Sashe 75
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina sake roƙonki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daɗi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taɓa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake" ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita.
Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta.
Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba ɗaya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daɓas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta.
"Lallai wannan uwani an yi Æ´ar........, ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?"
Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani.
Baba uwani ta fara koÉ—ata, ta ce "Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?".
"Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba"
"Ƙarya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ƙullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri".
Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce "Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ƙoƙarina dan Allah kiyi haƙuri".
Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba É—aya ta gigice.
Ruƙayya ta shigo ɗakin, tana duban Mummy ta ce "Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?"
"Bakomai, jeki hutawa zan yi" Ruƙayya ta ɗage kafaɗa ta fice.
Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi.
Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa.
"Ammi sannu da gida"
Ammi ta ce "Yauwwa Æ´ar auta ta, ina ya baro mini ke ya shigo shikaÉ—ai? Ai ban san tare ku ka zo ba"
Ta zauna ta ja yatsan takawa da ƙarfi ta ce "Tafiya yayi ya barni".
"Ke baki san da zafi bane" ruma ta harare shi ta ce "To waye ya ce ka tafi ka bar ni?" Ta mayar da idonta kan Ammi ta ce "Ammi ina Anty Iman ne?".
Ammi ta ce "Kin san ta sarkin É—aki, tana can ko tana bacci ko tana karatu".
Rumaisa ta tashi ta nufi É—akin Iman, Sabir ya biyota, ta tsaya ta É—auke shi suka tafi tare.
Ammi ta ce "Yaya ake ciki, ai yanzu rigimar ta ta da sauƙi ko? Kuna sabawa a hankali na ga ta rage daru sosai".
Yayi murmushi ya ce "Ba zata sauya hali ba, kawai na koyi zama da ita ne kawai. She's simple at times wasu lokutan kuma ba a gane kanta"
Ammi ta yi dariya ta ce "Tun da ka iya zama da ita ai Alhamdilillah, Allah ya ƙara haɗa kanku"
Ya ce "Amin, sai dai Ammi akwai wani abu".
"To, Allah ya sa ba matsala ba ce"
"Ba matsala ba ce ba, ta ce zata gaya wa mummy abun da zai saka a fasa kirana wurin mai martaba, ban san me ta ce mata ba"
Ammi ta ce "Wai yanzu daga can take?"
Ya ce "Eh".
"Takawa meyasa ka barta? Idan kuma ta je sake hargitsa lamuran fa?".
"Ammi, am testing her thinking capacity, tama Sharp brain fiye da tunani, kuma na fara yadda da abun da ta gaya mini a kan Jamil, idan har tayi nasarar sanya Mummy, ta janye ƙarata data kai wurin su mai girma wambai, duk abubuwan da rumaisa take faɗa gaskiya ne".
Ammi ta numfasa ta ce "Takawa, kaifin basirar yarinyar da tarbiyyarta, su ne suka saka na zaɓa maka ita, ni na san tana da kaifin tunani tun kan ku yi aure, tana da basira. Dan haka a ƙara haƙuri, ka bi komai a hankali, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa kafin ka yi tafiyar nan, abun da hali zai yi"
"To shikenan Ammi, in sha Allah".
Ammi ta ce "Amma zan so sanin me za ta gaya wa Jamila, da har zai sanya ta janye abun da ta je ta faÉ—a".
Takawa ya ce "Nima na so sani taƙi faɗa, kuma mun yi da ita ba zan gayawa kowa ba. Idan na cigaba da matsa mata ba zata faɗa ba".
"To Ubangiji Allah ya iya mana, ya sanya ita ce sanadiyyar warwarewar matsalolin nan"
"Amin Ammi".
Ruma kuwa a kwance a ƙasa ta tarar da iman, a ɗan razane ta ƙarasa ta taɓa jikinta, ta ji yayi ɗumi.
"Anty iman, lafiya ko baki da lafiya ne? Ciwon kan ne ya dawo?x ta jero mata tambayoyin.
Iman ta tashi zaune, tare da yin yaƙe ta ce "Maman sabir, saukar yaushe?"
"Ba wani saukar yaushe, baki da lafiya ne?".
"A'a lafiyata ƙalau, kawai dai kwanciya nayi".
Rumaisa ta zaune sosai ta ce "Ke da papa wasu lokutan halinku ɗaya ma, idan ba rashin lafiya ba, akwai damuwa fuskarki ta nuna, dan Allah anty iman menene, bana son in ga damuwa a fuskarki, gaba ɗaya raina ɓaci yake yi. Ko wani ne yayi miki wani abun? zan iya rama miki".
Cikin dauriya, Iman ta ce "Maman sabir, bana son ɓacin ranki nima, kasancewarki a tare da ni, yana bani ƙwarin gwiwa.
Zan gaya miki menene, amma dan Allah kar ki bari ammi ta sani, kin san bana son damuwarta".
"Anty iman, duk surutun nan nawa, ina ɓoye sirri, gaya mini ko bani da maganin zan tayaki da addu'a".
"Ammi ce ta ce mini, wai uncle J yayi mata maganar yana so na, wai zai je ya sanar da mai girma turaki, a zo a nema masa aurena, naga ammi tana murna, amma....." Sai kuma tayi shiru.
Rumaisa ta ce "Amma ke ba kya son sa ko?"
Iman ta zubawa rumaisa ido.
"To wa ki ke so, dan ni ma bana son wannan jabir É—in, babarsa ba ta da mutunci, wahalar da ke zata din ga yi"
"Ba na son kowa maman sabir, bana son sake yin Soyayya, na barwa Allah lamarina, amma wallahi bana son jabir".
"Kin tabattar babu wanda ki ke so, tuna dai" ruma ta yi maganar tana basarwa.
Sai da gaban iman ya faÉ—i, tayi fatan, Allah ya sa ba ganota rumaisa ta yi ba.
"Na tabattar bana son kowa ni yanzu"
"Amma ya san ba kya son sa ya nace, kar ki damu ki yi ta addu'a, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, ba bari za ta yi ba. Ko kina son wani a yayyena, amma su talakawa ne?"
Iman kallon rumaisa take yi, tana son gano gaskiya, ko dai ruma ta gano ta ne. Ganin sun gaza haÉ—a ido, ya sanya ta ce "Kin manta nima talaka ce, Æ´ar fulanin tashi da aka tsinta a dokar daji, ai mutane masu asali kamar yayyenk......"
"Iman bana son wannan maganar wallahi, raina ɓaci yake idan kina gayawa kanki haka"
"Shikenan na daina".
Ruma ta ce "Da dai yafi, yauwwa da muka je gida ranar, mai sunan baba ya tamabayeni kina ina? Na ce masa kina nan ƙalau"
Murmushi ne ya bayyana a fuskar iman ta ce "Allah sarki yaya umar" ruma murmushi kawai tayi, dan tuni ta harbo jirginsu.
"Kar ki damu anty iman, ba zan gayawa ammi ba kya son sa ba, amma in sha Allah ba za ki aure shi ba, dan nima haushin sa nake ji. Bari na je wurin papa" ta tashi ta koma falo, ta tarar ammi ta tashi.
Ta je ta zauna a kusa da adam, ta yi ƙasa da murya ta ce "Done, na gama aiki, ka zuba ido ka gani".
Adam ya ce "Amma baki gaya mini me ki ka ce mata ba".
"Zan gaya maka, amma sai ta fasa É—in tukuna"
Ya ce "Shikenan, mu tafi ne, kin gama?"
Ta ce "A'a sai da daddare"
"Aliyu ya kirani, ya ce mini mama ta za ta yo miki aike, wannan yayan naki mara fara'a zai zo"
Ruma ta ce "Da mai sunan baba ka ke ko?"
"To waye mara fara'a idan ba shi ba"
"Hmmm, ai kusan halinku É—aya, ina kallonku fa ko magana ba kwa yi, kowa yana ji da kansa ko, zan gani dai "
"Ke waye ya ce miki bama ma magana"
Ta kai bakinta kunnensa, ta kare da hannunta ta ce "Ina kallon duk abun da ku ke yi fa, idan ku ga juna ku wani din ga basarwa, shiyasa duk na iya zama da ku, amma gara kai ka fi sauƙin kai wataran, kai baka sakani punishment kamar mai sunan baba, tsakar dare zai sani kneeldown idan na yi laifi fa".
Dariya Adam yake, hannu É—aya yana danna wayarsa.
"Banbancinku, shi bai fiye magana ba, kai kuma idan ka ga dama, kana magana, wasu lokutan kana da wasa kamar yaya usy, jin kai kamar da son girma kamar yaya Aliyu, wataran sauƙin kai kamar yaya Abubakar, idan nayi wani laifin sai na zata zaka dakeni ne, amma sai na ga ka mini banza. Shiyasa wataran nake jin kunyar yi maka rashin kunya".
"Ashe kina sane ki ke duk abun da ki ke mini".
"Mama ta ce hali zanen dutse, ai ka ga bana tsokanarka sosai, kuma zuwa yanzu ba shiryu ba dan Allah, a makaranta fa ko ƙawaye bani da su, saboda kar a ɓata mini rai, a kawo maka ƙarata, bana son ka din ga ɓacin rai sosai, tausayinka nake ji" jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli rumaisa, har cikin zuciyarta, take maganar.