Sashe 7
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk a falon sashen ammi ya tarar da su, har ammin, ana koyawa Sabir zama an shiryashi cikin wasu kaya masu kyau, an zaunar da shi a gefen kujera, cikin dabara iman tana taje masa sumar kansa, sai kai hannu yake yana turewa alamar ba ya so.
Adam ya fara gaida ammi, sannan ya É—au sabir ya zauna da shi a jikinsa.
Adam ya karɓi brush ɗin hannun iman, ya cigaba da taje masa kai, amma ya cigaba da kai hannu yana turewa yana son yin kuka.
"Kai rigimamme, baka son gayu?" Adam yayi maganar yana murmushi tare da kallon ɗan nasa cike da ƙauna.
Sabir yayi shiru yana kallonsa.
"Yi mini dariya mana, an ce kana dariya amma ba ka taɓa yi mini ba"
Ammi ta ce "Kai ai wannan ɗan naka kai ya yo, babarsa kawai yake washewa baki gaba ɗaya yayi mata dariya, har mamakin irin soyayyar da ke tsakaninsa da ita nake yi, da ya ganta har wani ƙara nutsuwa yake yi".
A ransa ya ce 'Aikuwa ba zan ba ta riƙonsa ba, ya tashi a sangarce da rashin kunya kamarta ba' ya ɗaga kai yana kallon ƙwayar idon sabir, take aisha ta sake faɗo masa a rai, dan suna ɗinar kama da sabir, duk da ya fi kama da shi.
Ammi ta ce "Ina ta magana ka yi shiru, tunanin me ka ke yi ne?" Yana É—ago ido Ammi ta ga hawaye kwance a idonsa.
Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"
Yayi murmushi ya ce "Lafiya lau ammi"
Ammi za ta yi magana, hadimarta ta shigo, ta durƙusa ta ce su Samha ne suke neman iso.
Ammi ta ce, ace su shigo.
Samha ce da ruƙayya, suka shigo tare tana ganin adam sai da ta yi hamdala a zuciyarta, ta wani lumshe ido, wata irin ƙaunarsa da soyayyarsa na sake ratsata.
Suka ƙarasa, suka gaida ammi ta amsa musu cikin fuska, samha ta kalli adam ta ce "Yaya ina kwana?" Ta yi maganar cikin rausaya.
"Lafiya ƙalau, kuna lafiya?"
"Lafiya ƙalau, sabir na zo gani, ammi yaushe za'a kai mana shi ne? Na gaji da jiran na kasa jurewa".
Ammi ta ce "Banda abunki samha, yaron ai haryanzu jariri ne, ba a haÉ—aku da jego ba".
"Haba ammi, tun da muka rasa fulani ai shi ne madadinta"
Ta matsa kusa da adam, za ta ɗau sabir a hannunsa, sai da ta taɓa shi, wani irin kallo take masa ji take kamar ta rungume shi, ko ta samu sassauci a kan abun da take ji game da shi.
Ta ɗauki sabir tana yi masa murmushi, wanda a ƙasan zuciyarta ji take kamar ta buga shi da ƙasa, dan yadda ba ta ƙaunar uwarsa shi ma ba son sa take yi ba.
Miƙa sabir yayi ya hau kuka, duk yadda ta so ta rarrashe shi yaƙi yin shiru, ya cigaba da kuka ba shiri adam ya karɓe ɗan sa, ta ji tamkar ta dunƙule hannu ta daki kan yaron ko ta huce.
Cikin iya siyasa ta ce "Ammi wai har ya iya ƙyuya ne?"
"To gashi dai ya yi miki, É—an na ku ne É—an ganin dama, ko dariyarsa babarsa kawai yake yi wa"
Da sauri samha ta ce "Wace babar ta sa?"
"Rumaisa, yarinyar da ta zo da shi"
Jin an ambaci labarin da Mummy ke son ji ya sanya ruƙayya cewa "Ai ammi haryanzu tana nan?"
"Tana nan mana, ina za ta je?"
"To ammi zuwa take ta ganshi?"
Kan ammin ta bata amsa samha ta ce "Ai an ce mini an kai ta wurin turaki rannan ko?"
Ammi ta ce "Eh"
Ruƙayya ta sake cewa "To ammi gidan nan take zuwa?"
Maimakon ammi ta ba ta amsa sai ta ce "Ruƙayya an ce mini Mahmud ya zo gari ko?"
"Eh ya dawo"
Ammi ta ce "To masha Allah"
Iman ta É—auko baby carrier ta ce "Yaya kawo na saka shi a Carrier ko zai koma barci, na ga yana ta rigima dama yau da wuri ya tashi"
Adam ya ce "Zo ki É—au abunki iman, na fuskanci duk abin da na yi iman sai kin nuna mini ban iya ba, ni ban san a ina ki ka koyi raino ba, tun da mu dai ba jariri ne da mu ba"
Iman ta yi dariya ta ce "Ni na isa?"
"Gashi nan kuwa" yayi maganar cikin sigar wasa. Ya bawa iman sabir ya tashi ya bar falon, a rayuwar duniya samha ba ta kishi da aisha kamar yadda take yi da iman, saboda akwai alaƙa mai kyau a tsakanin takawa da iman, ga iman da kyau tamkar ita ta yi kanta.
Suka gama zamansu, daga bisani suka tashi za su tafi, Samha ta ajiye wata leda cike da kayan sawa da na wasa, wai sabir ta kawowa, ammi ta yi mata godiya sannan suka tafi.
***
Ba kowa a gidansu rumaisa, kowa ya fita da masu makaranta da sauransu, sai mama itakaɗai, kasancewar ta ji sauƙi, ya sanya ta ɗora abincin rana, dan ba ta son su dawo ba ta kammala abinci ba, yanzu ƙaramarsu babbarsu za ta zo ta fara kwanciya da tura baki ita yunwa.
Sai dai babu tsammani ta ga kiran ammi a waya.
Ta É—aga wayar suka gaisa, ammi ta kuna yi wa mama ya jiki.
Sun ɗan taɓa hira sannan ammi ta ce "Yauwwa maman rumaisa wata magana nake son mu tattauna da ke, duk da kamata ya yi na zo ƙafa da ƙafa, ina da wasu baƙi ne da zan yi yau, kuma maganar yakamata mu yi ta"
Mama ta nutsu ta ce "To ina jin ki, Allah ya sa lafiya".
"Yauwwa, zuwa wannan lokaci tun da Allah ya riga ya haɗamu, mun riga mun zama ɗaya, tun bayan da na baro ku, nake ta tunani a kan maganar da ki ka yi mini a kan rumaisa, da kuma wasu dalilai na makomar jaririn nan, shine na yanke shawarar mai zai hana adam ya auri rumaisa, kin ga maganar wata gulma da ɓacin suna ya ƙare, kuma kin ga za ta samu cikakkiyar damar kula da sabir kamar yadda take buƙata, amma me ki ka ce?"
Jiki a sanyaye mama ta ce "Aure kuma rumaisan? Shekararta goma sha uku fa, kina ganin yadda ake fama da ita, ga kuma karatunta".
Ammi ta ce "Maman rumaisa ba zai gagara ba, mu ma duk da ƙuruciyar aka yi mana aure, kuma ba abun da zai samu karatunta, za ta cigaba idan aka yi auren nan ni da adam za a yi wa alfarma kuma ina tabattar miki in Allah ya yarda zai zama alkhairi, yanzu amsarki nake jira, zan kai maganar ga magabatansa, tun kan ace za a bashi wata matar, ban san wa za a bashi ba, ko dan makomar rayuwar marayan nan".
Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, amma gani nake rumaisa ba za ta iya raino ba, ita ma ba hankali ta cika ba"
Ammi ta yi murmushi ta ce "Babu damuwa, ai ba sakar mata rainon za a yi ba, ya zamana dai ta samu kusanci da shi sosai yadda take so".
"To, bari yayyenta su zo mu tattauna, abun da suka yanke shikenan"
Ammi ta ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi, ina saurarenku dan da wuri nake son ayi komai a gama"
"To shikenan, duk yadda muka yi zaki ji ni" tun da suka yi sallama mama ta kashe wayar take zullumi. Ayi wa rumaisa aure ta je ta yi me a gidan auren? Yarinyar da ban da zunzurutun ƙuruciya da wauta ba abun da yake damunta.
A haka mama ta É—ora girkin nan, take aikin jikinta duk a sanyaye.
Rumaisa ce ta yi sallama, ta shigo da jakar makarantarta a ka, tana yamutsa fuska.
Mama ta kalleta ta amsa mata, rumaisa ta jefa jakarta ɗaƙi, ta cire hijjabinta ta kalli mama ta ce "Mama ki aika aje a yi wa mai ice warning ba ruwansa da ni, me na yi masa da idan na zo wucewa zai din ga cewa gata can, sau biyu yana yi mini, kar na yi abun da ba shikenan ba a zo ace na yi tom" tana gama maganar ta ɗau buta ya wuce banɗaki.
Bayan ta fito ta kalli mama a taɓare ta ce "Mama wai ba a gama abincin ba, ni fa yunwa nake ji" mama ta bi ta da kallo tana hango rumaisa da aure.
Ta gama taɓararta mama ta kammala girki, ta ci ta tafi makaranta, sai da yamma da mai sunan baba ya dawo, mama ta yi masa zancen.
Aikuwa ya haɗe rai ya ce "Dama na san ɗawainiyar da suke yi da ita, dole a ƙarshe su nemi wani abu, wane irin aure yaushe aka haifi rumaisan da har za a wani ce a aureta, mutumin da faɗa suke yi ba sa shiri, kawai ki ce musu ba zai yiwu ba su yi haƙuri".
Kasancewar usman yana nan ya ce "A'a fa ayi tunani, yarinyar nan kuna ganin abun da take yi a kan yaron nan, me ake nema a aure ne ba mutum na gari ba, kuma in da za a iya riƙeta ba, idan ta amince kawai ayi musu fatan alkhairi a nawa ganin, mussaman yanzu da ƴan unguwa suke ta ƙananan maganganu a kanta, wataƙila ana yi mata auren ta nutsu"
Wani mugun kallo mai sunan baba yayi masa, dan haka yayi shiru, kuma tun da ya kafe a kan ba ya so, ba zai canza magana ba.
Gaba ɗaya hankalin mama ya rabu biyu, kowannensu yana da gaskiya, ita kanta ba ta shirya rabuwa da rumaisa yanzu ba, dan Allah ya sani rumaisa ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyar aure a yanzu ba, dan a sangarce take, sai dai kuma tana matuƙar jin nauyin ammi ta ce mata ba zata basu auren rumaisa ba.
Ayshercool.
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*