← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 124

Sashe 23

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Usman ya fito yana faɗin "Bagidajiya kawai, wannan ai yawa ne ki ka yi, to wallahi nan gaba rainaki zai yi, sai la ce wata budurwar ƙauye, ke ba wani class bakomai"

Abdalla da bai daÉ—e da shigowa ba, ya tambayi mai ta yi, Usman ya gaya masa, ya ce "Kai yanzu har wani aji kake nema a wurin rumaisa, ai tun da suka ce za su aureta a haka, sai fatan Allah ya sanya su gama lafiya"

Ko a jikinta, an mintsini tattaura, abun da ya dameta kawai shi ne a gabanta.

***
Su Iman da suka koma gida kuwa, Ammi ba ta nan, Iman ba ta son ta fita ta koma gida ta tarar Ammi ba ta nan, gashi tare suka fita da Nusaiba, Kasancewar Sabir yayi bacci, da shi Adam ya tafi sashinsa ya kwantar da shi, Iman kuma ta wuce É—akinta.

Sai dai tana zuwa É—akin, ta yi tozali da Samha a tsaye, sai da ta razana ta ce "Anty Samha lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, munafuka tsintacciyar mage da ba ta mage" cikin rashin fahimta iman take kallonta, dan ba ta san me ya kawo wannan maganar ba.

"Saboda tsohuwar munafuka ce, shi ne ki ka je ki ka cewa giwa kina son Adam, za a haÉ—a aurensa da ke a maimakon ni, duk da irin kashedin da na yi miki ko?"

Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kuma?"

"Ke ɗin fa, algunguma ni zaki yi wa pretending, to ki rubuta ki ajiye, gidan Adam kabarinki ne, yadda aisha ta shige shi ta bar duniya, duk wadda ta shiga bani ba sai ta bita, idan ba haka ba kuwa ayi babu, kowa ya rasa daga ni har ke, da ni ki ke zancen, zan yi maganinki baƙar annamimiya"

Gaban Iman ya faÉ—i da jin furucin da Samha ta yi, tana gama zazzage mata ta yi waje.

Jikin iman har rawa yake yi, saboda tsananin tashin hankali, da yadda hankalinta ya dugunzuma, a take rumaisa ta faɗo mata, wato a zaton Samha Takawa ita zai aura, tausayin rumaisa ya kamata ya ruma za ta yi da wannan manyan al'amura ta ko ina, ga maƙiyan mijinta, ga tarin ƙalubalen gidan, ga kuma masifar Samha, a kaf dangin nan babu wanda bai sarawa masifar Samha ba, an shakkarta sosai da sosai, saboda a tsaye take ba ta da kunya, yaya rumaisa za ta yi da ita, ita da take yarinya ƙanƙanuwa?.

Rasa abun yi ta yi, ta saɓule ta zauna a kan gadonta, ƙirjinta na cigaba da dukan uku-uku saboda tsananin fargaba.

Mintuna kusan sha biyar da fitar Samha, amma iman ta kasa kataɓus, ƙirjinta sai cigaba da bugawa yake yi.

Nusaiba ce ta shigo da sallama ta ce "Ashe kun dawo, bamu zaci zaku rigamu dawowa ba, mun je sai wa Sabir kaya, kin san ya kusa 6months, Ammi sai nuna mini irin kayan da za a zubawa amaryar takawa a lefe take, ya kuka baro ta?" Sai da Nusaiba ta kai aya, sannan ta lura kamar Iman a tsorace take.

"Lafiya kuwa?"

Iman ta jinjina mata kai ta ce "Lafiya lau"

Nusaiba ta ce "Kin ga idonki kuwa kamar mara gaskiya, ko wani abun ya faru a gidan da ku ka je ne?" Iman ta girgiza kai alamar a'a.

"Tsaya, ko jikinki ne ya motsa?"

Iman ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu ko ɗaya, cikina ne ya ɓaci zuciyata ce take tashi"

Nusaiba ta sauke numfashi ta ce "Har kin tsorata ni, bari na kawo miki anti acid, ina da shi a É—akina" iman ta jinjina mata kai.

Da Nusaiba ta fita ta sanarwa da Ammi iman ba ta jin daÉ—i, ulcer ya tayar mata, a rikice ammin ta nufi É—akin Iman, ta je ta tutsiyeta tana tambayar ko jikinta ne ya motsa.

Kamar yadda ta yi wa Nusaiba ƙarya, haka ta dake, ta ɓoye damuwarta, ta tabattarwa da ammi, ulcer ne kawai ya tasar mata.

***
Kwanciya ce ta isheshi, musamman da kwana biyun nan, a gida yake wuni saboda ƙafarsa, amma yanzu ta yi saƙi sosai, kawai dai fita ce bai yi ba, gashi ya kusa komawa makaranta.

Kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fita falo, ya ɗau lemon kwali mai sanyin gaske, ya koma ɗakinsa, corridor ya nufa, ya buɗe tagar a hankali, wata sassanyar iska ta dake shi, ya zuƙe lemon tare da lumshe idanunsa.

Dare ne sosai, manyan security lights, sun haske ko ina na gidan, kukan tsuntsye na ta tashi, da ƙanan ƙwari, ga ƙamshim furannin harabar gidan sun gauraye da sassanyar iskar da ke kaɗawa.
Yanayin yayi masa daɗi sosai, sai dai babu tsammani ya ga wani abu yana dudduƙe, yana motsi ta jikin fulawoyin da zai sadaka da sashinsu.

Tsayawa yayi ya ƙura ido sosai, yanayin inuwar abun, kamar mace ce, dan har da lulluɓinta.

Mamaki ne ya kama Mahmud, ganin maimakon ta shigo direct ƙofa, ta kutsa can ƙarshen ginin da kai tsaye ɗakin Mummy zai kai ka.

Bai yi wata-wata ba ya sauka, ya nufi sashin Mummy a hankali, sai dai bai buÉ—e ya shiga ba.

"Kin shanya ni, tun É—azu nake zaman jiranki, amma baki zo ba"

Baba uwani ta risuna ta ce "Tuba nake Allah ya baki yawan rai, sawu ne bai gama É—aukewa ba"

Mummy ta hura hanci ta ce "Ina jinki, bani labari, meke wakana da ki ke son ganina?"

"Allah ya baki yawan rai, labari ne nake tafe da shi, idan yayi miki daÉ—i haka nake fata, idan bai yi ba ayi mini aikin gafara"

Cikin ƙosawa Mummy ta ce "Hanzarta, ina jin ki"

"Takawa zai yi aure, sai dai alamu sun nuna kamar Iman zai aura, kuma zancen ya iske Samha ƴar wurin turaki, dan ɗazu ta zo har wurin Iman ɗin ta yi mata kashedi da zafafan kalmomi, dan na laɓe na ji komai"

"What? Aure kuma? A wannan karon kuma ita za a liƙawa, ita ma ya cinyeta, lallai giwa ba ta tsoron Allah, amma na yi mamakin yadda aka yi Samha ta zo ba ta ƙaraso nan ba, kuma ba ta yi mini wannan bayanin ba, ko da yake ni kujera ce, ko dan zama za a neme ni, jeki na gode na ga yadda wannan lamarin zai yiwu"

Baba uwani ta ce "Godiya nake, na barki lafiya".

Mahmud ya so shiga ɗakin Mummy, dan ganin wacece wannan, take zuwa a tsohon daren nan, amma ya fasa, ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya fita harabar gidan ya laɓe.

Can baba uwani ta fito tana dudduƙenta cikin duhuwar fulawoyi, ta nufi sashinsu ammi, tana buɗe ƙofar, fitila ta hasketa, dan haka ya ganeta da kayan jikinta.
Hakan ya fallasa ma wacece ita, domin kuwa baba uwani kayanta ba ɓoyayyu bane ba, duk da tarin alkhairai da suturar da ammi ke bata, amma kullum cikin kaya ɗaya zuwa uku take.
Kan sa ya É—aure da mamakin me take zuwa yi sashinsu, a wannan daren cikin siga ta rashin gaskiya

A hankali ya koma sashinsa, gaba ɗaya baya son wannan halin na Mummy, na bin diddigi da shiga abun da babu ruwanta, ya san ƙarshe ba zai wuce rahoton wani abun ake kawo mata ba. Amma ya sha mamaki, idan har ace hadimar ammi ta kusa da ita, za ta aikata mata haka, to duniya kowa ma ba abun yarda bane ba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, mai girma turaki ya dawo daga aikin umara da ya tafi, duk da an riga an saba zuwa, amma ba a rasa Æ´an sannu da zuwa da su kan zo, domin yi masa barka da dawowa.
Ammi ba ta son takura masa, dan haka ta bashi lokaci, tare da sauraron abun da zai ce mata.

Duk da a nata ɓangaren ta tsananta addu'a a kan lamarin sosai da sosai, tare da fatan tabattuwar alkhairin da yake cikin al'amarin.

Ɓangaren Samha kuwa, da fari a iya tunaninta, za ta iya ji da lamarin, amma abun ya shallake tunaninta, kuma gaba ɗaya hankalinta ya karkata a kan Iman ce ake ƙoƙarin aurawa takawa, dan haka ta fara tunanin yadda za ta yi da ita, a ƙarshe dai ta koma wurin Khalifa, domin samun mafita sannan ta je ta samu Mummy da zancen.

Mummy ta yi dariya ta ce "Yaro man kaza, ai na yi zaton ba zaki gaya mini ba, shi ya sanya na zuba miki ido na ga iya gudun ruwanki, ba shakka giwa wata irin murɗaɗɗiyar mace ce, mara alƙibla, dan haka dole ki zage ki san abun yi"

Cikin damuwa ta ce "To ni yanzu Mummy ya zan yi?"

"Duk abun da ya kama ki yi, ko dai a kan Iman ɗin, ko kuma a kan giwa ko ma adam ɗin. A baya babu abun da ba mu yi ba a kan yarinyar nan, wanda hakan ya sanya duk ta rasa manemanta manyan mutane da suke zuwa wurinta, dan haka yanzu shine giwa ta yanke shawarar ƙarshe na aura mata adam, shawara ta rage gareki, ko dai ki bari ayi auren daga baya ki san abun yi, ko kuma dai ki ɗau wani matakin"

"Taɓ, ai wallahi da na bari ya aureta, gara uban kowa ma ya rasa, ni Mummy a cikin malamanki nake son ki haɗani da wani, a watsa komai ko da kuwa yana nufin in rasa ta rasa kowa ma ya huta ne"

Mummy ta jinjina kai tana murmushi ta ce "To shikenan, zan yi tunani a kai kar ki damu"

"Mummy ba ni da dogon lokacin da zaki yi dogon tunani, dan Allah ki taimaka".

"Na ji zamu yi waya, ko zuwa sunday ne, akwia wani ƙauye da nake zuwa, sai mu tafi tare"

Samha ta ce "To shikenan, na gode sosai Mummy".

Kusan sati guda da dawowar mai girma turaki, giwa har ta fara ƙosawa, tana tunanin ko magana za ta yi masa, babu tsammanni ya kirata a waya ya ce zai zo.
Hakan yayi mata daÉ—i, sai dai ta shiga fargabar da wacce zai zo, da nasara ko kuma babu?"
Chapter 23 · 0% Book details