← Book details Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 112

Sashe 90

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🔮🔮🔮🔮
*page 80*
Basu kai koina ba sae gashi sun dawo Ryynt ta fito da sauri ta shiga cikin gida jim kad'an ta fito riqe da wayar ta a hannun ta wacce ta manta da ita a d'akin inna.
Taje zata bud'e gambun mota knn sae saukar ball taji tim a kan cikin ta, a tsorace ta fasa ihu ,yayinda mohd ya fito motar a fusace ya nufi yaron da ya jefo ball d'in cike da niyar kai masa mari Ryynt tayi saurin zuwa ta riqe masa hannu tace"Mk dan Allah kayi haquri yaro ne fa"
Yace"dan ubansa ko yaro ne kan me zae jefo ball akan cikin ki ko kuma shi abinda ke cikin ki ba rayuwa bane!
Yi haquri dae dan Allah tun da kaga bada gayya bane.
Mohd dake kallon yaron rae 6ace yace"oya duqa ciro ball d'inka a qarqashin mota ta ko kuma wlh na taka ta na wuce"
A tsorace yaron ya duqa ya ciro ball d'in sa zae wuce man ya bisa da ido yace"kae xo nn"
Jiki sanyaye yaron ya juya,
mohd yace"wa na gani ya fito a qarqashin mota ta d'azun?
Yaron ya sadda kansa qasa yace"nine"
Mohd yace"uban me kamin a qarqashin motar to?
Yaron yace"ball d'ina ne da ya gangara na d'akko"
Mohd ya kalli Ryynt yace"u see kince bada gayya bane bayan wnn ne karo na biyu koma fiye dmn muna fitowa naga lokacinda ya fito a qarqashin motar da sauri ya fice shiyasa sam ban cika son barin mota na a waje ba dan irin yaran nn marassa ji sae su maka 6arna a banza,bari kaji idan na qara ganin kana ball a guraren gidan nn wlh sae nayi maganin ka,oya tafi in daina ganin ka a nn very stupid!
Sim sim yaron ya bar gurin.
Ryynt ta kalli man tace"dan Allah ka rage yawan fad'an nn bana so wlh"
Mohd yace"Ryynt nasan yaron baya ji wlh ko kad'an,
musamman yake da filin ball a cikin gidan su banga uban me yasa ya fito yana ball a waje ba har yake qoqarin hallaka min ke da babyna ,
wlh gwara ma ace motar ce ya daka glass d'in motar ya fashe kan ya doka min ke .
Tace" to yi haquri dae dan Allah ya wuce.
Yayi murmushi had'e da jan hancinta yace"ni a gurina bae wuce ba sae naga lafiyar babyna tukun"
Tayi murmushi yayinda yaja hannunta suka shiga mota yakai hannu ya yaye rigarta yana shafa cikin yace"ya kika ji a lokacinda qwallor ta dake ki?
Tace"naji zafin saukar ball d'in ba sosai ba na kuma tsorata don har sae da abinda ke ciki ya motsa.
yace"da qarfi sosai ya motsa ko kuwa?
Tace"da qarfi ba sosai ba"
Man yayi shiru yana kallon ta can yace"Ryynt ya zama dole muje asibiti nayi scanning dmn naga lafiyar babyna"
Ryynt tace"plz Mk ba sae ka duba ba inshaa Allah ba wata matsala"
A natse ya girgiza kansa yace"No Ryynt abinda zaki d'auka ba matsala ba shi zae zo ya zama matsala kuma hankalina zae fi kwanciya idan na duba kiyi haquri muje kinji baza mu wani jima ba"
Ta gyad'a masa kai snn yaja motor suka tafi sae asibitin shi.

Kan hanyar su ta dawowa daga asibitin ne Ryynt ke kallon man wacce gabad'aya jikinta a sanyaye tace"mk nifa na tsorata don sae naga kmr yara har uku a cikina"
Saurin kallon ta yayi don sae da fa yace ta rufe idonta ashe ta bud'e bae sani ba,bae dai ce mata komai ba yayi d'an guntun murmushi yace"Ryynt knn kije ina da yara har uku photon ne kawae ya rarrabu"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"ai ni har na soma shiga tension wlh"
Yace"tension name dan Allah ya baki babbar kyauta.
Tace"um um wlh ni ko biyu ne bazan iya ba bare uku"
Yace"to idan Allah ya baki fa sae kiyi yaya?
Tace"hm nima ban sani ba amma na tabbatar cikin da kanshi zae zube kan tsananin tashin hankalin da zan shiga"
Mohd yayi murmushi kawae ba tare da yace komai ba yaci gaba da jan mota.

Suna isa family house basu zarce koina ba sae 6angaren iyayen sa.
Basu sami kowa a falon ba mohd ya umarce Ryynt da ta zauna bayan ta zauna ya haura sama jim kad'an sae gashi ya fito shida mahaifiyar sa da suka qaraso Ryynt ta zame kan kujera ta russuna cike da ladabi tana gaida ta.
Ba yabo ba fallasa mahaifiyar sa ta amsa mata har tana tamvayar ta ya hanya tace"Alhmdllh"
Mohd yace"Abba fa ko har yayi tafiyar dan jiya da na shigo gaida shi naji yana waya kan cewa zae je abuja"
Tace" Aa bae tafi ba tukun sae gobe yanzu haka yana d'akin shi bari naje na dubo maku shi.
Nan ta tafi zuwa sama mohd ya kalli Ryynt wacce ke durqushe still bata koma kan kujera ta zauna ba sae zama tayi a takure nn qasa gun gefen kujera.
Yace"Ryynt koma mana kan kujera ki zauna kin wani takura kanki haka sae kace kinxo baqon guri"
Tace"um um barni a nn kawai ya isa"
Bai ce komai ba sae hannun ta ya riqo zae maida ta kan kujera tayi saurin qwace hannun cike da jin kunya sbd Abba da ta hango tafe shida umma.
Mohd da bai gansu ba yaje zae sake riqo hannunta tayi mai wani kallo na alamar ga fa su Abba nn tafe suna kallon mu.
Nan ya juya had'e da d'an sosa bayan kansa alamar jin kunya suna qarasowa ya durqusa cike da ladabi yana gaida Abba,Abba ya amsa snn ya kalli Ryynt wacce tayi qasa da kanta tana gaida shi ya amsa d'auke da murmushi a fuskar sa yana tamvayar ta ya hanya tace"Alhmdlh"
Bayan sun gama gaisawar ne Abba ya koma daga ciki umma ta kira mai aikin ta ta kawo musu ruwa da lemu da kuma abun motsa baki.
Umma da kanta ta zubawa Ryynt lemu a cup ta bata ta kar6a ta samu da qyar ta kur6a kad'an ta ajiye don gabad'aya kunyar hjyr take ji gashi sae kallon ta take.
Kuma su biyu ne kawae zaune a falon sbd mohd ana kawo masu ruwa da lemu aka kirasa a waya ya fita.
Hjyr mohd kuwa tana kallon Ryynt ne sbd ganin yanda Ryynt ta canza tayi kyau klr ta ta koma kmr tashin er abuja ga natsuwa sae duk taji ta soma son Ryynt sosai a ranta,nn ta tsinkayo muryar Ryynt na tambayar Ameera fa.
Allah sarki taga dae ko kad'an Ameera bata ta6a nuna mata so ba amma kuma har take tamvayar ta ai kuwa sae taji ta qara sonta,
ta sakar mata murmushi tace"Ae Ameera na can gidan pretty,pretty taje da ita dmn ta samu ta riqa rage mata wani aikin kafin hutun makarantar su ya qare.
Ryynt da kanta ke qasa tayi d'an guntun murmushi tace"Allah sarki"
daga hk tayi shiru bata sake cewa komai ba .
Sae ga mohd ya dawo yace"umma bari muje other parts mu gaida su"
Tace"to sae kun dawo"
Nan Ryynt ta tashi suka tafi.
Sae da suka tafi d'ayan 6angaren snn suka je 6angaren su saliha.

Da murna sosai umman saliha ta tarbe su yayinda man da Ryynt suka gaida ta ta amsa musu cikin sakin fuska tana tambayar su ya hanya suka ce Alhmdlh nn Ryynt ta wuce d'akin saliha ta bar mohd suna qara gaisawa da umman saliha.
Chapter 90 · 0% Book details