← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 112

Sashe 101

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🔮🔮🔮
*page 87*
Haka Ryynt taci gaba da rayuwa a cikin gidan har aka sake kwashe sati d'aya bata fita koina daga d'akinta sae d'akinta har abinci bata fita ci sae dae tasa kuku ya kawo mata dan ita tsoron mohd ma take ji yanzu bata ko son had'uwa da shi don ko da kuskure ta kalle sa sae ya watsa mata mugun kallo.
Washe gari ta tashi da wani irin zazza6i mae qarfi ta yini haka komai bata iyayi sae alawiyya ce ke d'an kula da ita wacce taso a snr da mohd Ryynt tace a'a dan ta fahimci alwiyya bata san abinda ake ciki ba.
Kwanan ta biyu tana fama da rashin lafiya a na ukun ne taji sauqi sosai dan komai tana iya yiwa kanta qarfin jikinta ne kawae bae gama dawo mata ba.
Da yamma bayan la'asar tana zaune kan darduma riqe da qur'ani tana karatu sae ga mami ta shigo d'akin aguje tace"Anti yaya Nasir na kira ku gaisa"
Ryynt ta tashi riqe da hannun mami suka fito Nasir na zaune shida mohd kan doguwar kujera yayinda mohd ke riqe da laptop yana wani aiki wanda yana ganin Ryynt ya tashi ya bar gurin byn yace da Nasir idan kaje ka gaida inna.
Nasir yace "za taji"
Yayinda Ryynt tayi qoqarin had'iye hawayen dake son fito mata ta shiga gaida nasir, nasir ya amsa gaisuwar yana kallon ta da kulawa dan ya fahimci da kmr akwai damuwa a tattare da ita har dae yanda yaga ta rame nn ya bawa mami makullin motar sa yace je d'auko ice cream a mota mami ta kar6i key ta tafi aguje sae murna take tana tsalle a natse nasir dake kallon Ryynt yace"me yake damunki ne Ryynt?
Ryynt tayi saurin girgiza kanta tace"ba komai"
Yace"amma kuma kika rame da yawa haka ko dae ba kya son gaya min abinda ke faruwa ne"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tace"ba haka bane nayi zazza6i ne kwana biyu"
Yace"Eyyah Allah sarki to ya jikin?
Tace" Alhmdlh ae naji sauqi sosai"
Ta qarashe mgnr ne yayinda mami ta dawo riqe da ledar ice cream,Nasir ya kar6i makullin motar sa yace"to ni na tafi Allah ya bida lafiya tace"Amin"
snn ya tafi ita kuma taja mami suka koma daga ciki suna shiga mami ta bata d'ayar robar ice cream dan guda biyu ne Ryynt tace"Aa kaiwa alawiyya dae idan zata sha .
Mami na fita Ryynt ta zauna tare da d'aura hannun ta akan cikin ta sae kallon cikin take tana shafa shi a hankali tana sauraren yanda cikin ke motsi yayinda hawaye ke silalowa a hnkli kan fuskarta dan tayi kewar kulawar mohd ba kad'an ba.
Bayan kwana biyu da faruwar haka guraren qarfe goma sha biyu na dare Ryynt na kwance tana bacci kan darduma riqe da littafin addu'o'i a hannunta,
a cikin baccin nata ne ta soma jin daddad'an qamshin turaren mohd yana shiga hancin ta nn ta soma bud'e idanun ta a hankali har ta sauke su akan mohd dake durqushe a gabanta d'auke da qwallah tap a idon sa sae kallon yanda ta rame yake.
A d'an tsorace ta tashi zaune tana kallon sa sae ganin tayi ya tafi da ita zuwa jikin sa ya rungume ta sosai a jikin sa sae kuka ya fashe dashi yana bata haquri kan abubuwan da ya mata dashi kansa baisan dalili ba Ryynt dae bata ce komai ba sae kuka ta fashe dashi itama yana ta rarrashinta har ya samu tayi shiru ya cire mata hijab tare da d'aura hannun sa akan tulun cikinta yana kallon yanda cikin nata ya qara girma bae ce komai ba sae kallon yanda ta rame yake cike da tausayi don har sae da idanun sa suka ciko da qwallah yace"my Ryynt dan Allah ki yafe min wlh bansan ya akayi ba haka kawae naji na tsane ki amma bayin kaina bane wlh i don't know why"
Ya qarashe mgnr ne yayinda hawaye suka gangaro kan fuskar sa.
Ryynt da bata kawo zargin kowa a ranta ba tasa hannu ta share masa hawaye snn ta kwantar da kansa a qirjin ta tace"ba komai Mk sharrin shaitan ne da baya son ganin ma'aurata cikin shiri kuma inshaa Allah ba zae sake yin galaba akan mu ba.
Nan mohd ya maida ta kan qirjin sa ya kwantar ya lumshe idanun sa sae shafa bayanta yake haka itama idanun ta a lumshe suke tana shafa sumar qijinsa a hankali sbd rigar da ke jikin sa a bud'e take.
Haka suka kwana abinsu har safe baccin da Ryynt taji kmr kar ta farka sbd ta jima batayi bacci mae dad'i irin sa ba.

Guraren qarfe tara na safiyar rnr Ryynt ce ta shigo d'akin mohd cikin doguwar rigar ta mae kyau ta atamfa ta sami mohd d'aure da towel ya fito daga wanka knn yayi tsaye sae kallonta yake tayi dan sosai tayi kyau duk da ramar da take d'auke da ita kuwa.
Bata iya qarasawa ba sae sadda kanta tayi qasa dan haka kawae taji tana jin kunyar sa sae mohd d'in ne ya qaraso da kanshi gurinta ya kai lips d'insa a hnkli kan goshinta ya d'aura mata kiss,a nn ta mishi ina kwana ya amsa tare da jan hannunta suka je kan bed suka zauna yakai hannu sae shafa cikinta yake yana kallonta yace"babyna yana lafiya?
Ta gyad'a masa kai tare da kwanciya kan qirjin sa takai hannu tana shafa sumar qirjinsa da ta kwanta luf abin sha'awa.
Mohd kuwa d'ankwalin kanta ya ture yana shafa gashin kanta da yasha gyara har ma yana fitar da wani daddad'an qamshin da kai tsaye mohd ya soma jin kansa a kasala ya lumshe ido sae shaqar qamshin yake yana ci gaba da shafa sumar a hankali, Ryynt na jinsa har ya soma wuce gun dan zip d'in rigarta ya zuge sae shafa jikinta yake ta koina yana kissin d'inta bata hana shi ba ta bada kai suka shiga romancing d'in juna kamar zasu kashe kansu har suka lula duniyar ma'aurata wacce suka ji dad'inta ba kad'an ba.

Tun daga rnr wata irin tsabar kulawa da soyayya mohd ke nunawa Ryynt wacce tafi ta farko ma dan duk rnr girkinta zaka gansu harabar gidan gurin shan iska manne da juna sae soye wa suke tayi abinsu kmr wasu Luv birds.
Malika kuwa tun da ta fahimci sun dawo da shirin su ba yanda batayi ba na ganin ta wargaza shirin ta hanyar sake zubawa man garin magani a abinci amma abu ya faskara sbd still Ryynt batayi sake da nafilfili da addu'o'in da takeyi ba dare da rana.
Kan dole malika ta gaji ta daina zuba masa maganin cike da nadamar ina ma tun farko bata soma ba dan gashi yanzu shirin da sukeyi ma yafi na daa yayinda ita kuma ta qara dawowa kwandon shara.

Sannu sannu lokaci keta tafiya dmn yanzu cikin Ryynt ya shigo cikin wata na tara yayinda cikinta yayi wani irin girman gaske da duk wanda ya ganta sae ya tausaya mata don ta ma daina fita koina ko downstairs ma sae da taimakon mohd take iya saukowa wanda yanzu kwata kwata mohd bashi da wani aiki sae na kula da ita hatta office ma ya daina zuwa ya barwa Amir da Aamil ragamar kula da asibitin dan shi yanzu ta Ryynt yake wacce duk safe da yamma sae ya fita da ita a cikin harabar gidan ya sata su zagoya gidan kaf duk fad'in sa kuwa.
Hakan duk yafi qona ran malika dan duk tulun cikin da ke gaban Ryynt bae hana man ya d'auki abar sa idan ta gaji da zagayawar ya tafi da ita gun resting chairs ya zaunar kan kujera ya kuma tsiyaya mata fresh milk mae sanyi a cup ya bata tana sha shi kuma ya shimfid'a handkerchief a qasa ya zauna ya kama qafafunta ya d'aura kan jikinsa yana matsa mata su cike da so da kulawa.

Ranar lahadi da dare guraren qarfe tara mohd ne jikin wardrobe yana ciro tufafi sae ga Ryynt ta shigo d'akin cikin shirin ta na bacci mohd yazo da saurin sa yaja hannunta yaje da ita kan bed ya zaunar da ita ya ciro farin handkerchief yana share mata zufar da ya gani a kan goshinta d'auke da damuwa a fuskar sa yace"Ryynt meyasa kika fito da kanki baki kirani a waya nazo ba"
Tace"na kira wayar ka ban samu ba kuma gashi ina son in fito"
Kallon ta mohd yayi cike da tausayi dan yasan da qyar ne ta iya saukowa don gashi sae numfashi ma take ta fitarwa sae duk yaji kamar ya cire cikin ya maida a jikin sa amma ba yanda zae yi tunda abune da bazae yiyu ba hkn ya tashi ya tsiyayo mata ruwa masu sanyi a glass cup ya zauna ya bata tasha snn yasa ruwan a handkerchief ya d'an jiqa shi yana share mata goshinta,fuskarta har zuwa qirjinta.
Ryynt dake kallon sa tace"ina zaka tafi da daren nn naga kana ciro kaya?
Yace"tafiya ce ta kamani Ryynt"
Kmr zata yi kuka tace"zuwa ina?
Yace"Abuja zan tafi"
Tace"zan bika"
Cikin muryar rarrashi yace"my Ryynt kinsan ba zae yiyu ba kiyi haquri ae kwana biyu kawae zanyi kinji"
Tace"to ka kaini gidan inna in ka dawo sae ka d'auko ni"
Yace"No my Ryynt ga alawiyya ae zata riqa taimaka maki da wasu abubuwan kinji yi haquri"
Kallon sa tayi qwallah tap a idonta yayi saurin girgiza kansa yace"yi haquri dan Allah kar kiyi kuka kinji ba jimawa zanyi ba 2dayz ne fa kawae"
Da qyar Ryynt ta iya had'iye hawayen ta snn ta gyad'a masa kae.
Mohd ya rungume ta a jikin sa yana qara rarrashinta.
Chapter 101 · 0% Book details