← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 112

Sashe 93

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da suka iso gidan mohd tun daga kan harabar gidan Ryynt tasan cewa an qara qaya ta gidan sbd gabad'aya kujerun zama na shan iska an canza ba wad'an da ta sani bane haka da suka zo kan falo kaf komai yasa an sake sauya wa akan wad'anda malika ta farfasa kmr ma ba wata 6arna da ta ta6a faruwa a falon don an tsarashi matuqa Ryynt sae kallon falon take abin sha'awa kmr wata aljànnar duniya komai fari tas sae qawar da akayi da gold .
Da suka je d'akinta ma hakane Fari n gold duk an canza komai kmr d'akin turawa.
Dama tun da rana man yazo da kayanta kuma ta samu ya tsara mata komai sae akwatin mami ta kar6a dake hannun sa tasa a wardrobe ya bata makullin d'akin da ke kusa da ita wato inda alawiyya zata zauna wanda dama d'akin don baqi akayi shi.
Sae da ta kar6i makullin yace"idan kin kaita d'akin kizo falo ina son zanyi magana da kune keda malika"
Ryynt tace"to"
Snn ya fita ita kuma taje takai alawiyya a masaukinta ta d'an nuna mata yanda zatayi amfani da abubuwa ta fito taje downstairs ta samu har ya kiro malika taje tayi zaune ya soma yi musu bayanin tsari da kuma irin zaman lafiyan da yake so ayi a gidan shi baya son wani tashin hankali ko wani makirci da qulle qulle byn nn ya raba musu kwana wato two two days da kowace zata riqa yi a nata duty snn yace idan da akwae mai magana a cikin su sae tayi.
kowaccen su tayi shiru sae can Ryynt dake zaune qasa kusa da gefen kujera tace ita dae bata da abin cewa dmn tsarin da yayi dae dae ne a gurinta nn ya kalli malika dake zaune kan kujera kusa da shi wacce kmr ma bada su yake zancen ba ta wani d'aura qafa kan qafa tana chat yayinda take tauna chewing gum a bakinta.
Yace"kefa?
Ba tare da ta kalle sa ba tace"bani da abin cewa"
Daga haka ta tashi ta bar gurin ba tare da taji me zae ce ba.
Bae damu ba sae kallon Ryynt yayi d'auke da murmushi a fuskar sa ya sauko kan kujera ya zauna qasa kusa da ita yakai hannu ya tallabo fuskarta yana kallonta yace"kin san dae cewa dutyn ki ne yau don haka je ki sallami alawiyya da mami kizo ina jiranki a d'aki"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tare da gyad'a masa kai.
Nan suka tashi mohd ya nufi 6angaren d'akin sa itama haka.
Koda taje ta sami mami kwance akan bed tayi bacci.
Ta nufi wardrobe ta bud'e ta ciro farar rigar baccin ta irin wad'an da take sawa a mumbae sae dai wnn tana da er sama da zata rufe mata jikinta har qasa.
Bayan ta cire kayan jikinta sae da ta qara shafe koina na jikinta da turare snn ta saka kayan baccinta ,
ta cire wa mami kayan jikinta ta saka mata na bacci ta d'auke ta ta kaita d'akin alawiyya ta rufo musu d'akin ta fito.

koda tazo zata shiga d'akin mohd sae ga malika itama zata shiga da mamaki ta kalli Ryynt tace"jarababbiya me kuma zaki shiga yi a d'akin shi ke bada duty ba ko kuma nn d'akin uwarki ne da kike shiga duk lokacinda kika ga dama"

Man dake cikin d'akin shi yana kallon su ta ta camera setting a jikin TV ya fito a fusace yana kallon malika yace"wace irin magana ce wnn ke har kinada bakin kirama wani jarababbe wlh mind ur tongue kar na qara jin kin zage ta idan har ba so kike na sa6a miki ba and 6ace a nn in daina ganin ki da wani shirmen zancen ki can"
Malika tace"wlh ba inda zanje sae naji dan ubanta kan me zata fara duty kafin ni"
Yace"bana son raini su kwana biyun da kikayi kina duty fa!
Tace"yaushe ne ka raba mana duty da har na kwana biyu ina yi,ko kuma kwana biyun da suka wuce kulawar ka ka bani da har za kace nayi nawa duty.
wani irin mugun kallo ya mata zae yi magana Ryynt ta katse shi da cewa"No barta she is ryt"
Daga haka ta juya ta bar gurin malika ta bita da kallo le6ace da baki ita yaushe ne ta fara bokon da zata wani fara sako turanci a zancenta.
Tana qisa hkne a cikin ranta mohd kuwa 6acin rae bae bar ya tsaya ba ya koma daga ciki kafin malika ke binsa daga baya.
Ryynt kuwa d'akin alawiyya taje ta d'auko mami ta maida ta d'akinta tayi zaune kan bed tare da share qwallar da suka zubo mata sbd sosai taji ciwon zagin iyayenta da malika tayi had'i da jarababbiyar da ta kirata dashi.
Nan tayi addu'a ta kwanta had'e da kashe musu wutar d'akin.

Guraren qarfe goma sha biyu sae ga man ya shigo d'akin ya sami Ryynt duk tayi zufa sbd d'akin d'if ba AC nan ya kunna musu Ac snn yaje a hnkli ya cire mata er samar rigar baccinta sae kallon fuskar ta yake dake matuqar bashi sha'awa idan tana bacci yayinda yake ta faman shafa cikinta yaje a hnkli kan goshinta ya d'aura mata kiss snn ya tashi ya fita ya bar d'akin wanda koda ya fita idon Ryynt na kansa sbd taji lokacinda ya shigo sae tayi kmr bata ji sa ba.

Washe gari tun da asuba sae da yaje ya tashe ta snn ya wuce masallaci ita kuma bayan ta tashi tayi arwala taje ta tashi alawiyya.

Guraren qarfe goma ya sami Ryynt cikin kwalliyar ta sae zuba qamshi take kmr wacce zata fita anguwa.
Yayi tsaye jingine a bakin qofa sae kallonta yake cike da so ,
Ryynt dake zaune gun dressing mirror tana qara gyara fuskarta ta hango shi ta jikin mirror tana kallo ya qaraso ya kwanta kan bayanta a hnkli ya rungume ta tare da d'aura mata peck gefen fuska suna masu kallon junan d'auke da murmushi ta jikin mirror yace"kinyi kyau sosai my Ryynt"
A hnkli ta furta "nagode"
Snn ta mishi ina kwana byn ya amsa gaisuwar ne yace"ya akayi bayan kinsan jiya na gaya muku a tare za'a riqa cin abinci amma sae kika sa kuku ya kawo maki naki kika iza mami ita kad'ai.
Tace"Aa ae alawiyya nasa ya kaiwa abincin rashin fitowa na kuma ban kammala shiryawa bane sae yanzun"
Yace"oh sorry ae na d'auka ko kinyi fishi dani ne har na fara tunanin yanda zan bada haquri"
Tace"kan me zanyi fushi da kai?
Yace"abar zancen kawai tashi muje kar yunwa ta illata min ke da babyna nn ta tashi suka fito suna tafe mohd ke cewa"hln dae tsarin gidan nn da aka sauya bai maki ba?
Ta kalle sa tace"Allah yayi min kyau sosai me ka gani?
Yace"gani nayi tun jiya baki ce komai ba har yau"
Tace"hm ae tsarin kyawon sa ne ma yasa na kasa cewa komai amma cikin zuciyata wlh sae yaba tsarin gidan nake sae dae nace Allah ya qara maka bud'i"
Mohd yace"Amin"
Dai dae sun qaraso gun dining kowanen su yaja kujera ya zauna suka soma cin abinci malika dake kusa da man taje kan jikin sa ta zauna sae wani iyayi take tana ciyadda shi don kawae Ryynt ta gani taji haushi ,Ryynt kuwa yi tayi tamkar ma bata san da zamanta a gurin ba sae cin abincin ta take haushin ta d'aya mami dake gurin tana fuskantar su wacce bae kamata tana kallon irin abubuwan nn ba.

Sry 4 dis one banji dad'i bane da qyar ma nayi wnn.

Billy giro😊
[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page 82*
Cikin hikima da dabara mohd ya janye malika daga kan jikin sa ya soma ciyadda kanshi sbd ya fahimci tana yi ne kawae don ta 6ata ran Ryynt wacce yaji dad'in ganin yanda ta nuna ko oho duk da yasan dole a ranta xata ji wani abu.
Suna kammala cin abincin Mohd yakai hannu zae d'auki briefcase d'insa dake ajiye gefe malika ta rigashi d'auka ta rataya jakar ta tafi dashi rungume a jikin ta sae kwarkwasa take still Ryynt bata bi ta kanta ba sae hannun mami taja suka tafi d'aki.

Da dare bayan isha'i Ryynt ce zaune a d'akin ta tana koyarda su Alawiyya da mami karatun qur'ani yanda ake fitar da harafi da komai su kuma suna saurarenta idan ta gama su karanto inda duk sukayi kuren fitar da harafi ta gyara musu.
Tsawon lokaci Man na tsaye a bakin qofar d'akin yana sauraren yanda qira'ar Ryynt ke shiga kunnen sa mai dad'i sae duk ya qara jin sonta a ransa yana kuma jin shi kam ya gama yin sa'ar uwar 'ya'yansa a duniya.
Gyaran murya yayi had'e da yin sallama Ryynt ta kai aya snn ta amsa masa sallama tana mai kallon sa sae murmushi yake mata har ya qaraso gurin su yazo gab da ita ya zauna nn qasa kan dardaumar sallah inda take zaune akai nn mami da alawiyya suka gaida shi, ya amsa musu yayinda alawiyya taja hannun mami suka fita.
Ryynt ta gaida shi cikin sakin fuska,
Shima fuskar sa a sake ya amsa mata had'e da riqo hannun ta yana mae kallon fuskarta yace"karatun ki da dad'i Ryynt?
Ryynt tayi murmushi tace"uhm zolaya koh?
A hnkli yaja hancinta yace"ba wani nn aikin san gaskiya na fad'a,don haka yau sae kin koya min qira'ar nn taki mae dad'i.
Ya fad'i hakane tare da janyo ta zuwa jikinsa ya d'auki qur'anin da ke ajiye kusa da ita ya bud'e,
Yace"oya karanta min ina jin ki"
Tace"hm Mk knn ni bance ka koya min taka qira'ar ba sae kai"
Chapter 93 · 0% Book details