Sashe 13
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi ta kammala shirinta tsaf, ta fito falo, ta yi wa ma'aikatanta sallama, ta fita haraba, tana fita ta hangi Mahmud yana nufar in da motoci suke, ya ƙara ƙiba abun sa, kai da ka ganshi ka san hankalinsa a kwance yake ba shi da wata damuwa.
Ammi ta tsaya tana hangensa, ya ɗan daɗe yana duba abu a wayarsa, daga bisani ya nufi motar da zai hau, ƙarasawa ammi ta yi, zuwa in da direba yake jiranta a tata motar, suka yi ido huɗu da Mahmud, amma sam bai kulata ba, sai ta tsinci kanta da kasa shiga motar.
Mummy ta ƙaraso cikin shiri, da alama fita zasu yi ita da Mahmud, tun kan ta ƙaraso ta ga abun da ya faru, dan haka ta ƙaraso da fara'arta ta kalli ammi ta ce "Ran giwar galadima ya daɗe, fita zaki yi ne?"
Jiki a sanyaye ammi ta ce "Eh".
"Ok, ya Mahmud ƙarami, yakamata ko sau ɗaya a kawo mini shi sashina, ba dan halina ba".
Ammi ta jinjina kai kawai ta buÉ—e motar da zata fita. Mummy ta ce "Mahmud ka shiga ka ga É—an wurin Adam kuwa? Ka san sunanka ma aka saka masa"
Mahmud ya haɗe rai ya ce "Me ganin nasa zai ƙara mini?" Ya buɗe motar ya shige.
Wani abu ne mai ɗaci ya tsayewa ammi a ƙirjinta, ta san da gayya mummy take wasu abubuwan.
Kasa sake kallon in da su Mahmud suke tayi, har motar ta fice daga gidan.
Suna tafe a hanya Mummy ta ce "Mahmud, yakamata ka je ka ga yaron nan, sannan ka yi wa É—an uwanka barka tare da gaisuwar rasuwar matarsa, kar ace ni nake zigaka"
Mahmud da yake murza sitiyari ya ce "Dan Allah mummy ki ƙyaleni da sabgar mutanen nan, ina wuri ɗaya hankalina a tashe ni bana son tashin hankali da ɓacin rai, ni a kan haka sai na bar ƙasar na koma in da na fito, ba dai A'isha ce ba? Na ce Allah ya jiƙanta ya sa ta huta, shi kuma jariri Allah ya raya why sai na ta bin su ina wani gaisuwa abun da ba addini ba".
Mummy ta ce "To shikenan, sarkin faɗa, ni zan saka a ɗauko yaron ka ganshi, duk da nima ɗin sai na roƙa za a kawo mini shi, sau ɗaya na taɓa ganin yaron, shi ma sai da na taka da ƙafata na je".
Mahmud ya ce "Kin gani ko, Mummy meya kai ki? A wulaƙantaki a banza, dan Allah tun da ba sa sonki a sabgarsu, ki ƙyalesu su je sun cinye yaron, ina jin Samha ma na surutun wai ta je an yi mata wulaƙanci a kan yaron, sai ka ce dole ni fa bana zuwa in da ba a buƙatata"
Mummy ta yi dariya ta ce "Sarkin tsari, mu bama son zumunci ya samu matsala ne" ya É—an É—age kafaÉ—a alamar ko a jikinsa.
Ammi kuwa har suka je gidan turaki, ba ta hayyacinta, ta yi zurfi a tunani, sai da direban ya ce mata sun zo, sannan ta dawo hayyacinta ta sauka, ta shiga gidan.
Tun da mama ta ganta take ta wani cin magani, tana hura hanci, samha ce dai ta din ga rawar jiki da ta ga ammin, tana tambayarta ya sabir.
Ammi ta amsa mata cikin sakin fuska ta ce "Dan Allah samha ki aika ayi mini iso wurin mai girma turaki"
Samha ta ce "To ammi" gaba É—aya samha ta din ga tsuma, har a ranta take jin, anya ba a kan batun aurenta da takawa ammi ta zo ba, amma ai idan haka ne, da mai girma turaki ne zai yi mata zancen. Da haka ta je ta nemawa ammi iso wurin turaki, ammi ta shiga wurinsa.
Cikin sakin fuska da girmamawa, suka gaisa da turaki, ya ce "Tun É—azu muke tsumayinki da ki ka ce mana zaki zo"
Ta risuna ta ce "Tuba nake, ayyukan iyali ne suka sha kaina, tuba nake Allah ya baka nasara"
Turaki ya ce "To Madalla, Allah ya yi mana jagora ina abokin nawa, baki zo mini da shi ba?"
Ammi ta yi murmushi ta ce "Yana gida, ka san baya son mutane, yana ƙyuya, kar mu zo ya cika maka kunne da kuka, ko yayi ta zare maka ido" tayi maganar cikin murmushi.
Turaki ya ɗan yi dariya ya ce "Ai barewa ba ta gudu ɗanta yayi rarrafe, haka zalika kalar kumbo kalar ƴaƴanta, haka shi takawan yake ai ko da yana ƙarami, da aisha ya ɗauko da an ga haƙuri da fara'a, amma takawa dai kam hmmm"
Ammi ta yi dariya ta ce "Kun fi kusa ranka ya daÉ—e, ba ruwana" suka yi dariya gaba É—aya.
Ya ce "To giwa meke tafe da ke ki ke son ganinmu da gaggawa haka? Allah ya yi zaki samemu, dan gobe in Allah ya kaimu muke sa ran tafiya umara"
"Allah sarki, Ubangiji Allah ya sa ayi ibada karɓaɓɓiya"
Ya amsa da amin, tare da sake tattara hankalinsa a kan ammi.
"Allah ya taimake ka, dama wata muhimmiyar magana ce ke tafe da ni, wani hukunci na yanke da zartar da shi dole sai da izininka, kuma kai zaka yi mini jagora zuwa ga tabattauwar abun cikin hukuncin Allah"
Ya jinjina mata kai cikin nutsuwa alamar yana sauraren ta.
Ta ɗora da cewa "To bisa ga al'ada ta masauratar nan, duk cikakken ɗa a gidan nan, a kan yi masa zaɓi na matar da zai aura, ko ya kawo wadda yake so ƴar mutunci idan ta yi a aura masa. wani abu ne ya taso a kan yarinyar nan rumaisa, ƴan unguwar su suna ta yaɗa jita-jitar wai ciki ta yi aka kaita aka ɓoye ta haihu, sunanta dai ya ɓaci a unguwar su, na ga babu wata hanya da zamu bi domin wanketa face Adam ya aureta, duba da irin matsanancin son da take yi wa yaron nan da ta zo da shi, har ina ganin kamar rabata da yaron na shiga hakkinta, saboda na san ciwon abun, ga wannan abu da ya kunno kai game da rayuwarta, na ga abu ɗaya zan iya yi shi ne in sanya adam ya aureta, amma ya ka gani ranka ya daɗe?".
Turaki ya ce "Ikon Allah, kin ga nan Jamil ya zo mini da zancen, akwai buƙatar Samha ta maye gurbin Fulani, duba da yadda ta daɗe tana son adam, dan har na yi na'am na so na tuntuɓeki, to sai gashi kuma kin zo da wani zance da yakamata a tsaya a duba. Tabbas! Idan har da yadda zamu yi yarinyar nan bai kamata mu bari ta wulaƙanta ba, dan haka a wannan karon ma samha sai dai ta yi haƙuri, ko kuma idan yana da ra'ayi ya haɗasu biyu, amma rumaisa ita tafi cancanta ya aura, duk da ƙanƙantarta".
Ammi ta É—an ji rasss, ba za ta yi fatan adam ya haÉ—a rumaisa da samha ba, duk da rumaisa yarinya ce amma ba za ta yi fatan ta zama bora ba, tun da dai haryanzu ba ta isa rayuwar aure ba, tana son ya aureta ne dan ya inganta rayuwarta, a haka idan ta ce za su cigaba da É—awainiya da rumaisa, Æ´an uwanta ba zasu harda ba, dan ta lura suna da gudun abun hannun wani.
Turaki ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san akwai ƙalubale, a ƙa'idar masarauta, ƴaƴan sarakuna ƴaƴanmu suke aure, ko ƴaƴan wasu manya, akwai gwagwarmaya idan aka kai maganar nan gaban su wambai"
"Allah ya taimakeka shi ya sanya na zo wurinka, na san kai kaÉ—ai ne zaka iya shiga lamarin nan ka tsayawa adam, jikina yana bani akwai alkhairi a game da lamarin nan, rumais alkhairi ce ga adam"
Ya ɗan yi shiru ya ce "To babu laifi, in Allah ya yarda idan na dawo, zamu yi magana da su, na sanya zancen cikin addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabattar ya kawo komai da sauƙi"
"Amin ya rabb, idan komai ya daidaita bana son abun ya wuce watanni uku, kar wani abun ya kutso"
Turaki ya ce "Babu damuwa, babu abun da zai gagara da ikon Allah"
Ammi ta risuna, ta sake yi wa turaki godiya, sannan ta tashi ta fita.
Samha ce ta raka ammi har mota, tana yi mata ta gaida gida.
Ammi na tafiya samha ta koma É—akin ta, ta É—au wayarta ta kira jamil.
Yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Yaya jamil, yau ma ammi ta zo wurin mai girma turaki, dan Allah idan ka zo yau ka tuntuɓe shi da maganar, ka ji ko ita suka yi?"
Jamila yayi tsaki ya ce "Ke kin fiye abun haushi wallahi"
"Dan Allah yaya ka taimaka".
Ya ce "Gaskiya bana nan, bana gari sai dai ki jirana dawo, idan na dawo kuma yana umara, na san duk abun da ake ciki dai, in dai a kan maganar ne zasu tattauna da mama"
Samha ta É—an yi shiru sannan ta ce "To shikenan, na gode " ta kashe wayar cike da fatan Allah ya sa tattaunawa suke a kan ta maye gurbin Fulani.
***
Ana idar da sallar magariba, Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faɗa, ta ƙi cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa.
Aikowa aka yi wai ana sallama, ganin ba a faÉ—i da wa ake sallamar ba, ya sanya Usman tashi ya fita ya ga waye yake yin sallamar.
Aikuwa yana fita ya tarar da mijin maƙwabciyarsu, ya kawo ƙarar rumaisa a kan abun da ta yi musu, na jifa a cikin gida ta yi musu ɓarna, ga uwa uba fashewa matarsa baki ada marmara da rumaisa ta yi.
Usman ya ce "Malam shamsu ai ɓarnar da matarka ta yi mana ta fi wadda ruma ta yi mata, shiru kawai muka yi, duk yadda ruma take girmamata bai hanata yi mata ƙazafi a cikin unguwa ba, ba dan mama ta hana ba, ga kuma albarkacin aure, sai na yi mata wankin babban bargo a cikin unguwar nan, amma tun da abun ya zo da haka, kawai duk sai mu haɗu mu yi haƙuri".