Sashe 116
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaɗai ba ne ba, manyan ƙusoshin ƙasar nan SMOKE! Sai dai magana mara daɗi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare"
Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske.
Ruma ta dawo É—akin ta tarar da shi ya haÉ—a gumi, sai tsuma yake yi.
"Ka tashi ka bar mini ɗakina, ɗakin maƙaryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so haƙuri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai".
Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar É—akin.
Ta kwashe kayan ta ɓoye, ta ɗauki wayar sa, ta buɗe pin ɗin, ta kira Iman.
Iman na É—agawa ta ce "Kun tafi ne?"
"Eh, amma yanzu su mama suka shiga"
Ta ce "Ok".
Ta kira wayar mama, mama ta É—aga "Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?".
"Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sauƙi sosai".
"Mama dan Allah ba shi wayar"
Mama ta miƙawa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi.
"Hello daughter"
"Jikin ka da sauƙi daddy?"
Ya ce "Sosai Alhamdilillah"
"Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ƙarshen wannan lamarin, zamu haɗu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ƴan sanda"
Ya ce "Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week"
"Shikenan daddy, na gode sosai".
Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ƙarfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana roƙon Allah ya basu sa'a.
Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta.
Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ƙarya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.
Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ƙarfe biyu suna hira.
Ta yi iya ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haɗawa da abubuwan alkhairin Mummy.
Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya É—uri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faÉ—a a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse.
Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ƙarar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station ɗin aka kai shi ba.
Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.
Suna tsaka da wannan bala'in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinsu.
Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi.
***
Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara ɗaki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ƙanana.
"Rumaisa" ta ji ya kira sunanta.
"Ba zamu Asibiti ba?"
"Sai ka dawo, kar na je na kuma ɓata muku zumunci"
"Kiyi haƙuri, na rasa yadda zan yi ne"
Ta ce "Ni ba zani ba"
"Dan Allah "
Ruma ta ce "Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da Æ´an sanda a wurin".
Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je.
Ya ƙyaleta ya fita tafi.
Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki.
Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba.
Ammi ta ce "Takawa, ya dai?"
"Bakomai" zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce "Mummy sai yanzu ko?"
"Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni".
Ya ce "Allah ya baki haƙuri, a cewa likita ya zo ya sallame ni, saboda ayi ta ƙare a yau"
Mummy ba wanda ta kula sai mahmud, suma ba su kulata ba.
"Mahmud ina ka kai Jamil ne? Kana a wannan yanayin zaka je wani wuri? Ka sa matar nan ta tayar wa da mutane hankali, sai bala'i take yi. Ta shafa mini kashin kaji, wai ni na saka ka dake shi ka kulle shi. Ga wani zancen ma wai ko an kama Jamil gaske ne ko ƙarya oho"
Ammi ta ce "Kenan maganar ruma gaskiya ce"
"Ba da ke nake ba, da É—ana nake malama" Mummy ta yi maganar gatse-gatse ga giwa.
Ammi ta ce "Allah ya baki haƙuri"
***
Katafaren falon ya cika ga Wambai, ga turaki da wasu manya daga masarautar kano.
Ammi ta hallara, ga Mahmud dan ko gama warwarewa bai yi ba. Aka jima sai ga rumaisa da takawa, Bashir jami'an tsaro da wasu daga cikin yayyen rumaisa, ga Samha a wurin da mahaifiyar ta, ga Hajiya Lubabatu da duk wanda yakamata su halarci zaman.
Gaban Samha sai dukan uku-uku yake yi, dan bata san mai rumaisan za ta kwatsa ba.
Wambai ya ce "Su kuma waÉ—an nan lafiya?" Yayi maganar yana nuna jami'an tsaro, da suka shigo da jabir, a wahale.
Bashir ya ce "Ranka ya daɗe, zuwanmu wannan zaman yana da matuƙar muhimmanci, zaka ji dalilin zuwanmu in sha Allah. Zuwanmu nan ayi tattaunawar da mu, sai ya fi sirri, saboda wasu abubuwan da za a bayyana, akwai kunya ace wasu laifukan daga gidan girma da daraja suka fito"
Adam ya ce "Allah ya taimake ka, wannan ita ce rumaisa matata kamar yadda ka sani, waÉ—an nan kuma Æ´an uwanta ne, wannan kuma abokan aikina ne"
Wambai ya kalli rumaisa ya ce "Ke! Ke ce mai haddasa mana husuma da tashin hankali a cikin family ko? Kafin ki zo lafiya lau mu ke zaune, amma daga zuwanki kin hargitsa komai, ki ce wancan yana asiri, ki ce wannan baya son wannan saboda me?" Ya fara yi wa ruma faÉ—a, tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Turaki ya ce "Ina ganin, a fara bari mu ji ta bakinta tukuna ranka ya daÉ—e, kar a yanke mata hukunci kai tsaye"
Wambai ya kalleta ya ce muna saurarenki.
Ruma ta ƙulu, basarwa kawai ta yi, ta haɗiye wani abu mai ɗaci sannan ta ce "Kafin na ce komai, zan fara da bawa babana haƙuri a kan abubuwan da zasu fito daga bakina, duk da ya san wasu, na san bai san wasu ba. Ina neman afuwarka babana mai girma turakin kano"
Turaki yayi murmushi mai ciwo, sannan ya ce "Kar ki damu yarinyar kirki, kamar yadda na riƙe miki alƙawari a baya, ina umartar ki da ki faɗi komai, dan fita daga zargi.
Ayshercool.
08081012143
08081012143
Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu.
Silar haÉ—uwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba"
Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji.
Wannan wayar na É—auke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haÉ—a mota da Æ´an bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta É—auka, ciki har da jakar bullet mai É—auke da wasu lambobi, da sunan SMOKE.
A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara.
Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.
Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda.
Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.
Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce".
ÆŠiff É—akin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna".
Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna".