← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 112

Sashe 23

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe ko break fast basuyi ba mami ta jawo ledar chocolate ta fita wae zata kaiwa anti amarya ta d'iba.
Fitar ta keda wuya ta jiyo kukan mami ta fito da sauri har tana had'awa da gudu tana isowa main falo ta had'u da mohd shima ya fito sbd jin kukan mami da yayi ,mami taje da gudu jikin Rynt inda cikin kuka sosai take nuna malika ,mohd yace da malika me kika mata ne! shaye da toka tace"sanin kanka ne qanwar nn taka baqin srt tsiya ne da ita ,tazo ta sameni ina bacci daga kawo min ledar chocolate tayi wae na d'iba nace mata bana so bai isheta ba sae da ta wani cika ni da srt shine ni kuma na mareta,
jiki sanyaye ya kalli mami wacce bakinta ke fitar da jini ya jawo hannunta yasa tissue ya goge mata jinin yace"ki daina takura anti amarya idan tana bacci kinji, cikin muryar kuka tace"Allah yaya qarya take ba bacci take ba "malika ta dallah mata harara tace"dan ubanki ni ke qarya "a fusace ya d'ago yace"malika mind ur tongue qanwata ce fa kike zagin ubanta"to kai baka ji me tace min bane!kuma indai zagin ubana ne ai akanka na koya ,tsaki yayi ya kalli Rynt wacce yake ganin kmr duk laifin ta ne yace"da Allah malama jata ku tafi!
Rynt ta kalle shi snn ta d'auki mami tana share mata hawaye tace"yi hqr Allah zai isar miki"
Malika tace"jar uba! ke ni kike gaya ma magana!
ta tafi fuuu!zata kaiwa Rynt duka ,mohd ya jawota yace"barta kawai zanyi maganin ta ne,nn ya tafi da ita sae masifa take tana sirfàwa Rynt zagi har suka shige 6angaren mohd.
ta6e baki Rynt tayi snn ta wuce d'auke da mami.

Da dare mohd ya shigo d'akin Rynt ya sami Rynt da mami suna pillow fight sae dariya suke suna dukan pillown juna har Rynt tayi nasarar da pillown mami ya qwace ya fad'i qasa nn Rynt ta tashi cikin dariya tana mata gwalo tana fad'in "ko yanzu na cinye ki"cikin shagw6a mami ta turo baki,sae kuma ta washe baki ta tashi da sauri ta bud'e wardrobe ta d'auko qatuwar teddyn ta da tasan Rynt na mugun jin tsoro tayo kan Rynh aguje zata liqa mata,Rynt da ko ganin ta bata son yi ta rufe ido ta kuma kwasa da gudu zata bar d'akin,sae jin tayi ta fad'a jikin mutum nn ta fasa wani irin ihu ta zube gabad'aya a jikin man.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/16/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮
_*page*_ *```28&29```*
Tsaki mohd yaja tare da ture ta daga jikin shi, kan ta kai qasa yayi saurin tarbota dan sae a lokacin ya fhmci suma tayi,ya kwantar da ita nan qasan tiles ,mami kuwa ta jefar da teddy tazo da gudu gun Rynt ta saki ido tana kallon Rynt dake kwance,
mohd yace"je 6oye teddy ki d'ebo min ruwa"
Mami taje ta maida teddy snn ta kawo masa ruwa ya kar6i ruwan ya shiga yayyafa ma Rynt a fuska,firgigit ta tashi tana ihu tana fad'in"mami ki daina liqa min wnn abun bana so dan Allah"ta qarashe mgnr kmr qaramar yarinyar da zatayi kuka,wacce sae a lokacin ta kula da mohd da ko lokacinda taci karo dashi ta d'auka ko teddy ce,shiyasa ta qara firgicewa har ta kaita ga suma .
Mami tazo gab da ita tana kallon Rynt wacce tayi zaune ta had'e kai da guiwa yayinda jikinta ke ta rawar tsoro ta dafa ta snn tace"anti kiyi haquri kinji bazan sake ba"kafin Rynt tace komai mohd yace da mami,"d'auko min teddyn naje dashi d'akina idan kin buqata sae kije d'akina kiyi wasa a can ko? Mami ta gyad'a kanta tare da tashi ta d'auko mai teddyn ta bashi ya kar6a tare da duqawa zai d'auki agogon sa da ya fad'i kusa da Rynt,dai dai Rynt ta d'ago fuskarta da idanunta ke cike tap da qwallah,ganin teddy a hannun shi yasa tayi saurin matsawa tare da tura masa agogon sa da ta fhmci zai d'auka, sae da ya kalleta snn ya d'auki agogon ya fita.
Mami tazo jiki sanyaye gun Rynt tace"Anti kin haqura ko?Rynt ta gyad'a mata kai tare da share hawayenda suka zubo mata,snn tayi d'an murmushi tace"ba komai ya wuce"
Daga haka ta tashi sukayi shirin bacci suka kwanta.

Mohd kuwa 6angarensa ya nufa yana shiga ya jefar da teddy kan sofa snn yaje ya kwanta kan bed tare da ciro wyrsa a aljihu ya fara latse latse.
Malika ce ta shigo d'akin cikin rgrta ta bacci dani da babu taje kusa dashi ta kwanta tana kallon abinda yake yi a waya, ta kalli fuskar shi snn tace"my man ashe kana game"yace"in tamin dad'i ba"ta mirgino kan jikin sa tare da kai hannu tana shafa sajen fuskar shi tace"my man nifa ban gane ba har mun shigo cikin sati na biyu da aure amma banji kana zancen zamuje honeymoon ba"
yace "malika nida ke son komawa bakin aiki ina kuma zancen wani honeymoon"
ta 6ata fuska tana kallon shi tace"ba wani nn gsky ni sae munje honeymoon tunda ba fina akayi ba"to shikenan zamu je d'in"
kiss ta bashi tare da fad'in "tank u"yayi murmushi yaci gaba da aikin sa kawai,nn malika ta shiga qoqarin hana mishi game d'in don sae wasu abubuwa take mishi a jiki har ta kai ga ta qwace wyr tana qoqarin had'e bakin su, ya kauda bakinsa gefe snn ya koma kallonta sbd buttons d'in rgr sa da ta shiga 6allewa ya riqo hannunta yace"malika wae ke ba kya gajiya ne,naga yaushe yaushe ne muka rabu"
to my man kai d'in na daban ne kasani shiyasa bana gajiyawa da kai"ta qarashe mgnr tare da kashe mai ido d'aya ,yace"to muyi bacci har gobe don yanzu kam ngji"ta wani 6ata fuska tace"gsky nifa ina buqata"
ya salam shine abinda ya fad'a a ransa har ga Allah baya son yawan laluboshi da take wace irin mace ce da tun auransu bata ta6a bashi rana d'aya ya huta ba har yau,nn yace"ok ina zuwa"ya tashi ya fita sae gashi ya dawo d'auke da fresh milk da cups ya kalleta d'auke da murmushi yace"bari musha tukun ko" bai jira amsarta ba ya tsiyaya mata fresh milk ya bata,
har ta shanye cup d'in tas shi bai ko fara shan wacce ya zuba ma kanshi ba,ya kar6i nata cup yace"na qara miki ne? Ta girgiza kanta tare da matsowa kusa dashi ta kwantar da kanta a qirjin sa, daga nn tayi bacci don dama maganin bacci ya zuba mata don kawai ya huta da jarabarta.

Bayan kwana uku da faruwar hakane zuwa honeymoon d'insu ya tashi dan har ma ga gobe zasu tafi shiyasa tun safe yakai malika gidan iyayenta don ta musu ban kwana, Rynt kam bata san abinda ake ciki ba kawai dai kullum da safe mohd na shigowa 6angarenta yaja mami suyi breakfast ita kuma kuku ake aikowa ya kawo mata nata,kuma in banda gaisuwa ba abinda ke had'a ta da mohd.

Zaune suke ita da mami a d'aki kan bed tana koyadda mami karatun qur'ani, ya shigo ya same su ,
Rynt na had'a ido dashi ta kauda kai amma shi still kallonta yake sae ma cewa yayi ki taso keda mami zamu fita, daga haka ya juyawar sa ya fita mami ta bishi da gudu tana jin dad'i.

Koda Rynt ta fito harabar gidan ta samu har sun shiga mota ita kad'ai suke jira,taje ta shiga motar itama.
Basu zarce koina ba sae family house,mami ta tafi da gudu zuwa 6angaren su,mohd kuwa ya nufi nasu 6angare shida Rynt ,
suna shiga falo suka sami Abba zaune ta durqusa ta gaidashi cike da ladabi ,ya amsa mata cikin sakin fuska.
Byn sun zauna da ita har mohd d'in snn Abba yace" nine nace yazo min dake kan wani rashin adalci da naji yana shirin yi da na masa magana se yace kece baki buqaci hkn ba,Rynt ta kalli Abba don ita bata gane inda zancen nasa ya dosa ba, Abba yace"batun zuwan su honeymoon ne shida malika shin kinsan da batun zuwan?
Rynt da batasan meye honeymoon ba illa kawai abinda ta fhmta wani guri zasu, zuwansu da rashin zuwansu kuwa duk d'aya ne a gurinta se tace"eh"
to meyasa baza ki bisu bane ko kuma shi ya hana miki? Aa Abba kawai dai ina son zan koma islamiyya ne, Abba ya kalli mohd yace"to kaji idan ita waccan d'in honeymoon ta buqaci zuwa kaji wnn islamiyya take buqatar komawa don haka sae kayi adalci a tsakanin su"yace"inshaAllah Abba, nn mohd ya tashi ya fita Rynt kuwa ta tashi zata haura sama dmn gaida hjyr su mohd Abba yace"Ai bata nn ta fita,
tafi kawai abinki ku koma gida, tace"to snn ta fita"

Koda ta fito mohd na jingine jikin mota yana jiran fitowar ta,bata nufi gunshi ba sae 6angaren su saliha ta nufa yace"ke ina kuma zuwa?tace " Zanje gaida mama ne daga haka bata jira amsar shi ba ta shige abinta.
Bata wani jima ba ta fito ita kad'ai ba tare da mami ba don dama tun cikin mota da suna kan hnyr zowa tace in sunxo sae dare zata koma.

Tafe suke kan hanya ba mai ce ma wani can Rynt tace"gidan inna fa"kallon ta kawai yayi ba tare da yace komai ba yaci gaba da tuqin sa har suka isa gida.

Da dare ta fito daga wanka mohd ya shigo d'akin riqe da hannun mami ya same ta sanye da qaton hijab d'inta as usual ,ta d'auko Vaseline zata je kan bed ta shafa,ya tsaya bakin qofa mami kuwa taje da gudu gun Rynt snn ya juya ya bar d'akin yana mai jiyo yanda mami ta fara cika Rynt da srt.
Chapter 23 · 0% Book details