← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 112

Sashe 100

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan sun koma gida ne Ryynt na kwance d'aure da towel a jikin ta ga dukkan alama wanka ta fito bata samu tayi shirin bacci ba tayi kwance kmr wata marar lafiya don haka kawai abubuwan da suka faru a yau ta shiga jin kewar baffanta sosai.
Nan mohd ya shigo d'akin cikin shirin sa na bacci sae zuba qamshi yake yaje kusa da ita ya zauna ta tashi a hnkli taje zuwa jikin sa tare da kwantar da kanta a qirjinsa tana shaqar qamshin turaren sa mohd ya d'ago fuskarta yana kallon idanun ta dake son fitar da qwalla yace"kar kiyi kuka gaya min mene ne kinji"
Sae da ta maida kanta a qirjinsa ta kwantar snn tace"ba komai"
shiru yayi bae sake ce mata komai ba dan ya fahimci damuwar baffanta ce a tare da ita ,
yasan da ya matsa mata zata iya fashe masa da kuka shi kuma ba son kukan nata yake ba.
Nan yakai hannu sa a hankali yana shafa bayanta d'akin yayi tsit kmr ba kowa sae can mohd yace"tashi muje d'akina kinji"
Nan ta janye jikinta daga nashi zata tashi dmn d'auko kayan bacci mohd yace"yi zamanki bari na d'auko maki "
Nan ya tashi ya ciro mata rigar bacci a cikin wardrobe yaje ya sa mata rigar da kanshi snn yaja ta suka tafi d'akin shi.

washe gari Ryynt ce rungume a jikin man sun fito bathroom sae kuka take tana yarfi da hannu tana d'ingishi man dake janye da ita duk ya damu sae faman rarrashin ta yake har suka je kan bed ya zaunar da ita ta jawo blanket ta rufe jikinta sbd ba komai a jikin nata haka ma man wanda bae damu da ya rufa jikin nasa ba sae qafar ta ya riqo yana dubawa wacce ta fad'i kan qafar ne a bathroom ,
yakai hannu a hnkli yana ja mata qafar amma hakan bae hana ta fasa ihu ta qanqame shi sosai tana kuka duk sae mohd ya qara shiga damuwa amma hkn ya dake yaci gaba da ja mata qafar sae kuka take tana roqon ya daina bae daina ba sae da ya tabbatar yaja qafar yanda ya dace snn ya tashi ya d'auko wani magani ya shafa mata a nn fa Ryynt ta soma wani kukan dan maganin ba qaramin zafi ne dashi ba mohd ya rungume ta a jikin sa sae rarrashinta yake yana shafa mata qafar har zafin maganin ya rage ta daina kuka sae
lafewa tayi sosai a jikin sa tana shafa sumar qirjin sa a hankali.
Mohd ya d'ago fuskarta yasa bayan hannun sa yana share mata hawaye kasancewar baya son saka mata yajin maganin da ya shafa mata a qafa.
Yace"sannu ina zuwa kinji"
Ta gyad'a masa kai yayinda ya tashi ya nemo boxer yasa snn ya saka jallabiya ya nufi bathroom ya wanke hannun sa ya fita.
Bae zarce koina ba sae d'akinta ya nemo mata kayan sawa ya fito riqe dasu a hannun shi sae ga malika ta fito daga 6angarenta ta bisa da ido le6ace da baki tana kallon sa har ya wuce taje ta zauna kan kujerar dining sae wani abu take ji a ranta na baqin ciki wae yau man ne ke kula wnn abar ba ita ba har ma kayan sawa shike d'auko mata abinda bae ta6a mata ba ko lokacinda sukayi soyayyar su ta amarci nn kawae taji qwallah sun ciko tap a idonta bata bar sun fito ba ta had'iye su takai hannu tana shafa cikinta cike da shu'umin murmushi kafin take zubawa kanta abincin breakfasts ta soma ci jim kad'an da fara cin abincin nata sae ga man ya fito tana kallo ya d'ibar musu abincin breakfast shida Ryynt ya koma daga ciki ba tare ta iya ce masa komai ba sae binsa da kallo tayi tace"hm aikin banza"
Nan taci gaba da breakfast d'inta ita kad'ae sbd mami dae tana school alawiyya kuwa har d'aki kuku ke kai mata nata.
Cikin qunci sosai take breakfast d'in dan da qyar ma abincin ke wuce mata qarshe ma kasa ida cin abincin tayi ta tashi cike da tunanin bata jin zata iya ci gaba da ganin wnn baqin cikin ya zama dole tasa qiyaya tsakanin Ryynt da man yayinda man zae dinga tsanàr Ryynt har zuwa lokacin haifuwar ta wato lokacin da ita kuma zata samu ta cika burinta ba tare da ta sake ganin wani baqin cikin ba tayi sallama dashi har abada.
2 weeks later tun a washe garin rnr kuwa malika tayi nasarar had'a qiyaya tsakanin man da Ryynt ta hanyar sawa man garin magani a abinci wanda taje ta kar6o wani qauye gurin boka ita da qawar ta fa'iza.
yanzu ya kasance kwata kwata man ba ruwansa da Ryynt sae tsana mae qarfi da ta shiga tsakanin sa da ita dashi kansa bae san dalilin tsanar ba,bare ita Ryynt da kullum cikin kuka take tana roqon ya gaya mata idan wani laifi ta masa ta bashi haquri amma komai baya ce mata sae muguwar tsawa da yake korarta da ita wani lokacin ma har dukan ta sae da ya tashi yi shiyasa tun da daga rnr bata sake tunkarar sa ba,kuma bata snr da kowa halin da take ciki ba sae ubangiji ta barwa komai ta duqufa ba dare ba rana tana kai kukanta a gurin ubangiji tana roqon ya kawo mata sauqi a cikin gaggawa dmn sati biyun nn da man ya kwashe yana nuna mata tsana sae taji tmkr shekara biyu ne shiyasa duk ta rame ta zama abin tausayi don kullum bata da aiki sae na kuka ga wani irin girma da cikinta ke ci gaba da yi da kuma nauyi.
A gurin malika kuwa duk da cewa still man bae damu da ita ba wani irin farin ciki take ciki sosae na ganin tayi nasara har ma ji take yanzu bata da wani sauran baqin ciki a rayuwar ta don ganin take shikenan tayi nasara man ba zae sake kula ryynt ba har ta kai ga cika burin ta.

Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```
Chapter 100 · 0% Book details