← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 124

Sashe 117

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta.

Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.

Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.

Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya....

"Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna"

Wambai ya É—agawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?".

"Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.

Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah"

Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.

Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment"

Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta.

Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka É—auki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka É—auki gawar.

A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.

A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faÉ—uwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.

Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.

Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin Æ´an uwanta maza muka yi aikin nan.
Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking É—in ta, haka zalika É—an uwanta Yasir yayi tracking É—in ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result É—in sa, ni ma ina da nawa da police suka yi"

Wani daga cikin Æ´an sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne".

"Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro.
Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin.

Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma'aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki".

Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya.

Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na.

A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa.

Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare.

Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa".

Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma"

Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faÉ—i me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faÉ—a da kanku?"

Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike"

Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba É—aya falon ya hargitse da hayaniya.

Rumaisa ta ce "Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba".

Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba"

Adam ya É—aga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da Æ´an team É—in ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaÉ—ai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu É—aukar maka matakin suna cikin SMOKE.
ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan.
Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa.
Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa  ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil.
Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar.

Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.

Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"

Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba" Hawaye yake zubarwa kamar ƙaramin yaro, cike da ƙunar zuciya. Lallai faɗa da aljani ba daɗi, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta'addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya haƙura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot".
Chapter 117 · 0% Book details