← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 124

Sashe 26

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace mai sunan baba ya ce "Wulaƙancin naki da iskancin har ya kai ki din ga yi mana ihu cikin daren nan? Kar ki kuskura ki kaini bango, na kuma jin bakinki sai na zaneki, ki yi addu'a ki kwanta, idan ma kina yi ne saboda ba kya son auren, to kin yi kaɗan"

Mama gaba É—aya jikinta yayi sanyi ta kuma cewa "Me ki gani ya razanaki haka?" Rumaisa ta yi shiru.

Mai sunan baba ya ce "Ba wani abu da ya razanata, shirmenta da take yi ne yake zuwar mata har a mafarki"

Aliyu ya yi tsaki ya ce "Rigimarki ba ta ƙarewa, har tausaya bawan Allah nan nake faman da zai sha" ya fice daga ɗakin, mai sunan baba ma ya fice.

Duk iya rarrashin mama, da lallaɓa yaro a matsayin ta na uwa, ta yi, amma rumaisa ta ƙi gayawa mama ainihin abun da ya faru, haka mama ta ƙyaleta ta sake tayar da salla.

Tsoro ya hana rumaisa ko rufe idonta, dan haka ta tashi ta je ta yi alwala, ta zo ta tayar da salla ita ma, sai dai tana yin raka'a biyu, wani nannauyan bacci ya É—auke ta.
Mama tana jin yadda rumaisa ke ta surutai a baccin, kamar tana hannun Æ´an bindiga.

Sai da mama ta sanyata a gaba tana ta tofa mata adduoi, har mama ta fara tunanin, ko rumaisa na da aljanu ne, maganar aure ta taso za su fara motsawa.
Dan haka ta ƙudurce a ranta, dole ta nema mata maganin sheɗanu.

Ta cigaba da sallolinta, tare da tsananta addu'a a kan lamarin auren nan da yake tunkarosu.

***

Mamaki Samha take ba ɗan kaɗan ba, ganin irin surƙuƙin ƙauyen da suke kurɗawa, ita da Mummy da kuma Hajiya Lubabatu.
Kasa ɓoye mamakin ta yi ta ce "Wai yanzu Mummy har nan ku ke zuwa? Ni fa ma fara jin tsoro"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Yaro yaro ne, ke ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake, tafiya duk nisanta da surƙuƙinta, in dai da biyan buƙata ai shikenan, tafiya ɗazu ce".

Hajiya Lubabatu ta ce "Ke idan babu wannan ƴan biye-biyen mutum ya zauna lafiya, mussaman a irin gidajen sarautar nan, ai ni tun da Allah ya taimakeni, na kaɗa duk wata mata da ta raɓi gidana, na ga tsuguno ba ta ƙare mini ba, sai na dangana da mallakawa Jabir kujerar galadima,"

Samha ta ce "Takawan fa? Ba gidansu sarautar za ta koma ba".

Mummy ta zunguri Hajiya Lubabatu, sannan ta ɗora da cewa "Yauwwa, mun kusa ƙarasawa, daɗinta kowa yake gani, idan muka je sai ya katse ya sauraremu".

Samha ta ce "Ni fa idan za a kasheni, ban san hanyar komawa ainihin titi ba, gaba É—aya kaina ya juye".

Hajiya Lubabatu ta ce "Zaki zama Æ´ar gari ne da zarar kin waye".

A cikin surƙuƙin ƙauye sosai mutumin yake, dan an fita daga gari sosai wurin kamar daji, a nan aka yi masa wani shinge, suka tarar da tarin mata da maza a wurin, da masu zubin hannu da shuni, da masu saffa-saffa, ga marasa lafiya kuma, wasu abun nasu ma dai ba kyawun gani.

Ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba, bayan an sallami na ciki, suka shiga, wurin duk an kafe ƙahuhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, ga wani irin wari da tsamin turaruka da magunguna da ɗakin yake yi. Mutumin yana zaune cikin wasu tsummokaran kaya, ga wasu irin kayan tsubbu a gabansa shi kansa duƙun-duƙun da shi, kamar ba ɗan Adam ba, ga idonsa ɗaya hakiya ta rufe, ɗayan kuma a juye ga idon jawur.
Sai da kan Samha ya sara, ta nemi faɗuwa, Hajiya Lubabatu ta riƙeta suka zauna.

Mummy ta ce "Barka da warhaka malam, ya aiki ya ƙoƙari"

"Lafiya ƙalau, kin yi nusau, ko buƙata ta biya ne, ko kuma dai kin fasa aikin da ki ka buƙata, tun da ki ka ce mana akawai maganin da ake masa amfani da shi, muke jiran ki kawo mana maganin mu yi aiki a kai, amma mun ji ki shiru".

"Ai malam maganin ne yaƙi samuwa, duk wata hanya da zan bi a samu, ba a dace ba, amma ba haƙura na yi ba, ina nan zan dawo. Gamu tare da baƙuwa, ƴar facalarmu ce, da ita da shi yaron Adam, duk iyayensu ƴan uwa ne, ta daɗe tana son shi, amma ya auri ƙanwarta, yanzu ƙanwar ta mutu, amma uwarsa na son aura masa wannan ƴar tsintuwar da na taɓa baka labari, kuma wannan ɗin ta kuma rasawa, shine muke son ayi wani abu a kai".

Yayi shiru, sannan ya ɗebi wata ƙasa ya zuba a wani fai-fai, ya dinga juya hannunsa, sannan ya kalli fai-fan ya ce "Tirƙashi, tabbas ga maganar aure nan, sai dai ita yarinyar tana tafe da wata irin guguwa mai ƙarfin gaske, sai kun tashi tsaye sosai"

Cikin sauri Samha ta ce "Malam so nake kar auren ya yiw....."

"Aure sai an yi shi, ma'aunin ƙaddarar yarinyar da zai aura ya rinjayi tasa, sai dai idan ɗayansu ne ya mutu"

Kamar Samha za ta yi kuka ta ce "Dan Allah malam a kasheta, ba zan iya jurewa ba a wannan karon"

Mummy ta ce "Malam, ka san yarinyar, wadda ka taɓa yi mini aiki a kanta ce shekarun baya, kawai ka yi wani abu a kai"

"To ya aka yi ƙasa ba ta nuna mini ita ce ba? Ban ga taurarinta sun fito a cikin nasa ba, amma duk da haka babu damuwa, ta jiramu a waje, zan bata abun da za ta yi"

Samha ta jinjina masa kai, ta yi godiya, sannan ta tashi ta fita ta bar su Mummy.

Hajiya Lubabatu ta ce "Malam, ya ake ciki ne? Haryanzu galadima yana nan a raye, ga lokaci yana ƙurewa, bana son wani dalili da zai gifta, da Jabir zai gaza mallakar zunzurutun dukiyar nan da sarauta".

"Allah ne mai kashewa da rayawa ba ni ba, dole ki cigaba da jira, ke kuma ya aka yi?" Yayi maganar yana kallon Mummy.

"Malam, kamar aikin da yake tsakanin yaran nan ya fara sanyi, kamar mahamud ya sassauta ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan, sannan malam yadda yake yinƙurin yin auren nan, a sake damalmala lamarinsa, bana ƙaunar ganin wani cigaba a tare da yaran nan".

Malamin ya ce "Ina iya ɓata aiki ne, ba sauya ƙaddarar bawa ba, zan yi abun da ya dace a kai, ku tafi ta kudu, ku ajiye abun sadaka a mararraba ta uku, sannan shekara ta kusa, za a shayar da ƴar baƙa ta arewa da jini, sai dai ta daina samun jinin da take sha, dan haka za ayi mata sadaukarwa da wani abun, na sallameku".

Da haka suka fita, Samha take ce musu bai faÉ—a mata mai za ta bashi na aiki ba, suka ce kar ta damu, suka yi abun da ya ce sannan suka tafi gida.

***
Abubakar ya dawo, sun kuma tattauna sosai a tsakaninsu, a kan auren rumaisa, suka yanke shawarar a sake jarraba sayar da gonarsu, domin a samu abun yi mata kayan É—aki.
Ɓangaren rumaisa kuwa, sai koke-koke take a kan ita fa ba ta so, gashi har fargabar kwanciya bacci take yi, saboda munanan mafarkan da take yi, ta je ta samu malaminsu a islamiyya ta ce ya bata Addu'a, tana yawan yin mugun mafarki ya bata shawara da cewa "A duk lokacin da ki ka yi mummunan mafarki, ki nemi tsari sannan kar ki gayawa kowa, ki din ga kwanciya da alwala, sannan ki kwanta da ɓangaren dama, ya zamana kina Adduoi na safe da na maraice, sannan ki karanta na kwanciya barci, idan razana ki ake yi a mafarkin, ki daina tsorata, ba abun da yake samun bawa sai da iznin Ubangiji, kin riga kin yi azkar kin nemi tsari, babu abun da kuma zai cutar da ke".
Rumaisata riƙe maganar malaminsu, ta dage da addu'a da alwala, shine ta ɗan samu rangwame.

Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, tun da su ammi suka tafi, sai ana gobe kai kuɗi suka yi waya da mama, ranar juma'a bayan an saukko daga Masallacin juma'a, mai girma turaki da wasu manya a masarautar kano, suka kai kuɗin auren rumaisa gidan ƙanin mahaifinsu, naira dubu ɗari biyar, suka saka wata ɗaya rak.

Ƙanin mahaifin rumaisa ya nemi su ƙara musu lokaci, saboda shirin aure, ba abu ne mai sauƙi ba, amma suka ce basa buƙatar komai, rumaisa kawai suke son a kai musu, dan haka wata ɗaya suka saka.

Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
Chapter 26 · 0% Book details