← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 124

Sashe 65

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy ta din ga tsorata Mahmud a kan Adam, da sai da ta kawo, ba mai kallon wani, juya masa bayan da mahaifinsu ya yi, ba ƙaramin tsaye masa ya yi ba a ransa.
Sai dai ya je ya saka Ammi a gaba, ya yi ta kuka, abun da ake yi musu da tare shi da Mahmud, yanzu sai dai ayi wa Mahmud shikaɗai, hakan ya sanya ya ƙara tsanar Mahmud!.

Roƙon Allah da neman magani, da Ammi ta dage a kai ne, ya sanya ya samu sassauci har ya koma makaranta.

Lokacin da za su shiga jss1, Mummy ta saka aka kai Mahmud boarding, aka raba shi da gidan baki ɗaya, dan yanzu galadima baya iya ƙetare maganarta.

A hankali aka É—an fara sakin jiki da Adam, cousins É—in sa suke wasa da shi, kasancewar makarantar su ma É—aya.
A gidan su jamil, gidan turaki wanda yake wa ga sharif, akwai ƴar sa ɗaya da ya ɗorawa so shi ma, bayan mahaifiyarta ta rasu, mai suna Aisha yake kiranta da fulani, sai dai a bayan idonsa, babar su jamil, ta tsani yarinyar, kamar ba ƴar sarauta ba, saboda azabtarwa daga yayyenta, da kuma uwar riƙonta.

Tun ana yi a bayan idonsa, aka dawo yi a gaban idonsa, ba ya iya cewa komai, wasu lokutan ranar juma'a sai Ammi ta aika a É—auko mata Aisha, a kai mata ita, ta yi mata kitso, ta saka ayi mata lalle, tana son Æ´a mace, laila kuma ta riga ta balaga.

Ana haka Ammi ta haifi nusaiba, ta din ga murna, ta samu Æ´a mace, da wata salla suka je gombe, a nan yayan Ammi yake ce mata, ya wuce ta rigar su ade, ya ga kamar da mutane.

Nan da nan Ammi ta É—au hanya ta tafi, sai dai ta je ta tarar da wata kyakywar bafulatanar yarinya, da ciki.

Suka gaisa da Ammi, take tambayarta, ina su Ade.

Yarinyar ta ce "Ade kakata ce, sun yi gaba, ni daga yaye aka bar ni a wurin yayan babana, to sun tashi zasu tafi can iyaka, in da tushenmu yake, ni dai ban san sunan wurin ba, to mu ma can zamu tafi, da ni da yayan babana ne, da matarsa sai maigidana, sauran ayarin da muka taso tare sun yi gaba, ni kuma na yi nauyi, shi ne aka ce mu zauna in haihu, sai mu tafi, yayan babana ya san in da suke, ina son in ga Ade, kakata".

Ammi ta ce "Allah sarki, Ade kam tana bani labarinki, ta ce mamanki ma tana wata riga tana aure ko?"

Yarinyar ta jinjina mata kai.

"To ina mijin naki da matar yayan baban naki?".

Ta ce "Sun tafi kiwo, ita kuma ta je yin itace".

Ammi ta din ga murna ta ga jikar Ade, kasancewar za su yi kwanaki a can, ya sanya kusan kullum sai ta je, har suka saba da matar yayan baban ade.

Ammi ta sha mamaki, irin yawon da fulanin nan suke da shi, sun yi sanani sun hayayyafa, sun shafe shekaru a wurin, kuma su tashi su yi wani wurin kamar wasu iskokai.

Mijin yarinyar ma, mairamu yana matuƙar girmama Ammi, su yi ta ɗaukar nusaiba suna yi mata wasa.

Ammi kar ta tafi ta bar gida, dan ƙarfin zaman na ta ma, ayi wa Adam Addu'a ne, da nema masa magani.

Bayan Ammi ta koma Kano, tana yawan yin waya, a kan aje a gano mata jikar Ade.

Sai dai aka kira Ammi, daga garin su, aka gaya mata, an kashe mijin mairamu, an kore dabbobinsu, kuma an rasa yayan babanta da matarsa.

Kasancewar ammi ba laifi, tana faÉ—a aji, ta saka aka kai report wurin Æ´an sanda, amma ba wani labari, Mairamu ta tayar da hankalinta, a gidan su Ammi aka yi wa mijinta sutura, aka rufe shi.

Ita ba ta san kowa ba, sai mijinta da yayan babanta, in da suka baro, duka suka taso, ayari sun yi gaba sun bar su, dan su har a lokacin ba ruwansu da abun hawa, kuma ba ta san in da za aje ba, dan ta na da ƙuruciya sosai abun da ta riƙe a in da za su je kawai shi ne kan iyaka, nan ne tushensu.

Saboda tsabar damuwa, ta fara naƙudar dole, aka kwasa aka kaita asibiti, ta haifi yarinaya kyakkyawar gaske, jawur da ita.

Ammi ce ta yi mata role É—in uwa da na uba, dan ba zata manta karamcin Ade ba.

Ta tambayeta sunan da za a sakawa Æ´ar amma ta ce ta saka mata duk sunan da take so.

Ammi ta ce "Ta saka mata Khadijah, sunan mahaifiyar ta, kuma ƴar ta da ta taɓa rasuwa, amma take ce mata Iman".

Ta din ga rarrashin mairamu, tana bata tabbacin, za ta yi ƙoƙari a nemo in da ƴan uwanta suke, kuma a lokacin waya sai gidan manya, balle a sameta hannun bafulatanin daji.

Haka Ammi ta din ga sintiri tsakanin kano da gombe, mahaifiyar laila da ammi ta riƙe, ta cigaba da ɗawainiya da Mairamu, dan a lokacin suma iyayen duk babu.

Sai dai har watanni uku, babu labari a kan in da ƴan uwan mairamu suke, ga ƙuriciya kuma ta yi ta fama da rashin lafiya, ƙarshe Allah ya yi mata rasuwa.

Ammi ta yi kuka sosai da sosai, ta ce sai yayarta ta bata Iman, ya ce ba zata ba, sai ta nemo iznin mijinta.

Ammi ta yi wa galadima bayani, ya ji rauswar yarinyar, kuma ya san É—awainiyar da Ammin ke ta yi, dan haka ya ce ta É—aukko Æ´ar, dan ya san soyayyar da ke tsakanin Ammi da Ade.

Ta zube har ƙasa ta din ga yi masa godiya.

Ta je ta É—aukko Iman, a lokacin kuma ta riga ta yaye Nusaiba, ya ce ko magani za ta yi, da ruwan nono zai dawo ta shayar da iman, yayarta ta ce kar ta shayar da ita, ta na da Æ´aÆ´a maza, ba ta san me gobe za ta yi ba.
Haka ta haƙura, ta ɗaukko iman, ta zo tana bata madara.

Kowa ya ga Iman sai ya tankata, saboda tsananin kyan da take da shi, gaya jaririya, amma gashinta irin na larabawa, mai tsawo.

Nan ma mummy ta samu na yi, wai Ammi saboda jaraba, an yarda ƴar shege ta ɗaukko wai tana so, kamar ƴar jari bolan ƴaƴa, ɗan kowa ma sai ta ɗaukko ta ce za ta riƙe, da ganin kyan wannan yarinyar, an san shegiya ce.

Aikuwa aka yadda, wasu lokutan ammi har mamaki take, yadda sirrikanta ke fita.

Jamila ta hurawa galadima wuta, a kan lallai ya sa ammi ta mayar da ƴar nan, duk dan ta cusa wa Ammi baƙin ciki.

Ya kuwa je ya samu Ammi ya ce bai yarda da riƙon ƴar ba, sai da Ammi ta dangana da wurin sarki, da mai babban ɗaki a kan su saka baki.

Mai babban É—aki ta ce "Dan Allah idan ma Æ´ar tsintuwar ce, ita ta na so, Æ´ar ta yi mata kyau Tubarkallah".

Da ƙyar galadima ya amince, bayan mai martaba ya yi masa ta tas, a kan abubuwan da yake yi.

Iman ta fara girma, ga fari ga kyau, ga uban gashin nan, kullum tana tare da laila da su nusaiba, ga Aisha idan ta zo, amma muddin ta sake suka haɗu da Mahmud, Fauziyya ko ruƙayya, to tabbas sai ta yi kuka, saboda cin zali.

Sai dai duk da haka, ƴaƴan jamila na shiga wurin Ammi, kuma ba zaka ce ba nata bane ba, sai dai suna tsoron laila, dan suka yi mata rashin hankali ubansu take ci, duk da ana yi mata gorin ba gidan ubanta ba ne ba, ta kan ce musu, Jamila ma an riƙeta ba a gidan ubanta ba, dan ita har da Mummyn ma yi take yi, duk yadda Mummy ta so ta saka Galadima ya kori laila abu bai yiwu ba.

Adam kuwa yau fari, gobe tsumma, kusan kullum cikin rashin lafiya, idan ciwon nan ya tashi kuwa, haka zai ta burgima yana ihu, yana neman abun da zai riƙe ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta.

Sashin Ammi ya zama wurin faɗi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting ɗin sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin ɗan ta ya kashe musu ƴa ƴa, amma yaran sun riga sun shaƙu da ita.

Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faÉ—a, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata É—a, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faÉ—an da yake yi masa.

Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai.

Adam ba ya jin daÉ—in hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro.

Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ƙaddarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ƙauna sama da su.

Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daɗin rayuwa da su, a haka ɗan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ƙasar.

Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taɓa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam ɗin.

Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taɓa ɗaga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaɗowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faɗan sunan sa ba.
Chapter 65 · 0% Book details