Sashe 93
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta ce "Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi ɗa na kowa ne, yadda hajiya binta ke riƙe da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaɗai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ƙaunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaɗan".
Abubakar ya ce "Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ƙanwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la'akari da yadda mutum ya faɗa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan ɗin sa, zan yi magana da su baffa, a ɗaga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ƙarasa nasa".
Mai sunan baba ya galla masa harara.
Abdallah ya ce "Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yinƙura abu namu maganin a kwaɓe mu".
Yasir ya yi murmushi ya ce "Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah"
Huzaifa ya ce "Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal É—in da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa".
"Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni
zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir ɗin ɗinki, banda shegiyar ƙarya da saɓa alƙawari".
Mama ta ce "To zakaru, ai kun ci kun ƙoshi, dole ku yi mini faɗa".
Umar ya ce "Duk na ji ta bakin ku, na kuma gode sosai, amma babu wanda zai rabu da wani abun sa saboda ni, kai habu ba za a ɗaga bikinka ba in sha Allah, ina fatan nima wannan ɗin ba zai gagara ba, zan ƙara ƙoƙari".
Abubakar ya ce "Wai dan an haife mu lokaci ɗaya ni sa'anka ne? Bana magana biyu kai ka sani, gidan nan ya zama naka, dama kaine ƙarfin ginin, ni ba gaggawa nake yi ba, ita ma haka in sha Allah ita da iyayenta za su fahimce ni".
Mai sunan baba zai sake magana mama ta ce "Ka riga ka ɗaukki aiki babana, idan ba hakan aka yi ba, ni ban ga mafita ba, garbatina ɗan albarka, Ubangiji Allah ya ƙara haɗa mini kanku, ya kau da abun ƙi a tsakanin ku, a duk lokacin da abu ya tasowa ɗayanku, na ga kun haɗa kanku, ba ƙaramin daɗi nake ji ba".
Usman da tun da ake maganar bai ce komai ba sai yanzu ya ce "Mama duk jajircewarki ce ta kawo haka, Allah dai ya ƙara miki lafiya da nisan kwana".
Suka amsa da Amin, Abdallah ya ce "Mai sunan baba, idan abu ya taso maka, bamu yi maka ba, wa zamu yi wa? Sadaukarwar da kake yi domin farincikinmu ai tana da yawa, komai ka samu mu, kai ne wa, kuma kai ne uba, kowa ya kwaso matsalar sa, mai sunan baba, dan haka muna bayanka a kowane ƙadami Allah ya iya maka yayi riƙo da hannunka".
Karar da ƴan uwan nasa suka nuna masa, ba ƙaramin daɗi tayi masa ba, har sai da hakan ya sanya shi murmushi, kuma ya kasa ɓoye farin cikinsa.
***
Ko da labari ya iske dangin mahaifinsu Umar, sun yi murna, tare da tsokanar mai sunan baba, dama zai iya yin budurwa yayi soyayya.
Wan mahaifinsu ya ce zasu yi ƙoƙari, amma abubakar ma ba za a ɗaga aurensa ba.
Sai dai yayan mahaifinsu ya jinjina lamarin auro Æ´ar gidan sarauta yana talaka.
Tare da shi da umar, da yaya Abubakar da ƙanin mahaifinsu, sai mijin iya baffa musa da ya zo daga, suka je gidan turaki bisa jagorancin Mahmud kamar yadda ya buƙata.
Sai dai sun ga karramawa, da mutuntawa da basu taɓa tunani ba, turaki ya ƙara jaddadawa mai sunan baba matsayin iman, mai sunan baba ya ce ya amince.
Turaki ya tambayi Æ´an uwan mahaifinsa, a kan idan sun amince su ma, suka ce ai shi ne zai zauna da ita, kuma tun da ya ce ya ji ya gani, suma sun amince ai É—a na kowa ne, a tarbiyyar da umar yake da ita, sun san ba zai kawo abun da zai cutar da shi ba.
Baffa Musa wa ga mahaifinsu ya ce "Sai dai mu ma wani hanzari ba gudu ba, yaron nan maraya ne, bashi da ƙarfi saka biki nan da watanni uku yayi kusa da yawa, ga ɗan uwansa nasa bikin muke hari, muna fatan a ƙara mana ya zama watanni shida, gaba ɗaya ya mayar da hankali ne a kan auren ɗan uwansa bamu zaci nasan zai zo haka ba".
Turaki ya ce "Babu laifi, kar ku damu. Ubangiji Allah ya yi mana jagora, kuma a hakan nan ma kawai, na yaba da tagwayen sosai, ba dan ance shi ma É—an uwan aure zai yi ba, ai da sai na bashi Æ´a ta, ai duk wani wanda ya fito daga tsatson Æ´a ta rumaisa, duk abun da yake so, in dai ina da shi zan yi masa.
Allah ya sanya musu albarka, ya nuna mana lokacin lafiya".
Baffa musa ya ce "Amin, ranka ya daÉ—e tun da har an samu daidaito, ina ga ba sai mun ja lokaci ba kawo kuÉ—in aure, ga kuÉ—i mun taho da su"
Gaba É—aya suka kalleshi, su dai sun san ba su yi haka da shi ba.
Ya karkace ya ciro kuÉ—i, dubu É—ari da hamsin, ya ajiye a gaban turaki.
Turaki ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya albarka, to ba dan ba a shirya ba, ai da sai a É—aura, mu bashi gidan zama, a wuce wurin ko malam umar?".
Mai sunan baba ya risuna ya ce "Ranka ya daɗe ni yakamata na yi ƙoƙarin samar da mahalli".
Yayi murmushi ya ce "Babu laifi, Allah ya nuna mana"
Ko da suka taho hanya, Mahmud har gida ya kai su mai sunan baba, a gida suka sanar da mama ai an bayar da kuÉ—in auren ma, mama ta ce daga zuwa tambaya an biya kuÉ—in aure? Ta ce to sai a nemo kuÉ—in malam musa a bashi abun sa, amma ya hau mama da faÉ—a, a kan dan yayi wa Æ´aÆ´an É—an uwansa abu, dan me za ta ce a biya shi.
Turaki ma wayar ammi ya kira, ya sanar mata su mai sunan baba sun bayar da kuÉ—in auren iman, dubu É—ari da hamsin, sun sanya watanni shida dai-dai.
Ammi ta yi mamaki, dan ita bata ta;a zaton abun a haka ba, ta ce to ba a basu komai na tukici ba, sun kawo kuÉ—in aure.
Turaki ya ce su aika musu daga baya, amma sun zo da kuÉ—in aurensu sun bayar.
Farincikin ammi ya kasa ɓoyuwa, ta nufi ɗakin laila, da suke tare da rumaisa, tana ta koya mata abubuwa.
"Laila, rumaisa" suka É—ago suka kalli ammi.
"Daga zuwa amsa kiran turaki, sun bayar da kuÉ—in auren iman, an saka watanni shida".
Ruma tayi murmushi ganin yadda bakin ammi yaƙi rufuwa.
"Au shine aka wareni, ban ma san za a kawo kuɗin aure ba, iman yanzu ta rama ta ƙwace mini yaya, dan na auri takawa"
Suka yi dariya, laila ta ce "Kaii Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu. Ni dai gayen ya burgeni ranar da na taɓa ganinsa, so gentle".
Ruma ta ce "Taɓ, mai sunan baban ne gaye".
Ammi ta ce "Ya Ubangiji Allah ka sanya ƙarshen matsalar nan ne ya zo, Allah ya sa kar a gaya masa wani abu da zai saka ya ce ya fasa".
Ruma ta ce "Ammi, idan kin ga ba ayi auren nan ba, sai ƙudirar Allah. Mai sunan baba ba zai taɓa cewa zai fasa ba, sai idan ku kuka fasa auren, duk rintsi kuwa"
Ammi ta ce "Allah ya sa, bari ta dawo na gaya mata, Allah sarki ƴar marainiyata, Allah ya kaɗe abun ƙi".
Ƙasan zuciyar ammi, tana ta yi wa iman addu'a Allah ya sa ta dace, dan yanayin nature mai sunan baba, tana bata tsoro, gani take kamar yanayin iman ya nuna tana son shi ba kaɗan ba.
Da labari ya iske iman, da ta koma É—akinta sai da tayi sujudu shukur, sujjadar godiya ga Allah, saboda tsananin farinciki, haka nan a ranta take jin, sassauci zai samu a rayuwarta.
A irin kyan da Allah ya yi wa iman, zaka raina abun da aka bayar na kuÉ—in aurenta, amma jiki na rawa ta kira mai sunan baba.
Sai da ta kusa katsewa sannan ya É—aga.
"Yaya umar"
"Na'am".
"Ashe kuÉ—in auren zaku kai, na zata kawai zuwa kayi ka amsa kiran da mai girma turaki yayi maka?".
"Na yi garaje ko, na kai kuÉ—in auren ba tare da kim ce mini kin amince ko a'a ba. Tun da rumaisa ta ce mini, akwai wanda ki ke so".
Iman a ranta ta ce 'Kai É—in ne dai, kai nake so yaya umar'.
A zahiri ta ce "Ni ba wanda nake so fa"
Har cikin kansa ya ji shagwaɓar da tayi masa, ya sake gyara zaman wayar sannan ya ce "To ya aka yi?"
"Bugowa na yi, na maka ya ka je gida, Allah ya ƙara buɗi".
"Masha Allah, ayi haƙuri abun talaka na san kin fi ƙarfin hakan"
Iman ta ce "A'a ban fi ƙarfin haka ba, Allah ya yassare maka".
"Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, thanks" ya katse wayar.