Sashe 83
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Usman ya yi ƙuri da ido yana kallonta.
"Yaya usy ba ka ce komai ba?"
"Ji nake kamar in kama ki in maƙure mini wuya ne".
Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri"
"Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya ɗauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ƙiri-ƙiri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taɓa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali"
"Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba"
Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?"
"Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ƙona ni idan na yi"
"Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ƙara auren, kuma ba abun da zai hanamu raƙashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen ɗin.
Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.
Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haÉ—a shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.
Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya É—auke ta, ta bashi adress É—in gidan.
Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.
Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.
Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi"
"Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba"
Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taɓa masa kayan zane, wataran ranƙwashina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai"
Ya ce "Lallai team ɗin nan an haɗa manyan ƙwari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya ɗau ruma suka tafi gida.
Aikuwa ta sha faÉ—a a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji É—in nan.
Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.
Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a É—aki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.
Abu É—aya ne yake yi mata daÉ—i, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daÉ—in haka.
Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.
Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.
Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaɓe, sai taɓara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.
Rumaisa har leƙawa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'Taɓ sukumbiya, wai baby taɓ' laila tana jin ta, taƙi kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.
Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta ɗau kwalliya kamar zata biki, ta sha ƙanan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.
Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni Æ´ar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?"
Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.
Da safe kan ta tafi makaranta, ta karɓi wayar iman, ta kira Adam voice call.
"Budurwata"
"Papa" ta kira sunansa a shagwaɓe.
"Ya aka yi?"
"Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faÉ—a, duk ta bi ta saka mini ido".
Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ƙara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata".
"Yi haƙuri ya kake?".
"Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba"
"In ji wa? To yau saura kwana É—ari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo"
Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara"
"Ni kar ka kashe"
"So ki ke ki makara a school ko?"
"Hmm ka san me?" "A'a sai kin faÉ—a"
Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.
Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?".
"A'a"
"To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima"
Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so".
Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa"
Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun"
Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi".
Da ƙyar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi.
Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta.
Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya ɗau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats ɗin su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online ɗin ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ƙaramin ƙular da shi yake yi ba.
Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma taƙi yarda su sake ɗaukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ƙarƙashin ƙasa kuwa, tana cigaba da shirin, sake rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai baƙin ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta.
Æangaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani.
Baba uwani ma kullum zaman É—ar-É—ar take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta.
Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haÉ—a lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna.
Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ƙi daɗi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faɗa ba.
Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya taƙi magana, Nusaiba kuwa sai zaƙalƙalewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance.
Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo.
Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karɓeta.
Sai dai ta turɓune fuska ta ce "Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah"
Ammi ta ce "To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?"