← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 112

Sashe 104

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Malika ta fito daga kitchen knn riqe da plate da abinci akai yayinda d'ayan hannun ta ke riqe da glass cup da ruwan lemu a ciki.
Ta tsaya cak tana sauraren ina ne gud'a ke fitowa.
Kafin ta iya yin komai sae gasu sun shigo falon ba shiri ta saki plate da glass cup d'inda ke hannun ta tayi saurin dafe mararta da taji ta wani irin tsinka mata sae ga jini agurguje yana fitowa ta qafafunta yàyindà ta saki ido tana kallon Ryynt da suka fara shigowa ita da man tsaye a qafafuwanta lafiyar ta qalau ga kuma jarirae uku da ta gani a hannun su umma da inna wacce still sae gud'a take ci gaba dayi shiyasa da kmr ba wanda ya lura da malika a cikin su bare zancen jin qarar fashewar glass cup da plate d'inda ta yar har suka haura sama zuwa d'akin Ryynt.
Malika kuwa kmr wata zautatta ta nufi hanyar d'akinta ba tare da ta lura da jinin dake ci gaba da fita a jikinta ba har ta isa d'aki ta d'auki wayar ta kai tsaye ta kira fa'iza muryar ta na rawa tace"Wayyo Allah fa'iza na shiga uku wlh wnn abar bata mutu ba haka ma abinda ke cikinta da ta haifo har su uku"
Da qarfi fai'za tace"what! she is still a live fa kikace! kuma ta haifo en uku hm never ga dukkan alama tashin ki knn daga bacci kinyi mafarki shine kika zo kina gaya"
Malika tace"wlh maganar gaskiya nake gaya miki fa'iza yanzun nn suka shigo da ita har da yaran"
Hm!plan ne kawai suka had'a maki malika dan inaga akwai wanda ya ganki a lokacin da zaki saka mata wnn maganin"
No fa'iza na tabbatar wlh ba wanda ya ganni a lokacin da nake saka mata maganin dan duk yaran da take tare dasu sunyi bacci kuma man baya ko gari kin sani.
Faiza tace"malika ki yarda da zance na wnn maganin qarfin tsiya ne dashi kuma kince kin had'a mata overdose snn young girl like her ace ta haifi yara har uku haba ae hankali hanji ne wa ita nn"
Hm fa'iza na gaya miki fa a gaban idona wlh ina la6e ina kallo tasha ruwan da na saka mata maganin a ciki snn girman cikinta kad'ae ya isa na yarda cewa ita ta haifi yaran, at all yanzu nasan shike nn ta gama saye min miji"
Ta qarashe mgnr ne cike da qwallah tap a idonta.
Fa'iza tace"ae wlh bata isa ba tayi kad'an"
Qwalar da suka taru a idonta ne suka zubo cikin muryar ta mae d'auke da rawar kuka tace"to yanzu fa'iza me kike ganin zanyi wanda zanci riba a kanta kuma, na farko na xubar da ciki na a banza wanda da yanzu qila ma nice na haifa masa yaran,na biyu maganin da muka kar6o a qauye gurin boka na sawa man a abinci dmn ya tsaneta har ya fara aiki yazo ya karye kuma tun daga lokacin maganin bae sake ci ba yanzu na sa mata maganin da nake ganin da ita har abinda ke cikinta ba wanda zae yi survive amma sae gashi she is still a live an dawo da ita lafiya qalau da ita har yaran,known fa'iza how can i do, me kuma ya rage da zan mata yanzu .
Fa'ixa tace"wlh baza mu barta ba sae kin dawo da mijinki hannun ki ,ki shirya yanzu yanzu nn kizo gidana muje wani qauye gurin wani shaharren boka aikin sa kmr yanka wuqa yau yau d'in nn sae a neme ta a rasa da ita har 'ya'yan kuwa kuma sae a lafira ko za'a ganta ta wlh dan nasan wacce tasa akayiwa kishiyarta haka kuma har yau mgnr da ake shekara uku da suka wuce ba ita ba labarinta har iyayenta sun haqura da nema.
Malika tayi saurin share hawayenta tace"shikenan gani nn zuwa yanzun.
Nan ta tsinke wayar had'e da juyowa cikin hanzari sae kawae ta tsaya cak ko tako d'aya ta kasa yi tana kallon man dake tsaye a bakin qofa ga kuma jinin da ta hango tun daga wajen qofar har zuwa inda take tsaye a lokacin suma ne kawae bata yi ba ta dasqare guri d'aya dan tasan tata ta qare man ya gama jin komai dan jikin sa har rawa yake kan tsananin 6acin rae ga wani irin mugun kallo da yake mata har ya qaraso gareta wanda kae tsaya ya kai hannu kan qugun sa ya zaro belt d'in wandon sa a nn malika tayi saurin durqusawa kan guiwoyinta ta kama qafafunsa sae girgiza kanta take tana fad'in"my man dan girmañ Allah kayi haquri wlh kasan duk abinda nakeyi a dalilin sonda nake maka ne dan Allah kayi adalci akan hukuncin da zaka min na roqeka"

Da qarfin tsiya man ya ture ta ba tare da yace mata komai ba sae zabgar ta da ya fara yi ta shiga ihu tana roqon yayi haquri amma ina kmr ma ziga shi take qara yi dan sae dukanta yake ci gaba dayi ta koina baji ba gani ita kuma bata fasa ihu tana bashi haquri ba.
Ganin yana neman hallaka ta yasa ta fito d'akin aguje yana biye da ita yana duka har suka sauko downstairs zuwa falo aguje ta nufi hanyar fita ya fizgota yana ci gaba da dukanta sae ihu take sosai tana bashi haquri.
Sae gasu umma sun fito gabad'ayan su suna tambayar sa lafiya me yake faruwa bae basu amsa ba sae aikin ci gaba da dukan ta yake nn Nasir da shigowar sa knn ya samu da qyar ya riqe mohd wanda sae faman huci yake yana kallon malika da duk ya farfasa mata jiki,cikin 6aciñ randa yake d'auke dashi ya nunata da yatsa yace"kije na sake saki uku kuma yanzun yanzun nn fita a nn in daina ganin wlh"
Subuhanalillah!
Shine abinda su umma da nasir suka fad'a inna kuwa sae salati ta soma yi,
Ryynt bata iya cewa komai ba sae kallon malika take da ta d'oro hannu akae ta fashe da wani irin matsanancin kuka mae cike da nadamar abubuwan da ta aikata"
Tazo gabanta tana kuka sosai ta kama qafafuwan ta tace"Dan Allah Ryynt ki roqa min shi ya janye sakin wlh bazan sake yunqurin cutar da ke ba na rantse"
Ryynt bata iya cewa komai ba sae mohd ne yazo yaja malika ya tafi da ita qiiiiiii kmr kayan banza ya tura ta waje ya rufe qofa sae kuka take tana dukan qofar tana bashi haquri da qarshe ta gaji ta zame jikin qofar tana ci gaba da matsanan cin kukan da take tunanin shike nn rayuwarta ta lalace ta rasa mohd a rnr da take tunanin rnr farin ciki ce a gurinta amma ta zamo mata rnr baqin ciki mafi soyuwa da komai ya ca6e mata har d'an cikin da take kurin ta samu wata biyu da suka wuce taqi snr dashi akan sae burinta ya gama cika ko zata snr dashi gashi ya 6are,burin bae cika ba,ga saki uku ga kuma irin dukan da tasha, cikin ma bae ji d'aya daga cikin mugayen ayukkan da take aikatawa ba tukun.
Rayuwa knn shiyasa aka ce idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi kad'an dmn wata rana zaka iya fad'awa ciki.
Allah dae ya shirye mu yasa mu dace amin.

Mohd kuwa tun da ya fitar da malika ya rufe qofa su umma sukayo kanshi cike da son tambayar sa abinda ke faruwa bae bar sun kae ga tambayarsa ba yayi saurin barin gurin ya tafi zuwa d'akin sa.

Ba yanda suka iya nan suma suka juya suka koma daga ciki amma mafaiyar mohd da Nasir fita sukayi dan dama ta kirashi ne dmn ya maida ta gida tana so zata d'an shiryawa Ryynt abincin da masu biqi ke ci.
Chapter 104 · 0% Book details