Sashe 115
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Da tayi mata fashin ɗan? Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa. Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar riƙon arziki ce za ta raba uwa da ɗan ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da ɗan uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo"
Ammi sai ƙoƙarin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita kaɗai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba.
Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci.
Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu Lagos É—in zamu je, ko yaya za a yi? Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi "
Mai sunan baba ya ce "A'a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya"
"Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya ƙara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya ƴan uwan iman ne "
Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce "Na ce ba" ya juyo ya tsaya yana sauraren sa.
"Akwai buƙatar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba.
A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi É—an uwa daÉ—i. Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya"
Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai" mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi.
Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya, Æ´an dubiya sun fara kaiwa suna komowa.
Sai dai fa cacar baki taƙi tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa.
Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta.
Samha za ta saka baki ruma ta ce "Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai maƙiya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu".
"Su waye mushirikan?"
"Gaku nan gaba ɗayanku, ban da yawon asiri da ƙoƙarin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai maƙiya Allah"
A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kiciɓis a hanya, ta ce masa maza ya je ya ɗau rumaisa ya mayar da ita gida.
Sai dai suna shiga ɗakin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta riƙe ƙugu tana bala'i, Nusaiba sai ba su haƙuri take.
Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta miƙe, ta riƙe ƙugunta.
Ruma ta ce "Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina? Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar É—akunan mu ba?.
Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da saƙo, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka ƙulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta ƙare muku".
Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce "Me ki ka nufi? Nima sharrin zaki yi mini?".
"Wallahi na fi ƙarfin in yi miki ƙarya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri ɗaya saboda sheda, duk bala'inki ke da Adam sai dai ido Samha"
Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi ƙoƙarin hankaɗa Rumaisa.
Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya É—auketa da mari.
Tsit suka yi suna kallon Adam.
"Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi. Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha"
Mahaifiyar Samha ta fara bala'i "Wane irin mutum ne kai? Duk abun da yarinya ta faÉ—a sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan. Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari Æ´a ta"
"Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah"
Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya damar hutawa.
Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida. Mummy ta ce bai isa ba.
Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum É—aya, ruma ta nuna Ammi ta ce "Ga mahaifiyar sa nan" Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa.
Mahmud ya kalli ruma ya ce "Daughter kina ganin bai yi wuri ba?"
"Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo ƙarshe, enough is enough"
Adam ya ce "Ban gane me ku ke nufi ba"
"Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please"
Ammi ta ce "Mahmud, a kawo abincin? Ya ka ke ji yanzu?"
"Alhamdilillah da sauƙi, Yaya zai kawo abincin"
Da azahar takawa ya tafi sallar juma'a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba.
A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sauƙi.
Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce "Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa".
"Cikina dai babu daÉ—i, kar a É—ura mini abinci da yawa".
Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce "Ko a baki zan din ga baka ne? Na iya É—ura ka tambayi deeja ka ji"
Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba.
Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin.
Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun ɓoye ya fito fili, sabir zai yi ƙani.
Ta din ga tura baki, tana harar su.
Ko da suka je gida gaba É—aya takawa ya hau yi wa rumaisa faÉ—a.
"Why are you making things complicated rumaisa?"
Cikin rashin fahimta ta ce "As how?"
"Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an ƙi sakin sa an ce sai mahmud ya je. Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al'amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina ɓoye mini wasu abubuwan"
"Wait" tayi maganar tana É—aga masa hannu.
"Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan? To sai ka koma ka bata haƙuri ai. Ka san dai ba zan yi mata ƙarya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha ƙarya. Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan faɗeta.
Ta ƙarasa ta saka mukulli, ta buɗe wata wardrobe, ta ɗaukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa.
Ta ce "Ga kaÉ—an daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani. Ka duba a ciki har da abun da Samha ta yi, ta saka aka sanya a cikin katifarka da tawa, banda abun da aka binne"
Jikin takwa yayi sanyi, tsigar jikinsa ta tashi, saboda uban tarkacen da suka zubo daga cikin ledar, sai uban wari suke, ƙoƙarin rumaisa ya gani, da ta iya ajiye wannan tarkacen a ɗakinta.
"Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ƴan bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking ɗin ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haɗa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faɗa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana"
A gigice cikin tsawa ya ce "Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faÉ—a ne? Jamil fa ki ka ce"
"Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ƙi, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka ɗauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un " ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa.
Banza ruma tayi masa, ta fice daga É—akin ta bar shi.
Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faÉ—a ba gaskiya bane ba.
Jikinsa yana rawa, ya É—aukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya É—aga amma ya kasa magana.