← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 124

Sashe 123

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa kafin ta gama makaranta sai da ta haifi ƴan maza biyu, ta din ga Addu'a "Allah kar ka sa na yi irin ta mama na haifi ƙanwar maza, ba zan iya ba" takawa ya din ga yi mata dariya ya ce ashe kina sane ki ke tsiyata ku.

Idan ta tuna wasu rashin hankalin da tayi a baya, ta ji kamar ta yi wa kanta duka, babban abun da ya bata mamaki, bai wuce duk shekarun nan takawa yana ajiye da wasiƙar da ta rubuta masa, na cewar ya taɓa mata nono, yayi ta tsokanarta yana dariya.

Samha kuwa rayuwa ta juya mata baya, dan abun da Jamil ya aikata, da wanda tayi ita ma, ya zame mata baƙin fenti, aka rasa mai aurenta, duk gayu da ƙwalisar samarin duk suka watse.

Runaisa ba ta bar harkarta ta zane-zane ba, dan har rubuce-rubuce take yi, kamar wasa ta zama popular manyan mutane suke sayen zane-zanenta.

Cikin ikon Allah rumaisa ta zama criminal lawyer, sunanta ya shahara sosai, ga ta lawyer, ƙwararriya wurin zane-zane da rubuce-rubuce, kuma ƴar kasuwa.
A duk lokacin da aka yi hira da ita, ta kan ja hankalin mutane a kan cewa a duk lokacin da aka samu É—a mara ji kamarta a cikin al'umma, kar a tsangwame shi, a ja shi a jiki a duba wace irin baiwa Allah ya yi masa a dafa masa a kanta, saboda Allah baya halittar abun da ba shi da amfani. Kamar dai ita da tun a tasowarta ko makaranta ba ta so saboda rashin jin ta, amma cikin ikon Allah a yanzu, ilimi na addini da na zamani sai dai ta koyar da wani bisa jagoranci da jajircewar mahaifiyarta yayyenta da kuma mijinta ta zama abun da ta zama a yanzu.

TAMMAT BI HAMDILLAH!!!

GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TAIKAI MAI KOWA MAI KOMAI, DA YA BANI IKON FARA RUBUTUN NAN YA BANI ARON RAI DA LAFIYA NA KAMMALA SHI. ALLAH YA SANYA A AMFANA DA DARUSSAN DA KE CIKI, AKASIN HAKA KUMA ALLAH YA YAFE MANA.

SAƘON GAISUWA TA MUSSAMAN, UWAR KIRKI UWAR ALJANNA UWA TA TA KAINA, MALAMA NAFISU ADAMU, DA MUKA FARA TARE HAR NA KALLAMA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCINKI.

GODIYA TA MUSAMMAN GA ƳAN UWANA.
ZEE KUMURYA NIMCY LUV, TARE DA SAURAN MARUBUTA MAIMOON, MARYAM MAI ƘOSAI ANTY ZEETY, KUNA DA YAWA GASKIYA DUK INA JI DA KU DAI.

BAN MANTA DA KU BA, MUTANEN DA SUKA BANI TALLACE TALLACENKU
MAMAN MEENAT COLLECTION
MAMAN KHADIJAH MAI SABAYAR ƳAN GAYU TARE DA MAMAN ILHAM KUN GA DAI YADDA SUKA KANKARO RUMA A GIDAN AURENTA, KAR A GAJI DA CIGABA DA PATRONIZING KAYANSU, TESTED AND TRUSTED RUMA TA YI AMFANI DA SU KUN GANI.

WAƊANDA SUKA YI SUPPORTING ƊINA, WURIN SAYEN LITTAFINA, ƳAN NORMAL GROUP, SPECIAL DA AKE TURAWA TA PC, ƳAN AREWABOOKS DUK INA GODIYA, DA SUPPORTING ƊINA ALLAH YA ƘARO MUKU ARZIKI DA BUƊI MARA YANKEWA.

WAÆŠANDA SUKA DIN GA FITAR MINI TARE DA KARANTAWA, BA TARE DA KUN SAYA BA, DA WANDA SUKA YI MINI AMFANI DA SHI WATA SIGAR BA TARE DA IZININA BA, INA YI MUKU TUNI DA ALLAH BAYA YAFE HAKKIN WANI A KAN WANI, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA.
0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK.

DOMIN GYARA SHARHI, KO SHAWARA ƘOFATA A BUƊE TAKE.
SAI MUN SA
08081012143

Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu.
Silar haÉ—uwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba"

Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji.
Wannan wayar na É—auke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haÉ—a mota da Æ´an bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta É—auka, ciki har da jakar bullet mai É—auke da wasu lambobi, da sunan SMOKE.
A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara.
Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.

Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda.

Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.

Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce".

ÆŠiff É—akin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna".

Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna".

Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta.

Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.

Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.

Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya....

"Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna"

Wambai ya É—agawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?".

"Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.

Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah"

Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.

Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment"

Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta.

Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka É—auki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka É—auki gawar.

A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.

A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faÉ—uwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.

Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.

Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin Æ´an uwanta maza muka yi aikin nan.
Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking É—in ta, haka zalika É—an uwanta Yasir yayi tracking É—in ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result É—in sa, ni ma ina da nawa da police suka yi"

Wani daga cikin Æ´an sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne".

"Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro.
Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin.
Chapter 123 · 0% Book details