← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 124

Sashe 111

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba uwani bayan ta fita cikin kuka, ta kira Mummy ta sanar da ita halin da ake ciki, wanda hakan ya faru a dalilin ritsa Mummy da yayi suna waya da baba uwani, dan sai da suka samu saɓani ma.
Babu kunya Mummy ta ce "Ba abun da za ta iya yi mata, sakacinta ne ya janyo mata"

Baba uwani ta sha mamaki, ba ta taɓa tunanin abun da Mummy zata gaya mata kenan ba.

Sannu a hankali rumaisa ciki ke tasawa, tayi ta ɓoye-ɓoye, gashi yau da lafiya gobe babu, haka nan take zuwa makaranta.
Ga koke-koken ba gaira ba dalili, wai ita rasa abun da yake yi mata daÉ—i.
Sai dai takawa yayi ta rarrashin ta, ya san ƙuruciya ce da rashin sabo.

Iman kuwa kusan awanni kaɗan sai sun yi waya da mai sunan baba, idan ta maƙale a kan waya, har mantawa Ammi take yi da ita.

Ammi ta ce "Iman dan Allah ki ƙyale yaron nan yayi aikinsa mana, maƙal-maƙal a kan waya ko gajiya ba kwa yi ne?"

Rufe fuska tayi tana murmushi, dan kuwa ba ta yi zaton ammi ta É—agota da yawan wayar nan ba.

Ɓangaren mai sunan baba, yanayin aikinsa yayi masa daɗi, sai dai kewar gida da yake yi sosai, sannan ya fuskanci akwai tarin kitimurmura da rashawa a aikin.
Sai dai yadda yake umar É—in sa bai canza ba, ba ruwansa da kowa aikinsa ne kawai ya dame shi.

Sallama aka yi a office ɗin sa, ya amsa tare da kallon ƙofar.

Wani babban mutum ne ya shigo, fari sol da shi, cikin manyan kayansa.

Mai sunan baba ya yi masa ƙuri da ido, ya ƙaraso ya zauna suka yi musabuha da mai sunan baba.

Ya ce "Namu ne ka na jin hausa ko da turanci zan yi" yayi maganar cikin guɓatacciyar hausarsa ta cikakken bafulatani"

Mai sunan baba yayi murmushi ya ce "Ina kama da bayerabe ne?"

"To ai abun naku ne, wasu lokutan ba a banbance ku hausawa".

"Eh amma irin naku da kun ga junanku ku ke ganewa"

Mutumin yayi dariya, duk da yau ya fara ganin mai sunan baba, kamalarsa ta burge shi.

Ya ce "Masha Allah ya aiki?"

"Aiki Alhamdilillah"

"To da dai ba kai nake tararwa a office É—in nan ba".

"Eh, sabon ma'aikaci ne ni"

Ya ce "Yauwwa ni fa in ce. Kayana ne nake ta sintiri ayi mini clearance, amma bayan gama biyan duk wani haraji sai wani hanya-hanya ake yi mini, ana dai nuna mini sai na bayar da cin hanci, sai dai ba dan babu kuÉ—in ba, bayarwa ne ba zan yi ba. Tun da na san kayana ba na laifi bane"

Ikon Allah mai sunan baba yake gani, hatta yadda mutumin yake kallonsa, tamkar iman ce a zaune a gabansa.

Ya ce "Wasu irin kaya ne? Fanta ne, buredi da ƙosai ne ko kuma shanu"

Mutumin ya sake yin dariya ya ce "Ka fa dame ni fa, ko dai babarbare ne?"

Cikin murmushin sa na ƙasaita ya ce "Ba ɗaya, mai ɗakina ce bafulatana, ai ni akwai amana a tsakaninmu"

"Ahhh ashe ma sirikinmu ne, ina fatan ka bayar da nagge 100, kafin a baka" yayi maganar yana ciro wayarsa daga aljihu da take ringing.

Ya cewa mai sunan baba "Afuwan dan Allah"

Ya kara wayar a kunnensa, yana magana da fulatanci, mai sunan baba yana fahimtar wani abun, sai dai ya ji yana cewa Ade a cikin maganarsa.

Ya gama wayar ya girgiza kai ya ce "Ade na da damuwa. Wai mahaifiyata na ɗaukko daga garinmu, na dawo da ita nan Lagos gabana, na din ga ganinta. Ni da matata fa ƴan uwa ne, kuma akwai wasu ƴan uwana da na ɗaukko duk muke zaune tare. Amma ta saka an kirani a waya, wai na rabota da danginta na zo na ajiyeta a nan, ita tunanin shanunta da awakinta ma take yi. Ace Allah ya yi mini rufin asiri, amma uwata na ƙauye ai lamari ya ɓaci"

Mai sunan baba ba wai dan halayyarsa ce sakin jiki hira da mutane ba, sai dan son cigaba da kallon ƘUDURAR ALLAH (Kar ku manta da sabon littafin NAZEEFA SABO NASHE, da tuni ya fara zuwar muku, kar ku yi ƙasa a gwiwa wurin bin wannan ƙayattacen littafin)
Mutum mai matukar kama da matarsa, ya fara tambayar kansa anya mutumin ba shi da alaƙa da Iman ɗin sa.

Hira suka ɗan yi da mutumin, yana bashi labarin rigimar Ade, kuma ya ke gaya masa akwai mataimakin shugaban ƙungiyar fulani ta ƙasa a familynsu, Ade Allah ya yi wa iyalanta rufin asiri, amma ita ta dage sai zaman ƙauye.
Mai sunan baba ya bashi labarin, shi nasu gidan, da Æ´an uwansa, tare da tattaunawa a kan jajircewar iyaye mata idan aka mutu aka bar su da yara.

Haka suka din ga hira, daga baya suka yi exchange É—in numbern waya, mai sunan baba ya ce zai sake duba maganar kayan na sa.

***
Ƴan kwanakin nan, Mummy tana ta fama da ciwon kai, ta je asibiti an yi mata teses amma bai daina ba, ko san haske ba ta yi sosai.

A hankali kuma Allah ya taimaketa ya fara sauka, shiryawa tayi zata fita, tana son yin waya, amma tata ba network, dan haka ta karɓi wayar ruƙayya ta saka lambar wayar da zata kira, ta yi wayarta.

Sai dai bayan kammala wayar, ta ga saƙo ya shigo wayar ruƙayya daga Jabir.

"Wallahi ruƙayya idan ba ki zo kin same ni ba, mun cigaba daga in da muka tsaya ba, zan watsa videos ɗinki, duniya kowa ya gani, and i mean it"

Bakin Mummy ne ya fara rawa, ƙafafuwan ta suka nemi gaza ɗaukar gangar jikinta, cikin tsananin tashin hankali da mamki, ta dawo falo in da ruƙayya ke kallo. Fauziyya na chatting.

Tana zuwa ta jefa nata mata wayar, ta ce "Me wannan saƙon yake nufi?"

Gaban ruƙayya ya faɗi, ta ɗauki wayar, ta karanta, a take ta fara kuka tana girgiza wa Mummy kai.

"Ki gaya mini me saƙon nan yake nufi?"

"Mummy zan yi miki bayani dan Allah"

Danneta mummy ta yi tana hargagi ta ce "Ni zaki tonawa asiri ruƙayya, wace irin alaƙa ce a tsakanin ki da Jabir? Wallahi gara na kashe ki, na kashe banza, akuya ce ke? Da ke za a haɗa kai a janyo mini abun faɗa? Ni Lubabatu da Jabir za su haɗa kai su cuta? Ni?" Da ƙyar Fauziyya ta janye Mummy daga kan ruƙayya da tuni numfashinta ya fara sama-sama.

Ruma ce zaune daga ita sai mini skirt da brezia, domin kuwa kayan ma ita yanzu damunta suke yi.

Ta ƙurawa Adam ido, "Ya dai babyna, jikin ne?"

"To jiki ai sai Alhamdilillah, papa baka gano smoke É—in ba haryanzu?"

"Mimi da na gano, ai da na gaya miki, bashir suna nan suna bincike a kan al'amarin, kuma an gano wurin da ki ka ce ana É—ibar ma'adanai, mun yi magana da hukumar mu ta katsina ana targeting wurin, kama su ake son yi red handed kamar yadda na gaya miki"

"Papa, na san na yi maka laifi, tun haÉ—uwarmu yakamata ka san komai, amma na din ga yi maka wasa da hankali. Ka san dalili?"

Ya ce "A'a"

"A wannan lokacin da ka san komai, zaka yi aiki da zuciya ne, zaka iya ɓata aikin, saboda kana kan jin raɗaɗin abun da ya faru.
Anty Aisha ta bani labarin komai, wanene kai, abubuwan da suka faru a rayuwarta da taka, rashin jituwaku tsakaninka da Mahmud, sannan a ƙarshe ta roƙi da na auri mijinta, saboda tana ji a jikinta zan iya taimakonka, idan har zan rayu a tsakanin ƴan bindigar daji marasa imani da tausayi, in zauna a cikinsu da baƙin taurin kai, har na din ga abun da nake so wasu lokutan, su ƙyaleni, to lallai zan iya tanƙwara zuciyarka da koya maka haƙuri da sassauta fushinka.
Na tubure na ce ni fa ba zan aureka ba, dan ba ka yi mini ba, mussaman da ba ma jituwa, amma ta cigaba da yi miki magiya, tare da roƙon in taimaki rayuwar mijinta, ita tayi iya nata ƙoƙarin ta kasa".

Rumaisa ta É—an yi shiru sannan ta ce masa "Lokacin da anty aisha za ta mutu, ta cigaba da nanata mini, ta bar mini jaririn ta, kuma ta bar mini mijinta, dan Allah kar in bari Æ´ar uwatta ta aureka, kuma in tabattar an samu daidaito tsakanin ka da É—an uwanka, domin samun farincikin ammi.

Papa, wakili na da saka hannu a yin garkuwa da anty aisha, dan Æ´an bindiga sun ambaci sunansa, cikin dare suna zaton duk mun yi bacci".

Ƙirjinsa ya buga da saurin gaske ya kalleta.

"Amanarka na karɓo papa, shiyasa nake iya ƙoƙarina da zuciyata da jikina domin baka kariya, da tabattar da cika alƙawarin da na yi wa anty aisha. Ina neman afuwarka bisa wahalar da kai da na din ga yi, but Alhamdilillah atleast na cika wasu daga cikin alwashin da na yi"

Shiru yayi ya sunkuyar da kai, ya kasa cewa komai.

Rumaisa ta É—ago kansa ta ce "Papa fushi ka yi?"

Cikin tsananin ƙarfin hali, da hawayen idonsa ya kasa ɓoye damuwar, ya ce "Mimi ba ki yi mini komai ba, ni ya cancanci na yi miki godiya mimi, ban san da wasu kalaman zan yi amfani ba ma" yayi maganar yana kwanciya a jikin ta.

Ta kalli hannunta da hawayen sa yake É—iga a kan hannunta, ta saka hannu tana share masa hawayen, tare da shafa sumar kansa.

"Mimi ba kya so na? Saboda alƙawarin aisha kawai ki ke tare da ni?"

"To ai ban san me zan ji idan ina son ka ba"

Yayi murmushi ya ce "Shikenan, but i already fall for you, ni ina son ki sosai rumaisa i love you, and i will surely keep loving you, to my last breath. Ina son ki rumaisa".
Ji ta yi tsigar jikinta na tashi, kalamansa na ratsa ko ina na jikinta, har wani lumshe ido take yi saboda daÉ—in kalamansa.
Chapter 111 · 0% Book details