← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 124

Sashe 120

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fa lafawa, suna can suna cigaba da tashin hankalin su, ni ina nan ina fama da kaina, da mutuwar ɗa na, mummy sun watse da Hajiya Lubabatu, ashe Jabir lalata suke shi da ruƙayya, abun duk babu daɗi mahmud dai ya rufe shi"

Laila ta ce "Lamarin gidan nan sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa mu dace kawai mimi, bari na bari ki huta"

"To anty laila na gode sosai"

Tana gama wayar, Gwaggo ta shigo da kunun kanwa, ta ce ruma ta sha.

Ruma ta ce ita wallahi ta gaji da wannan kunun kanwar, gudawa yake sakata.

"To idan baki sha ba nonon ya zube ki huta ai, gyara ki nake son yi, na bayar da dawa ma a niƙota in sheƙa miki tuwo, ga yajin daddawar ki nan"

"Gaskiya gwaggo ba zan ci tuwon dawa ba, in haihu ki bani wani tuwon dawa taɓ. Kunu kuma ina da sauran sabayata, yaushe zan ta shan kunun kanwa cikina yana ciwo".

"Kya ji da shi dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya"

Haka rumaisa suke faÉ—a da gwaggo, komai sai ruma tayi raki.

Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa taƙi yadda ayi,  ta maƙale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi.

Takawa ya shiga É—akin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce 'Mimi meyasa ki ke da gardama ne?"

"Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar É—a na, ko na ruwan zafi?"

"Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je" yayi maganar yana miƙa mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa.

Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaÉ—an.

A banÉ—akinsa ya haÉ—a ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai.

Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya É—auki magungunan ta ya bata ta sha.

Ya kalleshi ta ce "Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?"

Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata.

Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ƙasar.

Ya ce "Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah"

Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaɓi.

Gaba É—ay tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa É—an, amma akwai wani pain É—in na daban.

Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi haƙuri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace.

(0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haÉ—in maman Khadija na sabaya
0703 777 7442)

Da safe har wurin ƙarfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita.

Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faɗa "Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ƙwari ba, dama gashi kin ƙi bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ƙarata".

"Ni fa gwaggo ke ba kya lallaɓa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ranƙwashi na ki ka yi"

"An ƙi a lallaɓa ki, ku ƙara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baɗala ba" haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta.

Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raÉ—aÉ—i da É—acin abun da iyalinsa suka aikata.
Wanda ya É—ora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haÉ—i, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so.

A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus.

Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta roƙi a saka baki a bayar da belin jamil, kowa yaƙi.

Samha ba ta taɓa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba.

Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan buƙatar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa'anin yin ba ne ba!.

***
Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ƙanin nata sam bashi da ɓaci.

Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin.

Babu ɓata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan.

Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce "Adamu ne?"

Umar ya ce "Kin gane shi? Kin san Ammi?"

Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Na san Bintu, bintu ƴar ɗakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ƙaunar ji"

Mahmud ya ce "Kin tuna jikar ki mairamu?"

Ade ta fashe da kuka, ta ce "Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ƴan fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ƙaryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ƴan uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro ɗan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan".

Mahmud ya ce "Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?"

Ade ta ce "Waye kuma ima?"

Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin.

Jiki na rawa ta ce "Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta riƙe ƴar mairamu?"

Mahmud ya ce "Ƙwarai kuwa wannan mijinta ne ma?"

Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka.

Ta ce "Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba ɗaya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari" nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da haƙuri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su.

Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daÉ—i da malam umar ya zamana mijin jikarta.

Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.

Nan da nan riga ta É—auka, an samu Æ´ar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.

Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga Æ´ar mairamu.

Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman.
Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta É—aya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?"

Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman É—in da amm...

Ade ta ce "Wane mutum, da ƙafar nan tawa ko a ƙafa zan taka na je kano, na ga Bintu"

Alhaji Aminu ya ce "Da wace ƙafar? Ƙafa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba ɗaya "

Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haÉ—a kai da Æ´an bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.
Chapter 120 · 0% Book details