Sashe 61
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ina ruwana. ka ci abinci ne?"
Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni".
Ɗan shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ƙarya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar shaƙuwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taɓa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.
Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sauƙi jikin?"
"Eh, Alhamdilillah"
"To sannu, ka tashi mu tafi gida"
Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba"
Miƙewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.
"Kuma duk mai kula mijin wata, É—an wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin É—aga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ƙwafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta ɗora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.
Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani"
Bai ce uffan ba, ya ƙara lafewa, yana sauke numfashi.
Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.
"Ita ma haka ka yi mata ko?"
"Ita wa?"
"Wannan matar da ta fita yanzu".
"Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai.
Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa"
Yayi Æ´ar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi".
Ya kalleta ya ce "Wani alƙawarin ki ka yi wa fulani?"
Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faɗa ba. Kuma gaskiya ka ɗagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini ɗazu, ƙasusuwana sai ciwo suke yi".
Bai É—agata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.
***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana ɓata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ƴar uwata, ni da a tunanina, na lallaɓata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?"
Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ƙi magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi".
"Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?"
Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi"
"Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma shaƙe mutane yake yi".
Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.
Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.
Can kuma ta ce "Tashi, in É—auko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki".
Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba"
"Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami".
"Mimi"
"Na'am basarake"
"Meyasa ki ka faÉ—i maganar É—azu?"
Ta É—an yi jimm, sannan ta ce "Wacce?".
"A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?".
Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ƙarya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba ɗaya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....."
Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta ɗaure ni tamau da sarƙa, ko ta din ga dukana da sarƙar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taɓa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?"
Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya ɓaci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da ɗan kirki kaɗan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo"
Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?".
"Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ƙara girma na auri Yaya Mahmud" ƙuri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.
Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri É—aya.
Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faɗa na ƙarshe bai yi masa daɗi ba.
***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ƙasan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.
Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karɓo masa, sai dai ta bar shi ya ɗan farfaɗo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.
Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.
Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.
Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci"
Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.
"Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya É—an tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah"
Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaɓe baki.
Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message É—in mai sunan baba.
Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ƙanan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.
Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.
Unexpectedly ya ɗaga kai ya ga Iman, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Sannu da zuwa yaya umar".
"Yauwwa sannunki" daga nan ta yi masa jagora, har ciki.
Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya É—auki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu.
"Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?" Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir.
Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haÉ—e rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba.
Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta.
Ammi ta ce "Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sauƙi.
Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama.
Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ƙi yarda ya ajiye shi ya maƙalƙale shi.
Ya fita da shi a kafaɗarsa ya na murmushi, murmushin ba ƙaramin kyau ya yi masa ba.
Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba.
Ya É—an kalleta sannan ya ce wa Sabir "Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?"
Iman ta yi murmushi ta ce "Baban mai sunan baba"
Murmushi ya yi, ya miƙa mata sabir da yake ta ihu, ya na sake miƙawa umar hannu.
"Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun É—azu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani" Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata.
"Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa".
"Shut up malama" yayi maganar cikin fushi da kishi.
"Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?" rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir.
Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ƙura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana.
Rai a ɓace ta wuce, ba ƙaramin haushi ta ji ba, dan tuni ta fara kuka.
Ruma ta ce "Mai sunan baba, bari na raka ka"