← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 112

Sashe 58

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

2:30
Rynt ce a bakin gate d'in school ita da qawar ta Sarah ko waccen su na jiran azo d'aukarta.
"Lah Rynt ga yayanki"
cewar Sarah wacce ta ta6o Rynt ta nuna mata man dake tafe zuwa gurin su ,
idon sa qyar akan rynt da yaga ta qara mae wani irin kyau da haske.
Itama Rynt haka taga man yayi haske ya kuma qara kyau sae dae ita kallo d'aya tayi masa ta kauda fuskarta akasin shi da har ya qaraso gurin su kallonta yake.
Bata ce dashi komai ba sae Sarah ce ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa yayinda Sarah tace da Rynt"kinga nima yayana yazo sae gobe Sunday idan mun had'u"
Rynt tace"to Allah kaimu"
Tana gama fad'ar hakane man ya d'ago fuskarta yana kallonta snn yace"ke baki iya gausuwa bane?
Shiru tamae kamar bata ji ba sae ma wani gefe da take kallo.
Yace"muje na sauke ki"
Tace"bana so"
Yace"ai gwanda kizo muje don drivernki naki ba zowa zai yi ba nace yayi zaman sa"
Tace"idan bai zo ba ma ai akwae napep"
Guntun tsaki yayi had'e da jan hannunta tayi saurin fizge hannun.
Yace"so kike na d'auke ki a gaban bainar jama'ar nn ko"
Tayi saurin kallon shi yace"ko kina musu ne?
Still kallon sa kawae take.
Ganin ya gyara hannuwan rgsa yasa tayi saurin ja baya sae kawai taji d'ayan takalminta ya tsinke ta kalli takalmin rae 6ace snn ta kalli man idonta tap da qwalla tace"ka gani ko"
Ya kalli takalmin snn ya kalleta yace"laifin ki ne ae"
Cikin muryar kuka tace"wane irin lafina ne bayan kaine kazo kana takurani"
Shiru mohd yayi ya hard'e hannyensa a qirji yana mae kallon yanda hawaye suka fara sakkowa a hnkli kan kumatun ta.
Inda cikin yanayi na shagwa6a Rynt takai hannu ta share hawayen .
Man dake kallonta yace"muje na saya miki wasu takalmin"
Ya fad'i hkne tare da riqo hannunta yayinda ita kuma bata musa mai ba tabi shi sbd ba gidan inna tayi kai tsaye ba gurin maman mami zata je duba mami dake jin jiki har ma yau kusan kwanan ta biyu knn bata zo school ba.
Suna isa gun mota Rynt ta warce hannunta taje ta bud'e gambun baya ta shiga.
Man da har ya bud'e 6angaren driver zai shiga sae mayarda ganbum yayi ya rufe.
Ya dawo nn seat d'in baya inda Rynt ta shiga shima ya shiga ya zauna yana mai kallon Rynt da ita ma shi take kallo.

Billy Giro😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [2/20/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

_Sarat Sale wnn page in nàki ne Allah ya bar min ke akan qaunar da kk min luv u ❤_

🔮🔮🔮🔮
*```Page 57```*
Yace" ke dan ubanki ni kk nufin na zamo drivern ki"
Cikin mugun 6acin rai Rynt ta kauda fuskarta had'e da hanzarin kai hannu zata bud'e gambun motar zuwa fita.
Man yayi saurin jawota yana mae kallon fuskarta yayinda Rynt ke kallon shi cike da tsana d'auke da qwallah tap a idonta.
Jikinsa ne yayi sanyi yana mae ci gaba da kallon yanda Rynt ke mae kallon tsana da kuma hawayenda suka soma gangarowa a hnkli kan fuskarta yayinda take yunqurin qwatar kanta daga gareshi.
A nn ya sami kanshi da rungume ta tare da kai bakin shi saitin kunnenta yace"sorry bazan sake zagin ki ba kinji"
Komai bata ce dashi ba sae kuka ta fashe mae dashi .
Nn ya sassauta riqonda yayi mata don ya fahimci zafin riqon ne yasa ta fashe da kuka.
Bata daina kukan ba taci gaba da yin abinta a nn kan qirjinsa.
Yayinda mohd ya shiga shafa bayanta a hnkli alamar rarrashi.
Minti d'aya sukayi a hk mohd ya soma jin kukan nata na mae zafi a rae a nn ya d'ago fuskarta zai had'e bakin su sae tayi saurin cusa fuskarta sosai a qirjin shi tana ci gaba da kukanta.
A sanyaye yace"to ki daina kuka idan ba kya so na miki .
Yana gama fad'ar hkne ta janye jikinta gabad'aya daga nashi ta kuma juya bayanta tana mae share hawayen fuskarta had'e da kai hannu ta bud'e ganbun mota ta fita.
Shima man fitowa yayi wanda duk a tunanin sa gidan gaba Rynt zataje sae kawae yaga ta tafi abinta tana neman napep.
Nan yaje yayi ta rarrashinta har ya samu da qyar ta koma cikin mota wacce still gidan bayan taje ta zauna.
Yayinda mohd yaje 6angaren driver seat ya shiga ya zauna yaja motar yana mae kallon Rynt ta jikin mirror can dae ya maida hnklinsa gun tuqi har suka iso wani babban shagon saeda takalmi ya faka mota ya fita yaje ya siyo mata takalma ya dawo ya bud'e 6angarenta ya shiga tare da fitar da takalman a leda yana nuna mata.
Takalmi ne masu kyau da tsada flat ba sosai ba ya kalli Rynt da ke kallon takalman don itama sosai sun bata sha'awa yace"sa muga idan zasu maki"
ba musu ta kar6i d'ayan takalmi ta sanya a qafar ta sae kuwa yayi dae dae a qafar ta.
Nan man ya bata d'ayan ta saka ta duqa zuwa d'auko tsinkakkin takalminta da suka tafi under seat bata kai ga d'aukowar ba man ya tada ta a hnkli yana kallon ta snn yace"kin manta da babyna dake jikin ki ne?
Kallon sa kawai tayi ta kauda fuskarta shi kuma ya kai hannu a under seat ya ciro takalman snn ya fita ya koma driver seat yaja musu motar.
A nn Rynt ta snr dashi inda zata.
Komai bai ce da ita ba sae kallonta kawae da yayi ta jikin mirror yaci gaba da tuqin sa har suka isa gidan nasu.

Tana fita yaja motar sa ya tafi ita kuma ta shiga gidan ta nufi 6angaren su mami .
Ta sami mami kwance a falo ita kad'ai wacce tana ganin Rynt ta tashi had'e da buga wani irin ihun murna tazo da gudu ta qanqame ta.

Umma dake kitchen ta fito a rud'e har tana had'awa da gudu se tayi tsaye turus tana kallon Rynt da ta d'auki mami sama zuwa jikinta.
Nn ta girgiza kanta d'auke da murmushi a fuskarta snn ta qarasa gurin su.
Rynt na ganinta ta saki murmushi had'e da gaida ta.
Cikin sakin fuska ta amsa mata har tana tambayarta inna tace"tana lfy"snn ta nemi guri ta zauna kmr yanda uman saliha ta buqata.
Umman saliha kuwa taje ta kawo ma Rynt abinsha da abinci ta ajiye tana mae kallon mami dake zaune gefen Rynt da ta fara cika Rynt da surutu tace"keh kam ko ba lfy bakin dae baya mutuwa ko"
Rynt tayi murmushi kawae tana kallon mami da ta tura baki tana kallon ummarta wacce takai hannu zata buge bakin tana mae fad'in"wae bana hanaki ba"
Mami kuwa tayi saurin 6oye fuskarta a jikin Rynt tana fad'in"yi hqr umma na daina.
Nan umma tayi dariya kawae tace da Rynt"kinga sauko kuci abinci tun d'azun ke kad'ai mami ke jira kixo kuci abincin nn har dae da taga lokacin tashi mkrnta yayi sae zuwa gate take tana dubowo idan kinzo .
Rynt ta kalli mami tace"ba kya jin jiki ne hln da kike faman yawo mami"
Umma tace"hm sauqi dae ta samu don jiya sae kuka take tamin har bata iya cin komai"
Rynt tace"Allah sarki Allah ya qara sauqi"
Umma tace"Amin sauko kuci abincin nn Rynh"
Ta fad'i hkne tare da bud'e kulolin abincin.
D'ayar kula alala ce d'ayar kuma sauce d'in qoda ne a ciki sae kunun aya dake gefe cikin jug yayi sanyi har ya gaji.
Ta zuba musu alalar a plate had'e da sauce d'in qoda gefe snn ta zuba musu kunun aya a cups tace"oya sae ku hanzarta kuci kar abincin ya sha iska.
Nan ta tafi ta barsu da suka gama ne umma ta dawo d'auke da ledar magunguna taba Rynt a cewar taba mami tasha kowanne spoon d'ad'ad'aya .
Rynt ta kar6a umman saliha kuwa taje da sauri ta d'auki wayarta da ke faman ruri kan dining wacce koda ta gama wayar har Rynt ta gama ba mami magungunan ,
nn ta kar6i ledar magungunan ta tafi dasu d'aki.
Sae ga Abban mami ya shigo ,
Rynt ta russuna har qasa tana gaida shi wanda cikin sakin fuska ya amsa mata snn ya shiga daga ciki.

Sae kusan qarfe hud'u Rynt tabar gidan koshi sbd tana da lesson ne amma taso ko zuwa yamai ne snn ko zata koma.

Da dare bayan sllr isha'i Rynt na zaune ita da inna,inna na cin abinci ita kuwa ta gama cin abincinta tana shan agwalima.

Sae ga Abban mohd ya shigo d'auke da sallama a bakinshi.
Inna ce ta amsa sallamar yayinda Rynt ta gaida shi cike da ladabi ,
ya amsa had'e da tambayarta ya karatu "tace"Alhmdlh"
Yace"baku fara Exams ba?
Tace"a'a mundae kusa"
Yace"To Allah taimaka tace"Amin"
Snn ta wuce.
Sae a snn suka gaisa shida inna bayan sun gama gaisawar ne yace"inna inshaAllah idan su Rynh sunyi hutu zamu je qauyen su mu kaiwa mae garin nasu gaisuwa sbd bae kamata ace tun lokacinda muka je neman aurenta ba bamu koma jewayarsu ba"
Inna tace"hkne kam nima na jima ina wnn tunanin sae naga Rynt makaranta take zuwa kuma kai kanka baka zauna ba sae tafiye tafiye kake shiyasa ban tuntun6e ka da maganar ba.
Yace"hakane gsky amma yanzu har izuwa lokacinda zasuyi hutu inshaAllah inada lokaci"
Inna tace"To Allah nuna mana lokaci ya kuma kaimu lafiya ya dawo damu lafiya"
Yace"Amin inna, bari na tashi dan ba daga gida na fito ba kan hanya nake"
Tace"ayyo to ko a kawo ma abinci kaci ne?
Yace"Aa inna ga dae wnn"
Ya fad'i hakane tare da ajiye mata leda a gefenta.
Inna tace"to Allah shiyi Albarka mungode"
Yace"Amin"had'e da fita.
Nan inna ta bud'e ledar ta sami gasasshen naman rago da ya gasu yayi kyau ga timatir da albasar da aka yanyanka akai da kuma qullin yaji gefe.
Rufe ledar tayi sae da ta kammala cin abincinta snn ta kira Rynt ta d'ibar mata nata sukayi zaune a nn falon suna kallo suna ci had'e da er firar da sukeyi jefi jefi.
Chapter 58 · 0% Book details