƙe shi, ita ma ba ita ta haife shi ba.

A wannan karon, shi ma Sharif ƙarara yake nuna son Adam, saboda soyayyar da yake yi wa mahaifinsa, da yadda mahaifin nasa, ya nuna masa ƙauna.

Jamila kuma ta yi alwashin rusa soyayyar nan, da cigaba da baƙantawa giwa, domin rama abun da ta yi mata, na fara auren Galadima.

Duk yadda ta so raba Mahmud da Adam, ba ta yi nasara yadda take so ba, duk da Mahmud ya fara yadda da abun da take gaya masa, sai dai duk yadda take korar Adam idan ya zo wurin Mahmud ya kasa zuciya.

Tuni Mutanen masarautar, wasu sun fara ɗauka, tare da kiran Adam magajin galadima, har da masu ce masa galadima ƙarami, ko kuma magajin takawa, idan ƴan kan zagi suka yi masa wannan washin, haka galadima zai ta yi musu kyauta.

Hajiya Lubabatu ta samo musu wani hatsabibin boka, malam na kan dutse, suka je wurin sa a kan suna son a nakasta Adam, yadda ba zai moru ba, kuma a saka gaba da ƙiyayya tsakaninsa da Mahmud, yadda wuta da ruwa ba zasu jitu ba, haka suma sannan a saka wa galadima tsanar Adam.

Bokan ya ce "Sai an kai masa Adam, saboda ya san aikin da zai yi a kan sa, sannan a taho masa da jinin Mahmud a sirinji.

Ta koma gida, ta saka galadima a gaba, wai tana son ta je garinsu, za ta tafi da Adam, galadima ya ce bai yarda ba, ta haɗa baki da malaman makarantarsu Adam, ta je ta ɗauke shi a makaranta, aka shaƙa masa wani abu ya suma, suka tafi da shi wurin boka, tare da jinin Mahmud.

Bokan ya zuƙi jinin Adam, ya haɗa da na Mahmud, ya zuba wani abu a ciki, jinin ya rabu biyu ɗaya ya yi baƙi, ɗaya ya yi ja, ya mayar da jinin jikin Adam, ya bata sauran jinin, ya ce ta yi girki da shi, ta bawa Mahmud da galadima su ci, ya raba su.

Ta ce ai ba iya nan take so ba, so take a haÉ—a shi da ciwon, da zai nakasa, nakasa ta har abada, da ba zai yi sarauta ba.

Nan ya yi wani ƙulumboto, ya saka wani abu, ya huda wuyansa, ya zuƙi jinin Adam, ta wuya, ya zuba a wani abu, ya ce "Ramin da na yi a wuyansa, ta nan aljanar za ta din ga shan jininsa duk shekara, sai dai babu wanda zai iya hudat, Sannan zan yi wani abu da sauran jininsa, duk shekara za a din ga samun mahaukacin doki, ayi masa, zan haɗa laya da sunansa, wadda za a kai maƙerar da ta shekara goma, a binne, sannan zan saka wannan aljanar, ta zuba masa jinin mahaukaciyar kura a jikinsa, an nakasta shi, nakasa ta fili da zahiri, iya rayuwarsa wannan aljana za ta cigaba da kula da komai, tun da an bata jininsa, sai dai loka-lokaci, za ta din ga buƙatar wani abun" ya wassafa musu abun da za su bayar, suka bayar sannan suka tafi gida.

Ammi ta kaiwa Adam, yana bacci, wai biyo ta yi ta hanyar makarantar su, ta ga an tashi shi ne ta É—aukko shi yayi bacci a mota.
Ammi ba ta kawo komai ba, ta karɓe shi, ta yi mata godiya, sai dai tun ammi ta na saka ran adam ya tashi, har tsoro ya kamata. Sai dai bayan ya tashi ba baki, sai dai kallo.

Hankalin Ammi ya tashi, ta gaya wa galadima, hankalinsa ya tashi suka tafi asibiti aka ce lafiyarsa ƙalau, ya ce idan zuwa washegari, bai yi magana ba, za a kai shi babban Asibiti, ko ƙasar waje ne a akai  shi, sai da daga haka washegarin, tunanin galadima ya sauya, ya ce wai ta ƙyaleshi shakiyanci ne.

Abu kamar wasa, sai da Adam ya yi wata tara, ba magana, ga wani irin bacci, mara kan gado, ammi ta dage addu'a, ta kai shi gidansu wurin mahaifinta aka dage da roƙon Allah, sannan ya dawo yake magana.

Gaba É—aya galadima ko a jikinsa, ya daina nan-nan da shi, sai dai abun ka da É—a da uba, soyayyar ba ta dishe duka ba, wataran idan ya gan shi ya na jin daÉ—i.

A lokacin Mummy ta haifi Fauziyya, mutane ana ta shigowa, Ammi da laila da adam, sun je ganin jaririya, Adam na ganin Mahmud, ya nufi wurin sa yana kiran sunansa.

Sai dai Mahmud ya hankaɗe Adam, sai da ya faɗi ƙasa, ai yana tasowa, sai idanunsa suka koma kamar na mahaukaciyar kura, yana wani irin gurnani, ya shaƙe Mahmud.
Ammi hankalinta ya tashi, duk wanda ya je raba su, sai Adam ya cije shi, kowa ya yaƙushe shi, sai jini ya fita.

Da ƙyar Ammi ta riƙe shi ta na yi masa addu'a, ta ja shi ta tafi da shi sashinta, tana kuka ita da laila, tana tunanin menene ya samu adam?.

Sai dai haka ya wuni yana wannan gurnanin, kamar kare.

Mummy kuwa bala'i ta din ga yi, wai za a kashe mata É—a, dama adam É—in maye ne, ya tsotsa a wurin uwarsa, ko kuma a garin yawon bin bokaye, É—an ta ya haukace.
Magana ta din ga yawo a fada, galadima ya je har sashin Ammi, ya din ga yi mata faɗa, wai ita ta sangarta Adam, har yake yinƙurin kashe ɗan uwansa.

Halin da ya tarar da Adam É—in sam bai dame shi ba.

Tun daga nan, idan faÉ—a ya haÉ—a Adam da yara, sai ya burkice, ya na gurnani, da cizo, idan kuma yayi cizo sai jini ya fita, wanda wannan jinin aljanar take sha.

Wani lokacin idan ana ziga wutar maƙerar nan, haka yake jin ta a cikin jikinsa, yayi ta ihu ya na fuzgar fatarsa, ko kuma idan mahaukacin dokin nan, yana dara, sai ya ji tamkar ƙashin sa ake takawa.

Idan kuwa shakara ta yi, lokacin shan jinin nan ya yi, ya din ga suma kenan, har ammi ta fitar da rai da shi.
Chapter 64 · 0% Book details