← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 124

Sashe 78

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ya bata labarin yadda rumaisa ta dawo da sabir, da yadda aka yi har ya aure ta, zuwa yanzu da suke tare, da abubuwan da take ta hasaka masa, a zamansu.

Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Well, amma ba ta da kunya gaskiya, a haka ku ke zaune?".

Ya ce "Ya ki ke zagar mini mata ne, zaki shiga sahun Black list É—in mu fa".

"Am serious matarka ba ta da kunya takawa"

Sai ya tuna abun da ya faru jiya, ya ce "Kin san family ɗin mu sai a hankali, gida suka zo suke yi mata rashin mutunci, ta rama. Kin san ƙanwar maza ce ba tsoro. Haka nan muke lallaɓawa muke tare, ake rainonta kan Allah ya sa ta gama hankali, ko me za ta yi, ta cancanci ayi mata uzuri, kuma in kula da ita, abun da ta yi mini, ko duniya na bata ban biyata ba"

"Haka ne, amma ban gane ake lallaɓawa ake rainonta ba, haka ku ke zaune kana kallonta tana kallonka"

Yayi dariya ya ce "Ina ruwanki ne?"

"Babu, amma tun a hotonta nayi mamakin yadda ka auri ƙaramar yarinya haka, na sam baka da ra'ayin auren ƙaramar yarinya, na san plan ɗin ammi ne, ban da haka wannan guda nawa take? Me ta sani?"

"Ai fa, in dai ɓangaren zamantakewar aure ne, ba ta san komai ba, sai kaifin basirar sanya ido da gane mara gaskiya, shiyasa na yi mata registration na islamiyya matan aure, ta ce dai ba zata ba, ita yara zan sakata, ba zata shiga cikin matan aure su rainata ba, wannan kuma da ammi zan bar ta, dan sun fi kusa"

Laila ta ce "Well, tun da ba tare zaku tafi ba, ka bar ta a hannuna, zaka ga canjin kafin ka dawo in sha Allah".

Ya dubi laila ya ce "Like how kenan?".

"Kai ina ruwanka, tun da tafiya zaka yi, ta zo mu zauna a gidan ammi tare, she needs to learn so many things, ko kuma you are taking another wife ne, wannan tayi ƙwaila da yawa".

"Allah ya sa ta ji ki na ce mata ƙwaila, zaku yi faɗa da ita sosai, nikaɗai ne idan na faɗa take ƙyaleni, ni ɗin ma sai da tayi mini abun da na daɗe ina jin kunyar kallon ammi, ta gaya mata wai na ce zan ƙara aure saboda bata da nono"

Rufe baki laila ta yi tana dariya, ta ce "Lallai wannan yarinyar É—anya ce sharaf, ka bar ta a hannuna kawai".

Hira suka cigaba da yi, ya din ga bata labarin abubuwan da suka din ga faruwa, tun bayan komwarta canada daga hutun ƙarshe da ta zo.

Laila ta sha mamakin ganin yadda rumaisa ta kawo mata abinci da ta girka, komai nata tsaf, hatta falonta a gyare yake, dan har ƙamshin turaren wuta yake, a tunaninta ko masu aiki ne suka yi mata, sai da adam ya ce mata ita take abun ta.

"Mimi ina nawa abincin?" Adam yayi maganar yana kallon ta.

"Au, dama zaka ci? Ya ƙare saura ƙanzo, ko in dafa maka taliya da manja da yaji"

Yayi murmushi ya ce "zan kama ki ne, da ke da taliyar.

Rumaisa ta koma ɗakinta, ta bar musu falon, wanka ta yi, ta fito da nufin ta shirya, ta ga takawa a ɗakin nata. Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Ya na ganka kuma, ina baƙuwar?".

"Haka ake yi, kin yi baƙuwa kin tafi kin bar ta?".

"To ba wurinka ta zo ba, ko zuwa zan yi na saka ku a gaba ina kallon bakin ku?".

"To, yanzu dai ba wannan ba, dan ta tafi ma, taho mu yi magana".

Rumaisa ta ce "Taɓ, kaya zan saka, ka je idan na kammala shiryawa, zan zo"

Ya janyo hannunta ya zaunar da ita a kan gadon, ya ce "Yanzu zamu yi, baki da isasshen lokacin cigaba da ganina. Idan na tafi gida zaki koma wurin ammi, zuwa lokacin da zan dawo, lokaci-lokaci kuma, zaki iya zuwa gida, shima sai kin nemi iznina tukuna"

Jiki a sanyaye ta ce "To meyasa ba zan koma gidanmu ba, ni fa ba zaman gidanku ne bana so ba, wannan ƴan rainin hankalin ƴan uwan naka ne ba zan juri wulaƙancinsu ba"

"Rumaisa kin iya cewa bani da haƙuri, ke haƙurin ne da ke? Babu ruwanki da su, gobe in Allah ya kaimu da azahar zamu tafi, idan na kammala wakilicin mai martaba, zan wuce in da zan yi course ɗina na watanni shida. Dan Allah ki nutsu ki zauna lafiya da kowa, ban da rigima, ga Anty Laila nan, zata kula da ke tana da kirki sosai".

"Wannan É—in ce mai kirki, bayan daga zuwan ta ta fara gaya mini magana, dan dai kawai ka ce yayarka ce".

"Dai-dai take da ke ai, idan ki ka yi mata rashin kunya, ta san yadda za ta yi da ke"

"To yanzu idan ka tafi, wa zai cigaba da aikin binciken da kake yi?".

Ya ce "Ga Bashir nan, akwai group É—in mu da duk tare muke yin ayyukanmu, ki sanya ni a cikin addu'ar ki mimi, matsaloli sun yi mini yawa".

Rumaisa ta ce "Allah yana tare da bayinsa masu tawwakali da haƙuri. Allah yana tare da mu papa, zan din ga yi maka in sha Allah"
"Thank you dear" yayi maganar tare da sumbatar hannunta.
Tayi dariya ta ce "Kai, sai ka ce abun indiyawa, kiss a hannu"

"To muyi a baki?" Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ta tashi. Murmushi yayi ya tashi ya bar É—akin.

A ranar takawa ya je ya yi wa mama sallama, ya sanar da ita batun zai bar ruma, a wurin ammi. Cikin kara mama ta nuna bakomai, tare da yi masa fatan alkhairi, sai dai bayan tafiyarsa Æ´an mazan mama, duka din ga mitar, dan me ba zata dawo gida ba, za ta tafi gidan sirikai ta zauna, kamar mara gata.

Ruma ba ta É—auki tafiyar takawa serious ba, sai da ta ga da gaske yana haÉ—a akwatinsa a daren yau.

Tana tsaye ya ce ta miƙo masa wannan, ta ɗaukko masa wancan.

"Papa, ya batun anty iman ne, ba wani abu da zaka yi a kai kan ka tafi? Kar wannan jabir É—in ya aureta fa".

"To ke ina ruwanki?" Yayi maganar yana duba wani turare.

"Da ruwana mana, ni fa na bana son jabir É—in nan".

"Ita ta ce miki ba ta son sa ne? Kin fiye damuwa, ko so ki ke in tayata mu bijirewa ammi?"

Rumaisa ta ce "Wallahi ba ta son sa, taɓ gaba ɗaya kalar munafukai ne jabir ɗin nan, da gani yana aikata wani laifi a ɓoye da Allah yake rufa masa asiri. Ko dan halin babarsa ma dole ya zama shaiɗani".

Ƙurii yayi da ido, yana kallon rumaisa, zuwa yanzu ya daina mamakin abubuwan da take faɗa da aikatawa, dan idan ta faɗa, ko ɗari-bisa ɗari bai zama dai-dai ba, kashi saba'in dai-dai ne.

"To, haka ta ce miki, kin san ba zamu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba, mu cigaba da yi mata Addu'a, idan shi ne alkhairi......

"A'a ba alkhairi bane ba ma, kuma ba zata aure shi ba" ta katse shi.

"Tun da kece waliyyinta ko? Wai ke kin fi ni son ta ne? Kin ƙwace mini ɗa, kin ƙwace mini ammi, kuma ƙanwartawa ma da nake ji da ita, kin ƙwace ta, haka ake rayuwa ne?"

Rumaisa ta ce "Eh É—in, tana da wanda take so yake son ta, amma ba wani jabir"

Takawa ya ce "To wa take so? Dan bani da labari"

"Ban gayawa kowa ba dai, saura ka faÉ—a kaima, mai sunan baba take so, kuma yana sonta shima"

Da sauri takawa ya É—ago ya ce "What?! Umar É—in gidanku?"

"Eh mana".

"Amma iman ba ta da da hankali, ina ita ina wannan yayan naki?".

Rumaisa ta haÉ—e rai ta ce "Saboda talaka ne ko?".

Shi ma ya É—an tsuke fuska ya ce "Bana son bahaguwar fassara. Amma kin san halinsa dai sai dai ki gayawa wani, iman kuma is very simple and cool, ta yaya?"

Rumaisa ta ce"Ta yadda aka yi ka aureni, kai ba ruwanka, sai dai idan saboda talaka ne ba zaku ba shi ba, yaya umar bai taɓa damuwa da halin da wani yake ciki ba, ko zai shekara dubu bai ga mutum ba, in dai ba mama ba ce ko ni, ba ruwansa, amma zuwan da muka yi ya ce mini ina ƙanwar mijinki, to dan Allah ba soyayya ba ce haka? Ai kai dai ka san soyyaya ko, ka san ya ake ji?".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ke baki santa ba?"

"Ina na sani, ni fa sau ɗaya wani ya taɓa cewa yana sona, su yaya Aliyu suka ce, idan suka ƙara ganinsa, sai sun zane shi. To sam ban san ya soyayyar take ba, in ta so in ga ina zance".

Ya kwashe da dariya, rumaisa ba ta rabo da wauta.

"Ni ba daga zuwa zance, ki ka haɗa kayan zancen ki ka cinye ba, ki ka faɗo jikina, ki ka sani neman kalaman kariya. To yanzu tun da baki taɓa saurayi ba, zan zama saurayinki, mu gani, idan na tafi sai mu din ga waya, irin na saurayi da budurwa".

"Eh ayi haka, Allah ya sa na ji ya soyayya take, in din ga yi maka waƙoƙin soyayya, irin na Indiya"

Dungure mata kai adam yayi yana dariya, ya ce you won't kill me.

"Papa ni fa da, mai sunan baba wani tsoho zai aura mini a unguwar mu, malam ladan, mutumin nan ya taɓa zaneni da carbi, wai daga na tambayi mama wani abu, wai sai yayi mini aure, ya sai mini tabarma da buta. Wai ko a aura mini wani Ɗan ladi mai kan sirdi, kansa kamar plate, ka ga baƙinsa Astagfirullah, tsoro yake bani, gashi ɗan ƙarami, shi ba wada ba gashi nan dai, wata ƴar ajinmu ta ce wai saɓo yayi Allah ya mayar da shi biri, da ya tuba, sai ya koma haka"

Takawa zai iya cewa rabonsa da dariya irin ta yau, tun kan aisha ta tafi Saudiyya, dan ruma labarai ta din ga bashi irin na ta'asar da ta din ga tafkawa.
Chapter 78 · 0% Book details