← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 124

Sashe 81

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laila ta kalli ruma ta ce "Kina ji na ko?" Rumaisa ta ji kamar ta ce mata 'Da ni kurma ce?"

Amma a zahiri ta ce "Eh"

"Tun da yau mijinki ya tafi, dama ya bar sallahun kai ki makarantar matan aure, gobe in Allah ya kaimu za a fara kai ki, daga nan zaki kwaso kayanki na gidanki ki dawo nan. Ni na karɓi ragamar kula masa da ke kafin ya dawo, dan haka dole zaki din ga bin duk abun da na saka ki, bana son gardama ko rashin kunya, dan idan rashin kunya ce, sai dai ki koya a wurina. Idan kin dawo daga makaranta, zan din ga yi lesson da kaina, da kuma dabarun zaman aure.

Abu na gaba, zamu din ga gyaran jiki, naga kina da tsabta, kuma kin iya girki ma, amma dole zamu din ga shiga kitchen tare ki koyi wasu abubuwan.

Wannan fatar taki, so nake ta murje ta fi haka haske da kyau".

"Taɓ wallahi ba zan bleaching ba".

"Ni ma ba bleaching na ce ki yi ba, gyara za ayi, wannan gashin ma, ya ce ba kya son kitso, dole ya din ga shan gyara, ga iman nan, ita zata ja ragamar koya miki makeup"

"Ni gaskiya idan na yi wannan damɓare-damɓaren, fuskata ƙaiƙayi take yi, duk in ji ta ɗaure kamar ta tsohuwa".

Laila ta ce "To kar ki yi mana, kanki zaki yi wa, iyaka ya kawo wata matar mu shige masa gaba yayi wani auren, kuma dole ki koyi magana, ki daina yaɓawa mutane magana son ranki"

"Na iya magana, kawai sai an yi mini ba dai-dai ba, nake yaɓa maganar".

"Ke! Baki san komai ba game da rayuwa, shi kansa mijin naki, yadda ki ke yi masa magana, tun da ba sa'anki ba ne, ba haka ya dace ki din ga magana da shi ba, idan kin shirya zaman auren, sai ki bi instructions É—in da zan din ga baki.

Abu na gaba dole ki ga maman Khadija".

Ruma ta yi ƙuri da ido tana kallon laila, wacecec kuma maman Khadija.

Kamar laila ta shiga ran rumaisa ta ce "Na san baki santa ba, amma zaki santa yanzu. Wannan ƙwailar da yake ce miki, a kankaro ki, kema ki shiga cikin sahun manyan mata".

Cikin zaƙuwa ruma ta ce "To ita maman khadijan me zata yi mini?" Dan a yanzu tana fatan su fito, a baya ne take zaton nono bashi da wani amfani a gareta, sai idan ta haihu za ta shayar, amma yadda ake gaya mata kalmar ƙwaila, yana ƙona mata rai.

Laila ta É—ora da cewa "Garin kunun sabayarta zan yi miki order, ki din ga amfani da shi kafin ya dawo, dan ni idan na saya, Canada ake tura mini shi, yana da daÉ—i, zai gyara miki fata da jikinki baki É—aya, kuma ki ciko ki murmure sosai, idan kuma kin shirya cigaba da zama ana yi miki gori shikenan".

Ruma ta tuna iskancin da su Fauziyya suka din ga yi mata, wai a kalli ƙirjinta kamar plate, ga samha cikakkiyar mace, amma takawa ya aureta, ta gyara zama ta ce "To ita maman khadijan a ina take? Kuma yaushe zaki sai mini kokon nata".

Laila ta ce "Ni ban ce miki koko take sayarwa ba, garin kunun sabaya take sayarwa, amma ba a kano take ba, a zariya take, bayan federal palladan. Na daÉ—e ina harka da ita, kuma na haÉ—a mutane da ita sosai, na san ingancin kayanta. Zan yi waya da ita, a sayo, tunda tana tura kayanta ko ina, amma ba zan baki ba, sai na ga gwargwadon biyayyarki"

Rumaisa ta yi shiru tana kallonta, laila ta gama bayananta, rumaisa ba wani fahimta tayi ba, ita dai babban fatanta, a samo abun da laila ta faÉ—a na yin kunu, saboda ta sha ko ya fito ta huta gori.

(*INA UWAR GIDA DA AMARE, INA WANDA SUKA HAIHU, KO SUKA YI YAYE, INA MASU RAMA DA SU KE SON JIKINSU YA MURMURE SU YI ƘIBA, INA MASU YARA WANDA SUKE FAMA DA MATSALAR RASHIN GIRMA? SHIN KEMA MIJI NA YI MIKI GORI, KAMAR YADDA TAKAWA YAKE YI WA RUMAISA? SHIN KINA KUNYAR SHIGA CIKIN ƳAN UWANKI MATA, SABODA RASHIN NONO, KO KUWA ƊINKI NE BA YA ZANA A JIKINKI, SAI KIN HAƊA DA CIKO? RAMA CE TAYI MIKI YAWA, KO KUWA YAYE YA SANYA NONONKI YA ZUBE KAMAR BANA MACE BA. TO ALBISHIRINKU! KUKANKU YA ƘARE, HAKA ZALIKA KAKARKU TA YANKE SAƘA. MAMAN KHADIJAH TA SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYE, DA INGANTACCEN GARIN KUNUN SABAYARTA. BAYA CUTAR DA LAFIYA KO KAƊAN, ZAI GYARA MUKU JIKI, YA CIKO DA NONO, INA WANDA SUKA YI YAYE, KO SUKE SHIRIN YI, KU JARRABA WANNAN GARIN KUNU, ZAKU BAYAR DA LABARI, MAMAN KHADIJAH NA NAN A GARIN ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN, KO KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA 08033411249*

Iman kuwa a sitting room ta iske jabir, ya wani hakimce yana danna wayarsa, tun da ta shigo ya kafeta da ido, kamar yadda ya saba. Ta nemi wuri ta zauna, tayi masa sbiru.

"Wai dan Allah iman me na yi miki ne? Meyasa ki ka tsane ni haka?"

Cikin mamaki ta É—aga kai tana kallonsa, ganin yadda yake neman ya raina mata wayo, ya fi kowa sanin abun da ya sanya, ba ta yin sa, amma yake ta wani basarwa.

"Ke shikenan abu ba ya wucewa a wurinki ne?. Son ki nake yi da gaske, aurenki zan yi, magana ta riga ta yi nisa, na samu amincewar ammi, takawa kuma kan ya dawo ma wataƙila an riga an yi".

"Amincewata da ta mahaifiyarka ba ta da muhimmanci kenan?".

Yayi murmushi ya ce "Amincewar hajiya wani abu ne daban, ke kuma a kowane lokaci idan mun yi aure komai zai wuce, dan Allah ki daina taurin kai, ke kanki kin san ba ki da wani rufin asiri, da ya wuce amincewa aurena, idan ba haka ba, duk wanda suka zo a baya sun tafi, sun kasa ɗaukar kasada. Ni a nawa ganin zaɓe-zaɓe ba naki bane ba iman, kamata yayi ki gode mini, da na ce ni na ji na gani"

"Ko ba ka yi ɓoye-ɓoye ba, na san ni ba kowa bace ba, abun da ka ke son gaya mini kenan, amma kasancewata ba kowa ba, ba shi yake nufin zuciyata ba ta da ƴancin ta so ko ta ƙi wani abun ba, ina girmamaka a matsayin yayana, idan farincikin ammi in aureka shikenan, amma ni babu soyayya a raina".

Jabir ya ce "Haka ne, ammi ta yi iya ƙoƙarin ta a kanki, har keta billenta ta yi, ta nemi alfarmar ɗan ta ya aureki, amma ya ƙi hakan, dan yana ƙyamarki, na cancanci ki gode mini ne iman, ba ki ƙi ni ba a halin yanzu ba ki da zaɓi, aure shi ne mafitarki, idan ba haka ba kuwa wannan kyawun barazana ne a gareki"

Sannu a hankali jabir yake gasa mata munanan maganganu, amma ta yi iya ƙoƙarin ta, ta din ga haɗiyarsu, duk da yadda take ji, suna barazana ga zuciyarta.

Jin bugun zuciyarta ya fara ƙaruwa, kuma numfashinta ya fara sama-sama, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta.

Rumaisa na ta jin daÉ—i, tare da fatan, Allah ya sa laila da gaske take, za ta sai mata abun nan, Iman ta shigo, sai dai ba sai an gaya mata ba, ta san iman É—in a cikin damuwa take.

Rumaisa ta yi shiru ba ta ce mata komai ba, ita ma ba ta ce mata ba, ta je kawai ta kwanta a kan gadonta.

Mintuna talatin ammi ta shigo, tana faÉ—in "Iman, ya ku ka yi da jabir ne, ba kya bani update?" Ta tarar da iman a kwance, kamar mai bacci.

Ammi ta ce "Iman Æ´an kwanankin nan baccin nan ya fara yawa, duk in da ki ka samu sai bacci? Rumaisa ko ta gaya miki wani abu ne?".

Ruma ta ce "A'a ba ta ce mini komai ba".

Ammi ta ce "To shikenan"

Da daddare rumaisa ta ce A É—akin iman za ta kwana, duk da ammi ta bata É—aki, amma ta ce a wurin iman za ta kwana.

Cikin dare iman ta tashi ta yi salloli, sannan ta zauna ta É—auki wayarta tana dubawa, rumaisa na kallonta, a haka bacci ya kwasheta.

Da safe rumaisa na baccin safe, laila ta shigo da system a hannunta, ta tashi rumaisa.

Ruma ta buÉ—e ido ta kalleta, "Kin manta hau zaki fara zuwa islamiyya ne? Tashi mijinki zai yi magana da ke"

Rumaisa ta kalleta ta ce "Da computer zan yi wayar?"

Laila ta dungurarwa da ruma computer a gabanta, tana kalla ta ga fuskar takawa.

Ta ce "Laaa video call a computer"

Yayi murmushi ya ce "Hi little mimi".

"Iyee daga zuwa turai har ka koma bature, irin...." Sai kuma ta kalli laila ta yi shiru.

Yayi murmushi ya ce "Ba ki tashi ba ne? Yau zaki fara zuwa islamiyya fa, ki tashi kiyi breakfast, ki shirya a kai ki"

Ruma ta yi miƙa ta ce "Shikenan weekends ma ba zan huta ba".

"Ki yi haƙuri, ina boy, bai tashi ba ko?"

"Eh, bacci yake shi da anty iman, kai har ka karya? Waye ya dafa muku abinci?"

"Har É—aki aka kawo mana, na karya"

"To yaushe zaku fara taron?"

"Sai Allah ya kaimu anjima" ya É—an yi shiru sannan ya ce "Mimi meyasa ki ka bani abun da zai sakani kuka?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ba dan kayi kuka na baka ba, ni ba dare ba rana, abun ci mini rai yake, amma ba na ce maka kar ka tambayeni komai a kai ba, sai anjima, bari na ɗan ƙara rage bacci".

"Mimi tsaya ki ji".

"A'a gaskiya sai anjima" ta ture system É—in ta kwanta.

Laila ta daki ƙafar ruma ta ce "Ke wace irin mashirirciya ce ne?" Ruma ta yamutsa fuska ta kalli ruman.
Chapter 81 · 0% Book details