← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 124

Sashe 53

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faÉ—ar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daÉ—i".

Ruma ta ce "Ammi, ba dan ya ji haushi na faÉ—a ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daÉ—i ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini".

"Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faÉ—i irin wannan a gaban wani kin ji?"

"To ammi, in Allah ya yarda".

Ammi ta dafa kafaÉ—arta ta ce "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa'a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan É—auko, har gida ta din ga koya miki ".

"Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya"

Ammi ta ce "Waye papa kuma?"

"Baban Sabir "

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku"

Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta.

Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu.

Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani ɓangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaɗi.

Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu.
Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa.
Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta ɓullo wani wuri.

Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi.

Bayansa ta gano ta ce "Papa" a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta ɗan tsura masa ido, sai kuma ta ce "Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taɓa sawa na shigo gidan nan" ta yi maganar tana ƙarasawa in da yake.

Ya ce "Wow, ashe zamu sake haÉ—uwa, sannunki, ya ki ke?"

"Lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana zama a kujerar da ke facing ɗin sa.

"Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?"

Da É—an mamaki ta ce "Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

"Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?"

Ya É—an yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha É—azu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito.

"Da gaske ke adam ya aura?".

Rumaisa ta ce "Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?".

"Ina ƙasar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji".

Cikin mamaki rumaisa ta ce "To ta yaya kuna gida É—aya, amma ba ka sani ba, wai ku ba Æ´an uwa ba ne?".

"Eh, kowa babarsa daban".

"To, ku Æ´aÆ´an kishiyoyi ne?".

Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce "Eh".

"Taɓ to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?".

"Ni ma ba ya zuwa wurinmu"

Ruma ta ce "Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi".

"Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?"

"Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daÉ—i".

Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce "Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?"

"Wai meyasa Æ´an dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da É—ankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba".

Mahmud ya yi dariya ya ce "Wow, i like your confidence "

"Wai kai ya sunaka ne?".

"Mahmud" ya bata amsa, É—an turus ta yi tana kallon sa, "Dan Allah da gaske?"

Ya ce "Eh"

Ta ce "Innalillahi, sunan babana, sunan É—a na"

ya ce "Shikenan na yi Æ´a, na zama daddynki"

Ta yi dariya ta ce "yauwwa to ka taɓa zuwa ka ga ɗa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi".

"Zan je wataran".

Rumaisa ta ce "A'a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taɓa gani ba, kai ma sai mu je ka ga ɗa na, mai sunan ka".

Mahmud ya ce "mijinki ya huta kallon Tv, ke kaÉ—ai kin isa ba shi dariya".

Ta ce "Taɓ, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita" ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy.

Ya ce "Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata"

Gaba É—aya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo.

Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ruƙayya, sai dai suna haɗa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faɗuwa.

Mummy ta ce "Wace wannan?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya".

Mahmud ya kalli Samha ya ce "Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba" ya kalli rumaisa ya ce "Daughter, ga mamana nan"

"To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?" Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa.

Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce "Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?"

Mahmoud ya ce "A'a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata".

Fauziyya ta ce "Tirƙashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma"

Samha cikin ƙuluwa ta ce "Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye alaƙarta da ke, tun da ba ɗanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?"

A fusace rumaisa ta ce "Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba".

Mahmud ya ce "Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana".

Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce "Barka da wannan lokaci "

Mummy ta ce "Barkanmu dai, kuna lafiya?".

"Lafiya ƙalau"

"Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini É—an naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?".

Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

Mummy ta ce "Ruƙayya, ki saka a kawo mata abinci".

"A'a na ƙoshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi".

Cikin ƙarfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ƙirjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta.

"Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk Æ´aÆ´anmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruÉ—ani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun 'yan bindiga, abun bai yi mana daÉ—i ba".

Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud "Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka alƙawarin" kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taɓin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban.

Yayi murmushi ya ce "To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta".

Rumaisa ta ce "Eh, Mummy sai anjima "
"To amarya, sai mun zo gidan naki kuma"

Allah ya kawo ku.

Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ruƙayya ya ce "Wannan ƙannena, ga Fauziyya ga ruƙaiyya"

Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce "Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini Æ´ar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaÉ—ai ya yi mini mutunci a gidansu".

Yayi murmushi ya ce "To shikenan mu je" suka fita.
Samha ta tashi zaune ta ce "Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa".

"Jikina ya na bani akwai wani abu ɓoyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su"

Fauziyya ta ce "Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye"

Mummy ta ce "Na gani" nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa.

Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya É—an fara É—agawa.

Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sauƙin kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce "To shikenan, ki gaishe mini da takwarana". Ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa"

Ya É—an yi jimm yana kallon rumaisa, "Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir".

"Ki shiga ki É—auko shi, ki kawo shi na ganshi".
Chapter 53 · 0% Book details