← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 112

Sashe 66

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🔮🔮🔮🔮
*```Page 63```*
Aamil na fita d'akin Rynt ta zare bakinta cike da jin kunya ta kwantar da kanta a hnkli kan qirjinsa tana shaqar qamshin turaren sa.
Shi kuma mohd sae wani qara kwantar da ita yayi a qirjin nasa yana mae shafa bayanta a hnkli cikin natsuwa.
Aamil kuwa yana shiga d'akin inna ya sami Abba da zuwansa knn ko zama bai yi ba sae Amir da ya samu ya zame kan kujera yana gaida shi bai kula su ba sae gun inna yaje a rud'e wacce taje zuwa bud'e fridge knn yace"inna zan so naji wace ce Rynt kuma ya take da mohd da na gansu a d'aki tare"
Abba dake kallonsa yace"mohd fa kace a gidan nn!
Aamil bai iya cewa komai ba sae kansa da ya gyad'awa Abba cikin rashin fhmtr yanayin da yaga Abba ya shiga ciki wanda yaga ya tafi fuuuu! a fusace yana fad'in lallai kuwa yau zan nuna masa haifo sa akayi ba haifar kansa yayi ba!
A nn Man da Rynt suka tsinkayo muryar Abba tafe hkn yasa suka miqe tsaye zumbur sae ga su Abba,inna, Aamil da kuma Amir duk sun shigo d'akin,inda kai tsaye Abba ya nufi mohd ya watsa masa mari biyu masu kyau ya kuma nuna kansa da yatsa yace"dan uwarka ni zaka mayar d'an iska ko kuwa shima nn gidan ban hanaka shigowa bane iye!
A natse mohd ya kalli Abba cikin damuwa sosai yace"dan Allah Abba....kaga yi gaggawar fita a nn kuma duk ka kuskura na koma ganin qafar ka a nn gidan ko a gidana to kuwa zan furta abinda baka ta6a tsammanin zan furta a gare ka ba!
mohd ya kalli Abba d'auke da idanuwansa da suka kad'a sukayi jajur yace"dan Allah Abba kayi haquri ka saurare ni wlh nazo ne dmn na bawa Rynt haquri na maida ta..... Kul!har abada Rayyanat baza ta ta6a komawa gare ka ba don ba shashashan mutum bane ni da zan aura ma ita ka sakota ka kuma yi tunanin zan barka ka maida ta,
Mohd yace"Abba itama fa tana son komawa"
Nan Abba yayi saurin kallon Rayyanat wacce ke kallon mohd shaye da toka yace"Rynt abinda yace hakane?
Ta kauda fuskarta da kallon da take yiwa mohd had'e da girgiza kanta snn tace"Aa Abba gsky ni bana son komawa"
Abba ya kalli Man dake kallon Rynt yace"maqaryacin banza shashasha fita a nn in daina ganin ka!
Mohd da ya duqar da kansa qasa yace"pls Abba dan Allah ko don abinda ke cikinta ka bar ta ta koma"
Kafin Abba yace "komai Inna ta riga sa da cewa" bafa zata koma ba shashasha marar mutunci idan har dan abinda ke cikin ta ne da ta haife shi zata baka abunka kaje can ka qarata dashi dan baza ta raina maka shi ba karatun ta zata ci gaba dayi.
Abba yace"Ba ma wnn kad'ai ba inna Aamil yaje min da wani zance na yana son zai auri Rynt na kuma yi na'am da zancen nasa dmn Aamil mutum ne da nsn zae riqe ta amana ko da kuwa ace baya sonta aka aura mae bare shi da kanshi yace yana so da haka na yanke shawarar idan Rynt ta haifu zan had'a aurensu sae taci gaba da karatun ta a can d'akinta.
Tun lokacin da Abba ya fara zancen sa mohd ya shiga wani irin tashin hankali yana kallon Aamil cikin mugun mamaki haka ma a gurin Amir ,Rynt kuwa banbarakwae taji zancen ta bud'e ido tana kallon Aamil yayinda Aamil duk ya sukuikuice yana kallon Abba cike da son cewa wani abu.
Sae dae kafin suce komai sae kukan kura suka ji mohd yayi zai afkawa Aamil Abba ya dakatar da dashi ta hanyar ture shi had'e da kife sa da mari yace "dan uwarka borin kunyar ne zaka saukar akanshi dan zae min abinda kai ka kasa min,to bari kaji Aamil yafi min kai sau dubu dmn yau ya yaye min duk wani baqin ciki da na shiga a knka,kuma aure shida Rynt ba fashi!
A nn Idanuwan mohd suka qara yin jajur har ana hango jijiyoyin goshinsa duk sun tashi yace"Abba wane irin zance ne wnn ace Aamil zai auri Rynt....gaya min inda yake haramun dan Aamil ya auri matar da ka saka!
Kmr zae yi kuka yace"haba Abba wnn ai abin kunya ne aji cewa wae Aamil zae auri matar da na saka kuma ai Abba ni wlh na mai......cikin daka tsawa Abba yace"kaga maza fita bana son sake jin zancen ka a nn idan ba haka ba wlh kasan sauran shashasha kawae!
Mohd bai iya fita ba sae wani irin mugun kallo da yake yi wa Aamil kmr zae je ya bugoshi dan jikin sa har ya soma rawa ma sae Amir ne yayi saurin jan hannunsa suka fita yayinda shi kuma Aamil yaja hannun inna suka tafi d'aki,Abba kuwa gun Rynt ya tsaya dmn jin ra'ayin ta wacce ya kalla a natse yace"Rynt gaya min gsky kina son komawa gidan mohd koh?
Tace"wlh Abba bana so"
Yace"to kina ganin zaki iya auren Aamil bayan kin haifu?
Shiru tayi sbd shirin da take yi da Aamil muqaddari ne da ta samu kanta dashi haka kuma bata da tabbacin wanda ya kashe mata baffanta a cikin su ukun ,
kawae dai tafi zargin cewa mohd ne.
Abba dake kallonta jin shirun yasa ya bud'e baki zuwa magana sae kawai wayar sa tayi qara ya ciro wyr a aljihu ya d'aga yayinda ni kuma na garzaya gun su inna dmn jin abinda Aamil zai ce da inna.
Cikin yanayin damuwa sosai na samu Aamil yana cewa da inna"inna wlh kwata kwata ban gane cewa Rynt matar man bace shiyasa naje wa Abba da zancen cewa ina son zan aureta, ba wae dan nasan cewa sun rabu ba"
Inna ta sauke numfashi tace"to Aamil ynx dan kaji cewa mtr da muhammadu ya saka ce meye matsala ko kuma sonta ne kaji ba kayi da kaji cewa ta ta6a aure har tana d'auke da juna biyu"
Ko d'aya inna ba ciki ba ko 'ya'ya goma ne da Rynt ni mae iya aurenta ne amma kasancewar ta mtr da man ya saka ce yasa bazan iya auren ta ba inna"
Aamil inace ba haramun bane dan muhammadu ya saki Rynt ka aura ,
Aamil yace"duk da haka dae inna ana barin halak dan kunya dmn man jini na ne da bazan iya masa haka ba"
Inna tace"Dan muhamadu yana jinin ka shi kuwa ubanka kabiru da yake ikirarin ka wanke mai baqincin da yake d'auke dashi fa ko kowa kaima so kake ka watsa mae qasa a ido ne iye!
ko d'aya inna bana son haka amma na fi son Abba ya haqura ya bar man ya maida matar sa tunda har ya nuna yana son maida ta"
Inna tace" Rynt fa bazata koma gidan muhammadu ba dan kaji in gaya ma idan kai d'in bazaka aureta ba ai bazata rasa wani masoyin ba"
Aamil ya fitar da numfashi yace"dan Allah inna me yasa ba kwa son ta koma ne?
Ajiyar zuciya inna ta sauke kafin take bashi kaf labarin abinda ya faru tsakanin man da Rynt.
Nan Aamil ya jima shiru yana tuna lokacinda inna ta mari man har abin ya d'aure masa kai wanda sosai yaso yaji dalilin faruwar hakan amma kuma sae bai san ya akayi bae tambayi dalilin ba,haka kuma ya tuna lokacinda ya shiga d'akin Rynt ta mai ihu a tunanin ta man ne kuma duk ta ganshi sae taji waye tukun kafin take sakewa dashi,ko hkn kad'ai abune da ya kamata ace ya fhmci wani abu amma kuma sae bai fhmta ba ,sae yanxu da inna ta bashi lbr.
Aamil ya ajiye tunanin sa da kallon inna yace"a gsky inna mohd bai kyauta ba amma tunda yayi nadama ayi haquri abar shi ya maida ta"
Inna tace"yo wa ya gaya ma nadama ce yayi kawae yana son abinda ke cikin Rynh ne dmn na tabbatar idan muka barta ta koma to kuwa ina gaya ma da ta haife mae abinda ke cikinta zaici gaba da wulaqanta ta ne,amma kai nsn zaka riqe Rynt amana tun da har ka iya riqe khadija tsawon lokaci ba'a ta6a jin kanku ba duk da kuwa cewa auren had'i ne a tsakanin ku da ita ba wae dan kuna son juna ba.
Aamil kam baya ko jinta dan yayi shiru yana tunanin shidae a ganin sa mohd ba don cikin sa kad'ai ne yake son Ryynt ta koma ba,dmn ya fhmci sosai mohd ya shiga damuwa a lokacinda Abba yace idan Rynt ta haifu zai had'a auren sa da Rynt.
Kuma ko abinda ya samu yana mata a d'aki abune dake nuna soyayya a tsakanin su, sae dai kuma Rynt d'in ce da ban mamaki da tace bata son komawa gidan mohd ko meyasa?
Baya da amsa kan dole ya sauke numfashi ya kalli inna yace"shike nn inna zan yi shawara"
Chapter 66 · 0% Book details