Sashe 38
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidansu rumaisa ma, shirye shirye sun yi nisa. Mai sunan baba ya buga wani invitation ɗin na ɗaurin aure, aka rubuta sunan Adam sharif, ba tare da sanya cikakken sunan Adam ba. Ba ƙaramin mamaki ƴan unguwar su rumaisa suka yi ba, jin za ayi mata aure, wasu suka din ga surutu suna cewa sai ka ce a ƙauye, wasu kuma suka ce ta tabbata rumaisa ta yi cikin shege ne, ake son a liƙawa wani, kuma aka kasa gane wanene mijin, sai dai hatta wurin da aka rubuta za ayi bukukuwan a wurin ba ƙananan wuri ba ne, nan ma aka yi ta surutun ina suka samu kuɗin kama wannan wurare.
Zaman Gwaggo a gidan, ta din ga yi wa rumaisa faɗa, tare da nasiha a kan aure, da yadda za ta kula da miji, sai dai sam rumaisan ba ganewa take yi ba, yadda aka sakata a gaba ana sake koya mata girki ya fi komai ci mata rai, a ganinta ana hanata hutawa, girkin nan da karambani ta iya shi, dan tun shekara tara take gwadawa, tun mama tana hanata har ta haƙura ta rabu da ita.
Samha ta yi kuka kamar zata yi hauka, gaba É—aya ji take komai ya fita daga ranta, ko abincin kirki ba ta iya ci, sabuwar soyayyar adam ta dawo mata sabuwa fil, sai dai ta yi alwashin yadda ta zubar da hawayenta a kan sa karo na biyu, daga shi har matar ta sa sai sun É—anÉ—ana kuÉ—arsu.
Fauziyya ta din ga zigata a kan ta san duk yadda za ta yi, ta cuzgunawa matar da adam zai aura, har da ba ta tabbacin cewa, ta ji an ce auren haɗi ne ba son ta yake yi ba.
Ana gobe za a yi wa rumaisa jeren kaya, Adam ya É—auki Aliyu da Abdallah, zuwa gidan rumaisa, dan su gani daga nan ya basu mukulli.
Sai dai da suka je, Aliyu ya raina kayan da suka saya, da suna ta murna sun yi wa rumaisa kaya masu kyau da yawa, sai dai gidan babba ne sosai.
Sama da ƙasa ne, ƙasan akwai babban falo, da ɗakuna biyu, da kitchen da store, saman bene kuma falo biyu, bedroom uku, da kitchen da dining, kowane ɗaki da toilet.
Gidan ya tsaru yayi kyau, dan an kashe kuÉ—i wurin yin sa sosai.
Aliyu suka yi ta santin gida, suna yi wa Adam godiya. Sai dai tun da suka koma gida suka sanar da mama, gidan yafi ƙarfin abun da za a kai, jikinta yayi sanyi, dan ba dan kar ta nuna halin ƙaranta ba, cewa za ta yi idan da ƙarami a saka rumaisa a ciki.
Kaf Æ´an unguwa ba wanda mama ta ce su je yi wa rumaisa jere, Æ´an uwanta da Æ´an uwan mahaifinsu rumaisa, sai yayyenta ne suke je suka jera mata abun da ya samu a saman benen.
Gado biyu aka yi mata, dangin babansa suka yi mata ƴan waje guda ɗaya, yayyenta suka yi mata ƴan gida, masu matuƙar kyau.
Kitchen É—in ta ma babu laifi, a dai Æ´ar talaka, iyayen rumaisa sun taka rawar gani sosai da sosai, ga kujerunta da labulaye, ga dininga komai dai-dai gwargwado.
Ƴan uwa suka dawo, suka din ga santin gida, suna yi wa mama barka da arziki, rumaisa ta je gidan hutu.
Da daddare Adam ya je gida da shi da su ammi, suka ga jeren da aka yi, ammi ta jinjinawa ƙoƙarin iyayen rumaisa, ba ita ba shi kansa adam, abun ya bashi mamaki, aka jere mata akwatunanta goma sha biyar a bedroom.
Washegari Adam ya saka aka kawo abubuwan da babu, wanda basu ƙarasa ba.
Rumaisa ba ta yadda aurenta za ayi ba sai da satin biki ya kama, dama Aliyu sun shirya football match, a nan cikin unguwa.
Tun da rumaisa ta tabattar da idan aka yi auren barin gidan za ta yi, ta fara koke-koke tana fasa.
Ranar da za ayi bridal shower, daga gidan su adam, aka aiko da mota, aka ɗauki rumaisa zuwa gidan kwalliya, ita da ƙawayenta, babu ko sisinsu, aka yi musu kwalliya aka wuce da ita wurin biki.
Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ƙawayenta.
Rumaisa gaba É—aya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan Æ´ar yarinyar takawa zai aura?.
Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ƙawayen amarya.
Babu zato babu tsammani, sai ga ƴan mazan mama sun dira a wurin, da shigar ƙananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.
Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.
Yasir ya ce "Taɓ, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?"
Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ƙaiƙayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan ɓata kwalliyar"
Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau"
Mamaki ne ya kama Æ´an wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.
Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ƙara gyara cake ɗin da yake kan table.
Rumaisa ba ta taɓa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.
Gaban table ɗin ya ƙarasa, kusa da iman ya ɗauki ƴar ƙaramar wuƙar yanka cake ɗin, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buɗe bakinta, ta buɗe kaɗan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ƙanwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake ɗin idonta ya cika da ƙwalla.
Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haÉ—e rai ranar aurenta"
Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ƙoƙarin yin abun da zai kwantar mata da hankali.
Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba ɗaya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a ɓangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haɗa ido, gabanta ya faɗi.
Ƙarshe dai da su aka gama partyn, suka ɗauki ƙanwarsu suka yi gida.
Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.
Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.
Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.
"Me ki ke jira baki tafi gida ba?"
A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho".
"Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command.
Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.
Ayshercool
08081012143
What's app only please
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.
Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a É—aki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.
Ƴan uwa sai bawa rumaisa haƙuri suke yi.
"Meye haka?" Ya faÉ—a a kausashe.
Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daÉ—i za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi"
"Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya"
Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar É—akan mama.
Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba É—aya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.
***
Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.
Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta É—aga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.
"Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?"
"Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?"
"Babu É—aya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?"
A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest"