← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 124

Sashe 16

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam lawan ya ce "Wai Meye haka ne Aliyu, ina nan aka sace ƙanwar ta ku me ku ka yi, sai yanzu zaku haddasa mana masifa a cikin unguwa"

"Wallahi malam lawan, duk shekarun da muka yi tare a unguwar nan, idan ka taɓa rumaisa sai na tuɓe na yi maka bugun sakwara, saceta kuma da aka yi wannan ƙaddararta ce, ba yadda muka iya"

Rumaisa ta riƙe hannun Aliyu ta ce "Yaya mu tafi gida"

Da ƙyar rumaisa ta riƙe hannunsa, suka juya suka fara tafiya, sai dai ana sakin mai kada, ya zare wuƙa ya nufi Aliyu da ita gadan-gadan yana ihu.

Ihu rumaisa ta saka ganin wuƙa tsirarata, wuƙa ba ta wasa ba an nufo yaya Aliyunta da ita, wanda ba da tabbacin ita aka nufo ko shi. Aliyu ya hankaɗeta, ya kuma riƙe mai kada suka hau kokawa ga wuƙa tsirarta.

Aliyu ya danne mai kada a ƙasa, ya ɗau wuƙar ya ce sai ya yankashi da ita a wurin.

Nan aka din ga kokowa da Aliyu, aka kasa ƙwace wuƙa.

Rumaisa ta ce "Yaya Aliyu kar ka yi kisan kai, amma dai ka yi masa dukan tsiya".

Cikin takunsa na isa da taƙama, ya din ga ture dandazon mutane, ya ƙarasa in da Aliyu yake kan mai kada ana fama da shi, ya riƙe hannun Aliyu mai wuƙar ya murɗa, ya jefar da wuƙar, sannan ya ɗago shi daga kan mai kada ya tsayar da shi a kan ƙafafuwan sa ya Kalleshi ya ce "Meya haka? Shaye-shayen kai ma ka fara ne?" Ya kalli rumaisa ya ce "Duk saboda ke ko? Sai ku wuce mu tafi ai".

Daga kwance mai kada ya ce "Na rantse da girman Allah, idan har ina yawo kana yawo a unguwar nan, sai na kasheka na kashe matsiyaciyar yarinyar nan, na ga uban waye gatanku"

Aliyu ya sake tunzura, jijiyoyin kansa suka kumbura, mai sunan baba ya kalli mai kada ya ce "Idan kana zubar da jini a unguwar nan kai da yaranka, ana tsoronku, kar ka ratso ta gidanmu, wallahi duk wanda ka zubarwa da jini in dai É—an gidanmu ne, kaima sai na zubar da naka, ka kiyaye"
Ya riƙe rigar Aliyu, hannu ɗaya ya tankaɗa ƙeyar rumaisa zuwa gida.

Mutane wasu har da shewa, abun ya burgesu, kaf unguwar nan babu gidan da suke da haÉ—in kai da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa.

A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ƙasa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba.

"Mai sunan baba, maiyafaru?"

"Kar ki damu, ba abun da ya faru"

Mama ta riƙe Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faɗa da gagararren ɗan daba saboda ɗorawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ƙyaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi haƙuri"

Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu É—inki, suka dawo gida.

Mama ta kai ƙarshen ƙulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ƴan mazan faɗa a kan biye mata wurin tare mata faɗa.

Kasancewar maƙwabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ƴan kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ƴan ƙato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wulaƙancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ƴan sanda abun da ya faru.

Mama har ta bar sallahun a rufe gida, Æ´an sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.

Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha ɗayan dare, ƴan sanda suka ƙi bayar da Aliyu, ƙarshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi iƙrarin kisan kai.

Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da É—ora zargin komai a kan rumaisa.

Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya É—an tsaya yana kallon ammi.

"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka saƙo ka kai wa rumaisa"

Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ssƙon?"

"Ban isa ba kenan?"

Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai"

"A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata saƙo, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran"

Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa.

"Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo"

Bai ce komai ba ya fice.

Ayshercool.

Chat me on what's app, to subscribes yours
08081012143
*PAID BOOK NE, ₦500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143*

Gaba É—aya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata Æ´ar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama.

Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama Æ´an koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci.
Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke"

Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi É—akin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata.
Ta leƙa ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?"

Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai"

Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karɓo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai"

Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau.

Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na É—aga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa Æ´an sanda"

Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case É—in tukuna".

Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ƙwai cret huɗu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya ɗiba, gaba ɗaya mutane fuska biyu ce da su".

Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret É—aya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa"

"Au laɓe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faɗa yana nemo abun duka.

Da gudu ta shige É—akin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station É—in.

Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman"

Mama ta ce "Ni dai ka ƙyaleni na je na ga a yaya ya kwana?"

"Lafiya ƙalau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi haƙuri" da ƙyar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi.

Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo.

Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wataƙila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini ɗa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?.

Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuɗin makaranta, ba babban abun da ya sake ƙular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naɗi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai.

Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta.

Kamar yadda ammi ta buƙata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta.

Ya ɗau sabir yana yi masa wasa, sai dai ƙememe yaron nan yaƙi dariya, sai bin sa da yake da kallo.

Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?"

"Eh, na biyo na karɓi saƙon ne".

Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki".

Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir.

"Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ƙalubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ƴar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuɗin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi"

"To, Allah ya wuce mana gaba".

"Amin, wai da ce mini yayi, Jamil ya ce ko za'a maye gurbin Fulani da samha, ni dai ban ce komai ba na shigar da maganar rumaisa, dan ita ta fi kwanta mini"
Chapter 16 · 0% Book details