← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 124

Sashe 32

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta yi murmushi ta ce "Na lura son kan ku yayi yawa, kin fiye son Æ´ar nan taki, babu mai takurawa É—ana nima ehe".

Ammi ta yi dariya, cikin jin daÉ—in hirar ta su, suka shiga tattauna yadda yakamata abubuwa su tafi game da auren.

Kamar an jefota rumaisa ta faÉ—o É—akin mama, mama ta É—aga kai ta kalleta ta ce "To madiga, yau babu sallama?".

"Na yi fa, baki ji bane ba, yunwa nake ji"

"Kai rumaisa ni wannan ci naki yana bani mamaki, gidan miji zaki tafi, maza ba sa son mace mai shegen cin tsiya, kuma ba ma cin kirki ba, kina ci kina wasa ba zaki zauna ki mayar da hankali ki ci lokaci guda ki tashi ba".

"Taɓ, aikuwa mama sai in din ga dawowa gida ina cin abincin, Allah ya halicci bawa da ciki, wani ya ce wai baya son mace mai ci"

"Ke tafi can ki bani wuri, yauwwa sirikarki ta ce, in an jima mijinki zai zo"

Rumaisa ta yatsune baki ta ce "Waye mijina kuma?"

"Ban sani ba" Mama ta bata amsa.

"Mama to ni kawai sai ki wani ce masa mijina"

Mama ta ce "Ke, nutsu ki saurareni, bana son wannan shirmen da wautar taki, dole ki shiga hankalinki, aure ba abu ne na wasa ba, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki ka yi wani abu na shirme ba dai-dai ba, wallahi ni da ke ne.

Namiji duk in da yake, ko ba mijinki ba abun girmamawa ne, balle shi da zai aureki, ki ka sake ki ka yi masa wata wautar ko fitsarar, sai kin ga yadda zan yi da ke".

Rumaisa ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tana tunanin shi meyasa ba ayi masa faÉ—an ya daina yi mata abun da yake yi mata, ko dan tun farko ba a san ita me yayi mata ba?.

"Yanzu me ki ke ganin za ayi masa wanda za'a tarbe shi da shi?"

Kai tsaye ta ce"Ruwa"

Abdallah da yake jiyo maganar ta su daga tsakar gida ya shigo, ya ce "Mama, ita fa wannan yarinyar taki, kamar namji take ba ta san komai na rayuwa ba, sai an karanta mata yadda yakamata".

Ya kalleta ya ce "Ke, ki nutsu malama, aure zaku yi, so muke idan ki ka tafi kin tafi kenan, ba zaki dawo mana gida ba, dole ki din ga yi wa mutane abun da ya dace, har zancen ma zan koya miki. Yanzu mama ki kawo kuÉ—i, mu sayo kayan meat pie, in taya ta mu yi, sai a haÉ—a masa da lemon roba da abinci"

"Duk shikaÉ—ai? Gaskiya ni ba zan iya aikin wani meat pie ba, bacci zan yi, ni idan ya zo ma ban san me zance masa ba? Sai dai Huzaifa ya rakani, ko Yasir"

Abdallah ya ce "Ka ga shashasha, tashi ki je ki yo cefanen meat pie É—in nan"

Gaba ɗaya rumaisa ga rasa gane dalilin da ya sanya, kowa laifinta yake gani a kan Adam, kowa so yake lallai sai ta kyautata masa, haka mama ta saka baki, aka aiketa sayen kayan meat pie da za a karɓi Adam.

Abdallah da Huzaifa suka sakata a gaba, a kan aikin, amma ta ƙi mayar da hankali, ƙarshe su suka yi aikin suka ɗai.

Yaya Usman ne ya dawo, ya tarar da su Abdallah suna ta kai kawo, an yi girki, kamar dai wani abu mai muhimmanci na shirin faruwa.

"Wai lafiya na ga ana ta wani shiri, ko bikin aka fara tun Yanzu babu labari, abu na masu hannu da shuni"

Huzaifa ya yi dariya ya ce "Yaya Usman, sirikin ne zai zo, yau zai fara zuwa zance, shi ne ake shirya masa abinci, kar azo a ji kunya. Gara mu  kankaro kanmu, sai dai ita yarinyar ce ba ta da hali, ana saita ta a hanya tana fizgewa".

Usman ya nufi É—akin mama yana faÉ—in, "ubanta kuwa za ta ci wallahi, dole a saita ta. ke kina ina?" Yayi maganar yana shiga É—akin mama, rums ta yi É—ai-É—ai tana kallon Tv, tana cin kantu mai gishiri.

"Ba zaki tashi ki fara shiri ba, yaushe ya ce miki zai zo?"

Rumaisa ta É—aga kai ta kalli Usman ta ce "Oho masa"

"Ke ina yi miki magana, kina amsa mini a haka, tashi zaune"

Rumaisa ta tashi zaune tana ɓata rai. Mama da ke gefe ta ce "Ai gara ku shiga cikin lamarin, tun da ni ba zan gaya mata ta ji ba".

Usman ya ce "Aikuwa da ni take zancen, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki yi masa rashin mutunci, ko wannan cin maganin, sai na yi miki bugun sakwara, ko ki zauna kina wannan ɓata ran, ki na kumbura baki zaki ga yadda zan yi da ke"

"To ni yaya usy ya zan yi? ku fa ku ka ce mini ba ruwana da maza, ni ban taɓa zance ba ban san me ake cewa ba, sai dai Huzaifa ya rakani, ni tsoro ma nake ji".

Usman ya ce "Au idan aka yi miki auren ma, huzaifa ne zai biki gidan mijin, ya tayaki zama da kula da mijin?".

"Ni ba zani gidan kowa ba, sai dai shi ya dawo nan gidan ya zauna, kuma bada Sabir kawai zan kula ba, shi ƙato da shi me zan masa?"

Huzaifa ya ce "Ki ce auren Bollywood za ayi, ayi aure miji ya tare a gidan su mata, yarinya sai dai kar ki yi zancen, idan ni zan rakaki".

Usman ya ce "Ni bari na koya miki abun da zaki ce, ya za ayi wani huzaifa ya raka ki, ya ji kalaman soyayya ya dawo yana tsokanar ki".

Ta kwaɓe baki ta ce "Soyayya kuma?"

Usman ya ce "Eh mana, au da ƙiyayya?" Ta yi shiru, tana kallon Usman.

Ya ce "Idan ya zo, ba ƙifi-ƙifi zaki yi da ido, kina kallonsa kamar fusatacciyar kyanwa ba, ya ga alamar girmamawa a idonki, idan ya zo sai ku gaisa, ki tambaye shi ya mamansa, da ƙannensa da Sabir. Cikin mutuntawa ba da zazzare ido ko harare-harare ba, ki na yi kina sunkuyar da kai, ban da tsyawa ki ƙure shi da ido, na sa cikin naki, duk abun da ya tambayeki ki bashi amsa, ba cikin tashin hankali da masifa ba, sai dai idan kin ga yayi miki wani abu da ya saɓa shari'a da tarbiyyar da aka baki, sai ki zo gida ki gaya mana".

A ranta ta ce "Saɓa shari'a da tarbiyya na nawa kuma, dan dai kawai kar na zubar masa da mutunci ne, amma da sai na gaya wa kowa abun da ya yi mini".

Muryar Usman ce ta dawo da ita hayyacinta, da ya ce "Kin ji abun da na ce ko kuwa?".

"Na ji" ta amsa da ƙyar.

"To tashi ki je ki yi wanka, zan din ga yi ina zagawa in ga yadda ki ke zancen, idan ki ka kuskura, ki ka aikata abun da na hanaki, a gabansa zan tuburbuÉ—aki".

"To yaya usy, ni fa na yi wanka da safe"

Huzaifa ya ce "Sokuwa, wannan wankan tarbar masoyi ne, wankan ganin baby".

"Allah ya kiyaye na ce masa wani baby, kamar wata Æ´ar iska, sunansa Adamu"

Usman ya saka hannu, ya talle mata ƙeya, sai da ta kusa kifawa. "Shashasha, ana koya miki abu kina iskanci, ki je ki yi shirme a auren, zaki gane baki da wayo, tashi ki je ki yi wanka" tashi tayi ta dafe ƙeya, ta fice daga ɗakin.

Mama ji take kamar ta yi dariya, yayyen sun zauna suna koyawa ƙanwarsu, yadda ake yin zancen.

Mama ta ce "Malam usman wannan lakcar, anya ba a zagaya zauruka da magariba? Ba a taɓa bani labarin sirikar tawa ba"

Usman ya sosa kai ya ce "Mama a wurin abokaina nake ji".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ba zan hanaka ba, ni dai fatana aji tsoron Allah, kar a din ga zuwa rage dare wurin yaran mutane, alhalin ba aurensu za ayi ba".

"Mama kar ki kawo komai a ranki ma, ba wurin da nake zuwa"

"Idan ma ana zuwan dai, ai dole na yi kashedi" Usman ya din ga murmushi yana sinne kai.

****
Iman tana zaune a kan gadonta, ta sunkuyar da kai, gefe Nusaiba na zaune, sai kuma jabir da ya saka Iman É—in a gaba da kallo, kamar zai haÉ—iyeta.

"Talk mana iman ko na ji daɗi, saboda an ce baki da lafiya ban gama abun da nake yi ba, na baro Germany, na zo na dubaki kuma kin ƙi magana, talk please"

Nusaiba ta ce "Please iman, stop treating our uncle J this way, ki yi magana mana".

Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin daÉ—i sam"

"Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba"

Ta É—an kalleshi ta ce "Am sorry".

"To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wulaƙanci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it"

Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai"

"Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please"

Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service"

Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita.

A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini zaɓi na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart. Ni ba kowan kowa ba ce, duk zaɓin da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta ƙarasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta.
Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar ƙarfe, an ɗaɗɗaure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace.
Chapter 32 · 0% Book details